Connect with us

Hausa

Hadarin da ke tattare da wankan kududdufi lokacin azumi

Published

on

Aminu Abdullahi

A ya yin da zafin rana ke ci gaba da gigita matasa da ke yin azumi a Kano, da dama daga cikinsu sun zabi zuwa wankan kududdufi domin rage wahalar azumin.

A zagayen da Kano Focus ta yi wasu daga cikin kududdufai a nan Kano ta iske matasa da dama da ke yin iyo a cin ruwan domin ragewa kai zafin azumi.

Galibin matasan na zuwa kududdufan ne da zarar rana ta take ba kuma za su bar wurin ba sai yamma ta yi.

Kabiru Isah mai shekaru 35 dake wanka a ruwan garin Kumbotso ya ce yana zuwa ruwan kullum da zarar rana ta take.

“Ina zuwa wanka tun daga karfe biyu na rana zuwa karfe biyar na yamma sannan na koma gida.

“Idan na gama wanka akwai bishiyu a gurin da nake shimfida darduma ko tabarma na kwanta,” a cewar sa.

Shima Salihu Umar dan shekara 25 ya ce yana zuwa yin wanka kullum da yamma a ruwan hauren wanki.

“Wankan yana rage mana lokaci da kuma azabar zafin da nake ji a jiki na.

“Idan kana wanka za kaji wahalar azumin ta ragu sosai, kuma ba za kaji rana kamar yadda wasu ke ji ba

Muftahu Garba dan shekaru 18 da ke wanka a ruwan promise ya ce tun yana karamin yaro yake zuwa wanka kududdufin.

“Da na dawo daga makaranta muke tafiya ni da abokaina, kuma babu wanda ya taba jin wani ciwo,” a cewar sa.

Hadarin rama azumi 60

Sai dai malamai sun ce dukkanin wanda ke shiga ruwa domin yin wanka tsautsayi yasa ya sha ruwa to zai rama azumi sittin ne.

A cewar babban limamin masallacin juma’a na Usman bn Affan da ke Kofar Gadon Kaya, sheikh Abdullah Usman ba laifi bane mutum yayi wanka a ruwan idan har azumi yana bashi wahala.

Sai dai ya ce ya zaman wajibi a dinga kiyayewa ya yin da ake wankan don gudun kada azumin su ya karye.

“Idan har mutum yaji azumi na bashi wahala babu laifi ya yi wanka ko a ruwa, ko a bandaki.

“Babu wani nassi da yace haramunne yin wanka a ruwa ga mai azumi.

“Sai dai matukar ya bari ruwa ya shiga cikinsa dagangan to ba makawa sai ya rama azumi sittin.” inji shi.

Ya kara da cewa idan har ya zaman dole yin wankan to yana da kyau al’umma su dinga kiyayayewa don gudun abinda zai karya musu azumi da zai sanyasu kaffara.

Wanne mataki iyaye ke dauka

Wasu daga cikin iyaye da Kano Focus ta zanta dasu sun ce suna daukar matakai domin hana yaransu zuwa wankan kududufin.

Lawal Musa ya ce kwamitin tsaro na unguwar Gwale sun taba kama dansa yana wanka a ruwan kududdufi.

Sai dai ya ce tun daga lokacin yake daukar mataki don ganin dan nasa baije yin wanka ruwan ba.

Muhammadu Sani ya ce wani lokacin sakacin iyaye ne ke sawa ‘ya’yansu ke zuwa wankan kududdufi, da hakan ke sawa wani lokacin ya kai ga rasa rai.

Ya ce idan har iyaye za su dinga sanya ido akan ‘ya’yansu tare da bibiyar abokan da suke hulda da su to za a samu saukin al’amarin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending