Hausa
Barazanar Ganduje: Ja’afar Ja’afar ya gudu London
Zulaiha Danjuma
Fitaccen dan jaridar nan kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar ya gudu Burtaniya, da iyalansa domin kubuta da ga farautar da ya ce ana yi masa.
Kano Focus ta ruwaito Ja’afar Ja’afar ya bayyana komawartasa a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi.
Ya ce zai ci gaba da zama a Burtaniya har sai ya samu nutsuwar cewar idan ya dawo gida gwamnati za ta iya kare rayuwarsa, da kuma tabbatar da yancinsa na Dan jarida.
Idan za a iya tunawa dai a baya-bayan nan ne Ja’afar Ja’afar ya shiga yar buya da jami’an tsaro bayan da ya zargi ana nemasa za a kamashi.
Wannan kuma a cewarsa na da alaka da faifan bidiyon Dala da ya wallafa, da aka nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karbar cin hancin Dala.
Sai dai Ja’afar ya zabi ya buya domin gudun me kaje yazo, damin kada a salwantar masa da rayuwa.
Hakan ce ma ta sanya yazu haka ya tattara ya koma burtaniya da iylansa don tsira da mutunci.
Hausa
The Chronicles of Kano #03 – Sarki Rumfa da kuma Taj–Al-Din Fi Ma Yajib Ala Al Muluk
Farfesa Abdalla Uba Adamu
A duk cikin Sarakunan da suka mulki Kano, guda uku sun yi fice fiye da sauran. Na farko shi ne Sarki Tsamiya (1307-1343) wanda shi ne na tara a jerin sarakunan. Ko da ya hau mulki ya tarar da bautar gargajiya a gari. Ya tara masu bautar ya yi musu bushara kamar haka: “Soyayya ana gadanta, ƙiyayya ma ana gadanta, babu wani abu tsakanina da ku sai baka da mashi da takobi, da garkuwa, ba yaudara, domin babu mayaudari sai matsoraci.”
Sarki na biyu shi ne Ali Yaji Ɗan Tsamiya (1349-1385). Shi ne wanda ya ci gaba da jihadin ba mahaifin sa ya fara. A lokacin sa Musulunci ya kafu a Kano, har manazarta suka laƙabawa Kano da darajar Sultanate. Wannan kuwa sakamakon umarnin da Sarki Ali ya bayar na cewa Kano ta zama ƙasar Musulumi daga 1349 bayan zuwan Malaman Wangarawa a ƙarƙashin Abdulrahman Zaite. na Farko, da suka kawo Musulunci su ka jaddada masa nasa Musuluncin (domin a kwai hasashen Musulumi ne shi).
Sarki na uku shi ne Muhammadu Rumfa Ɗan Yakubu (1463 -1499). A zamanin sa a ka samu bunkasar Musulunci da kuma ilimi. A wannan lokacin aka samu ingizowar Malaman Larabawa, Fulani, Kanuri, Buzaye suka yi wa Kano dirar mikiya domin neman ilimi.
A wannan lokacin ya yi abubuwa guda goma sha biyu na a-zo-a-gani, ciki har da kafa tushen reshen Jami’ar Sankore a Masallacin Madabo, wacce ta zama Jami’ar Madabo. A zamanin sa rukunin Wangarawa na biyu (in an tuna, rukunin farko sun iso Kano shekaru 114 da suka shuɗe a 1349), su ma a ƙarƙasahin Shugaba mai suna Abdulrahman Zaghaiti (na farkon sunan sa Zaiti, don kar ka ɓata!) suka zo Kano.
A zamanin wannan Sarki Malaman fada suka fito da Ajami a matsayin matakin farko na karatun yara a Tsangayu da makarantun Allo. Lokacin ne ma aka fito da ‘kuɗin laraba’ a matsayin kuɗin makaranta wanda za a bawa Alaramma domin yin cefanen ciyar da makaranta washe gari, watau ranar Alhamis.
Amma babban abin janyo hankali a zamanin Sarki Rumfa shi ne fitar da tsarin mulki a Kano – na farko a rubuce a kowacce daula a ƙasar Hausa. Wannan kuwa ya faru ne ƙarƙashin jagorancin mashahurin Malami Muhammad ibn Abd al-Karim al-Maghili, wanda ya zo tun daga ƙasar Algeria domin bayar da tasa gudunmowar wajen ciyar da ilimi gaba a Kano saboda shaharar da ta yi wajen kasuwanci da ilimin addinin Musulunci.
Da ya zo, Sarki Rumfa ya roƙe shi da ya ba shi shawara a kan tsarin mulki a Musulunci saboda inganta nasa mulkin da adalci. Al-Maghili nan take ya yarda ya rubuta masa littafi, Tāj al-Dīn fī Mā Yajib ʿalā al-Mulūk wa al-Salāṭīn. Wannan ya zamar masa jagora wurin tafiyar da al’amurran siyasa da mulkin ƙasar Kano.
A kwai kundaye digiri na uku aƙalla guda biyu waɗanda suka nuna sakamakon bincike mai zurfi a kan Al-Maghili and mulkin Sarki Rumfa. Ga jerin guda biyu sa suka fi shahara. Ba duk a ke samu a Acibilistan ba, amma in a ka ƙura ido, wataƙila a yi sa’a.
Gwarzo, Hassan. The Life and Teachings of al-Maghili with Particular Reference to the Saharan Jewish Community. Ph.D. Thesis. Univ. of London, 1972.
Starratt, Priscilla Ellen, Oral history in Muslim Africa: Al-Maghili legends in Kano. PhD thesis, University of Michigan, 1993.
A yau dai ga fassarar Tāj al-Dīn da Hausa, kuma an sarrafa ta a Ajamance. Bi rariyar liƙau ɗin da ke ƙasa ka tsinko shi.
https://bit.ly/3ZBDrHl.
Farfesa Abdalla Uba Adamu
Hausa
Shekara 60 na Hausawa a Doron Ƙasa (4) – Farfesa Malumfashi
Wannan wani raddi ne da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi wa Abduljalil Ismail Ajis
Bayan dukkan wannan balaguro tare da sauran al’ummar duniya wannan ya haifar da damar da aka samu Hausawan wajen ƙasar Hausa suka sake haɗuwa da sauran ‘yan uwansu, musamman na ɓangaren jinin Uwa da ba su yi balaguro zuwa ko’ina ba a sassan duniya, waɗanda suke zaune a nahiyar Afirka a tsawon shekaru. Wannan haɗakar barbarar ‘yan’yawa ita ta samar da kai da ni da duk wani Badauri ko Bagobiri ko Bakatsine ko Bazamfare ko Bakabe ko Bazazzage ko Basantolo ko Bakano ko Bagunge ko Bahaɗeje ko Barane da wasu ƙasashe da al’ummun Hausawa da dama da suka yi rayuwa, suka ɓace a tsawon tarihi.
Wannan ba komi yake nuna mana ba sai al’ummar Hausawa ba na yanzu ba ne, shi harshen Hausa ne na yanzu, shi ma ba yanzun-yanzu, irin na yau ba ne, shekara dubbai ne ake magana. Ƙila tambayar da wasu kan iya yi zuwa yanzu ita ce yaya aka yi aka san waɗannan batutuwa da yawanci ba su a rubuce ko ba a ci karo da su ba a rubucen ko kuma me ya sa ba a zubo hujjoji da za a iya gani ƙwaro-ƙwaro domin tabbatar da batun ko akasin haka ba? Ta yaya yawancin irin waɗannan bayanai ba su bayyana ba ko da kuwa daga kunnuwa da suka girmi kakanni, ta ina aka samar da tunanin?
Ire-iren waɗannan tambayoyi an sha yin su game da wannan bincike, abin da zan iya cewa shi ne, yawancin bayanai ba su ɓullo daga tarihin da muka saba karantawa ba ne, sannan yawancin bayanan da yake sun tusgo ne daga rayuwar lokacin da ba tarihi a rubuce ko ajiye suna da wahalar karɓuwa nan da nan, haka kuma fagen nazarin tarihi da tarihihi da muka gwanance a ka, ba su iya fasalta su da kyau ba, amma wasu daga cikin bayanan na nan kimshe cikin adabinmu na gargajiya da waƙoƙi da kalamominmu na yau da kullum, ba mu dai kula ko nazarce su da kyau ba ne. Wannan giɓi shi ya sa aka koma cikin gonar nazarin ilmin ƙwayar halitta da ke tattare da jinin al’ummar duniya, ciki ko har da Hausawa domin samun mafita.
Shi wannan fage na nazarin ilimin ƙwayar halitta ya zama kandami ne na fahimtar rayuwa ta tsawon tarihi ko da kuwa ba a rubuta ko ajiye shi ba. Saboda binciken masana kimiyya ya gano cewa a cikin gudan jini ko ƙwayar halitta akwai tarihin al’umma da ke jibge, sai an buɗa shi za a kwashi ilimin da ke ɓoye. Domin kowane kalami ko waƙa ko zancen azanci ko gudanuwar addini ko kuma bazuwar al’adu na haihuwa ko aure ko soyayya ko mutuwa suna damfare a cikin jinin al’umma, ba su ɓacewa baki ɗaya, ke nan daga lokaci zuwa lokaci ana iya ƙwaƙulo su domin nazarin rayuwar yau.
Saboda haka yawancin bayanan da muka zubo a nan, sun samo asali ne daga bincike da nazari da aka samu yi daga ɗibar miyan bakina da jini, a matsayin Bahaushe aka ƙwanƙwance tarihin da ke ƙunshe a ciki a shekarar 2017, a can Amurka, a ɗakin bincike na (Genographic project), a lokacin kuma akwai tarin bayanai kan Hausawa da ‘yan uwansu da suka rigayi nawa, daga wannan banki ne aka samar da bayanai da suka nuna yadda rayuwar ‘Hausawa’ ta kasance a tsawon tarihi.
Daga sakamakon wannan bincike ne aka fitar da bayanan da ke haskaka mana yadda Hausawan wannan zamani suka wanzu, mai nuna daga ina Hausawa suka tuzgo, su wane ne ‘yan uwansu na kusa da na nesa. Abin da kuma ya fito fili ya haɗa da:
•Akwai jinin al’ummar yankin sassan ƙasashen Maleshiya zuwa Indonesiya da Filifins a cikin Hausawa wannan zamani, (miya ta kuka ko taushe da muke da su yanzu, akwai su a harshen Malay da makusanta).
• Akwai jinin Barbar na yankin Siwa a Arewacin ƙasar Masar har kashi 20 cikin 100 a cikin jinin Hausawan wannan zamani. A wannan yanki ne Hausawa suka yi bautar rana da muke bayyanawa ta waƙoƙin gargajiya da suka nashe a ƙasar Hausa tun da daɗewa. Wasun mu ba su manta irin wannan waƙa ba; ‘rana, rana buɗe, buɗe in yanka miki rago ki sha jini, shar, shar’. Ba aron wannan waƙa aka yi ba, jini da gado ne daga al’ummar Hausawa da suka rayu a Masar ta dauri. Nan kuma aka samo kalmomi irin na auratayya da soyayya da ke jibge a tunanin Hausawan yau, misali ‘so’ da ‘soyayya’ da ‘aure’ da ‘mata’ da ‘miji’ da wasu irin su da dama!
• Haka kuma Hausawa yau suna ɗauke da jinin mazajen da ke zaune a kudancin ƙasar Masar na kimanin kashi 6 cikin ɗari, shi ya sa ake cewa Hausawan yau tsittsigensu na Yahudawa da Kibɗawa ne, wato ‘yan uwa ne ga al’ummar Annabi Musa da ta Fir’auna.
Farfesa Ibrahim Malumfashi malami ne a Jami’ar jihar Kaduna ya wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.
Hausa
Shekara 60 na Hausawa a Doron Ƙasa (3) – Farfesa Malumfashi
Farfesa Malumfashi
Wannan wani raddi ne da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi wa Abduljalil Ismail Ajis
Ke nan ko a wancan lokaci waɗannan al’umma ta Hausawa suna a doron ƙasa, a matsayin al’umma kuma ƙabila. Wani ƙarin haske kuma shi ne, ko kafin zuwan su wannan yanki na tsakiyar Afirka, ai sun rayu a matsayin mutane a sassan Arewacin Afirka; sun rayu a Kudancin Masar, inda yawancin ahalin Hausawa ta ɓangaren Uba suka wanzu, suka rayu a musamman yankin Siwa, wanda ke a Yammacin ƙasar Masar da iyakar ƙasar Libya kusan shekara dubu 20 da suka wuce.
Daga baya, Hausawa da ahalinsu sun yi rayuwa a wannan yanki na tsakiyar Afirka, kamar yadda na faɗa can baya, nan ne kuma aka samar da harsunan da aka yi wa laƙabi da ‘yan Ahalin Afrika da Asiya a daidai shekaru dubu 10 zuwa 9, nan kuma aka samar da tsatson ahalin harsunan Chadic, daga shekara ta 9,600 zuwa 5,200, inda aka haifar da harshen ‘Hausa’ da ‘yan uwansa, irin su Gwandara da Ron da Tangale da Warji da Bade da Angas da Barawa da Kare-Kare da sauran su. Ke nan akwai al’umma da ƙabilu da mutane masu mabambanta addinai da al’adu a wannan yanki, tun da daɗewa.
Idan aka nazarci harshen Hausa da harsuna da al’ummar waɗannan yankuna da ‘Hausawa’ suka taso daga ciki can baya, musamman daga yankin Maleshiya a Asiya da yankin Larabawa, musamman ɓangarorin Yemen da Falasɗinu da Saudi Arabiya da Masar da Isira’ila za a tsinci wasu al’adun ‘Hausawa’ da addinai da wasu kalmomi na harsunan waɗannan yankuna a cikin rayuwar Hausawa ta yau; dubi lamarin bautar rana, ire-iren abinci da sutura da soyayya da mulki da waƙe-waƙen gargajiya. Akwai misalai na kalmomin Hausa na yau da suka samo asali daga waɗannan yankuna da addinai da al’adu da za su yi mana jagora, in sha Allah.
Bayan haka zaman Hausawa na tsawon tarihi a Arewacin Afirka, a tsakanin ‘yan uwa da abokan hulɗa kamar na zamanin Annabi Ibrahim da Annabi Musa, wato waɗanda suka wanzu cikin harsunan Ibrahimanci da na Misirawan dauri da Yahudawan zamanin da kuma Kibɗawa, daga cikin waɗannan al’umma, wasu sun yi hijira zuwa yankin ƙasar Hausa da maƙwabtanta na yanzu tun wancan zamanin, inda suka yi tarayya da ‘yan uwansu, wato ‘Hausawa’ zaunannu, waɗanda suka daɗe suna bautar gargajiya, kuma ba su san wani abu addinin zamani ba, domin ba a saukar musu da addini ko Annabi ba, sai daga baya ta hanyar shigowar waɗannan baƙi da suka taɓa yin ire-iren waɗannan addinai a can baya da suka nashe da su, har kafin zuwan masu yaɗa addini na zamani daga baya.
An ga ɓirbishin irin waɗannan al’umma a wasu sassan ƙasashen Hausa da suka haɗa da Daura da Gobir da Kano, wanda ya nuna mana cewa ‘Ibrahimawa’ da ‘Larabawa’ da da ‘Misirawa’ da ‘Yahudawa’ da ‘Kibɗawa’ da wasu alummu masu yawa sun zaunu, sun zaune, a sassan ƙasar ‘Hausa’ ko kafin sake bayyanar Larabawa da addinin Musulunci ƙasar Hausa, daga baya.
Idan an natsu, za a fahimci cewa ‘Hausawan’ dauri kusan iri uku ne ko huɗu, wasu na ganin ma sun kai biyar a doron ƙasa kafin Hausawa zamani. Sun kuwa haɗa da ‘Hausawa’ da suka rayu cikin aljanna a zamanin Annabi Adamu, (atishawa kalma ce tun zaman aljanna) da kuma Hausawa da suka rayu a doron ƙasa bayan an sauko da Adamu da Hawwa’u wannan duniyar, suka haihu da hayayyafa har ta kai Ƙabila ya kashe Habila aka fara mutuwa a doron ƙasa, (ke nan sunan Adamu da Hawwa’u da mutuwa) suna tare da ‘Hausawa’ tun wancan lokaci. Akwai ‘Hausawa’ da suka rayu cikin kwale-kwalen Annabi Nuhu da kuma bayan ruwan Ɗufana da sake sauka a bisa doron ƙasa. Kalmomi irin su Nuhu da Ɗufana da Tantabara, (uwar alƙawari) da Jaki da doki, tun lokacin ‘Hausawa’ ke tafe da su a rayuwarsu, har zuwa yau, ba aro suka yi ba.
Haka batun yake game da rayuwa a zamanin Annabi Ibrahim, ‘Hausawa’ ma sun nasu a lokacin, Abram makusanci ne da Abiramu ko Abrahamu ko Ibrahimu ko Ibrahim, haka kuma Basaraken nan Lamarudu (Namrud ko Nimrod) da ƙasar da Annabi Ibrahim ya tare daga baya, wato Ƙan’ana, (Canaan), akwai su ko a zamanin Dauramomin ‘Daura’, kafin zuwan Musulunci da Kiristanci a ƙasar Hausa.
Farfesa Ibrahim Malumfashi malami ne a Jami’ar jihar Kaduna. Ya wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.