Connect with us

Hausa

Haramun ne biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane

Published

on

Aminu Abdullahi

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan kuma mataimakin shugaban masallacin birnin tarayya Abuja Farfesa Ibrahim Makari ya ce haramun ne biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Kano Focus ta ruwaito Malamin ya bayyana hakanne ya yin tafsirin Alqur’ani da yake gabatarwa a babban masallacin Abuja ranar Asabar.

Maqari ya ce idan har Allah S.W.T zai hana baiwa makiya na yaki  kudi don kar a karfafe su suci gaba da yakar musulmi, ina kuma ga mutanen da saboda zalunci da ta’addanci za su kama mutum suce sai an hada musu kudi za su sake shi.

“A don haka ku hada kudi ku bayar a saki wannan mutumin haramun ne, kuma laifi ne.

“Idan a cikin kudinsa ya ga dama ya cire ya fanshi kansa wannan shi ya ga dama, amma bashi ne abinda manzon Allah S.W.A ya zabar masa ba.

“Hadisin Abu Huraira na Muslim, wani mutum yazo ya samu manzon Allah S.A.W ya ce, mutum ne yazo yana son ya kwace kudina.

Manzon Allah S.A.W ya ce kada ka bashi, kada ka bari ya kwata, ya ce ya rasululla idan ya yakeni fa? Ya ce ka yake shi kaima.

“ Ya ce ya rasulullah idan na kashe shi fa? Ya ce yana wuta, ya ce idan ya kasha ni fa? ya ce kana Aljanna,” inji malam.

Ya kara da cewa a babin toshe kafar barna haramun ne kuma yana daga cikin mafi girman hanyar toshe wannan kafar mai yi yasan cewa duk abinda zai yi ba za a bada wannan kudin ba.

“A karshe shi zai yi wahala ya yi barnar kudin, sannan a abincin da ya baiwa mutumin da ya kama da lokacin sa da kuma harsashin da yayi amfani dashi wajen kisan, amma yasan cewa ba za a bada kudin ba.

“Wanda duk kuma aka kashe lokacinsa ne ya yi kuma shahidi ne dan aljanna,” a cewar sa.

Ya kara da cewa matukar al’umma ta tsaya akan wannan ka’idar da musulunci ya aje, za a magance bala’in masu garkuwa da mutanen.

Sai dai ya ce matukar mutane za su cigaba da bada kudi domin su fanshi ‘yan uwansu to masu garkuwa da mutanen za su cigaba da yi ne don samun kudin siyo wasu makaman tare da firgitar da mutane.

“Kuma za su cigaba da yin karfi ta yadda za su gagari al’umma da gwamnati, kuma mutuwa dole ce za ta zo idan ma baka tafi yanzu ba dole zaka tafi watarana,” a cewar Maqari.

Ya kuma ce idan har masu garkuwa da mutane suka kama mutum to da ma ce da Allah ya bashi domin ya gwada jihadi.

“Jihadi ne yazo mana a arha shahada ce Allah ya bamu kawai kayi addu’a Allah yasa mucika da Imani, Allah ya karbi shahadar mu shikenan.

“Amma bai kamata ka baiwa mutane kudi ba ka karfafe su,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending