Connect with us

Hausa

Dalilai 4 da ke janyo kwacen waya a Kano

Published

on

Zuliha Danjuma

Masana  a bangaren halayyar dan adam sun alakanta dalilan da ke jawo kwacen waya a cikin al’umma da tsananin rashi tarbiyya.

Lamarin kwacen waya dai ya ta’azzara a Kano ta yadda a yanzu jama’a ke dari-darin bin wasu hanyoyi a Kano domin gudun abinda zai faru.

A zantawar jaridar Kano Focus da masanin halayyar dan adam dake jami’ar Bayero a nan Kano Abdullahi Maikano Madaki ya bayyana wasu dalilai hudu da ke sanyawa matasa ke fadawa cikin lamarin.

Maikano ya ce dalilan sun hadar da lalacewar tarbiya, talauci da rashin aikin yi, sai yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi, da sakacin gwamantoci da mahukunta.

Lalacewar Tarbiyya

A cewar Maikano Madaki, iyaye sun saki hakkokin da Allah ya doramusu wajen tarbiyyantar da yaransu.

Haka kuma a yanzu iyaye na dorawa yara kauna marar misaltuwa ta yadda basa iya dakatar da ya yansu ga aikata wani al’amari da suke yi a gabansu.

Wannan ta sanya yaran ke yin abinda sukaga dama ba tare da iyayen sunce kanzil ba.

Tallauci da rashin aikin yi

Malamin ya kara da cewa tsananin talauci da rashin aikinyi ya taimaka wajen kekashewar zuciyar matasa har suke fadawa harkar kwacen waya.

Ya ce  yadda al’amura suka yi zafi a halin yanzu ya ta’azzara rashin zaman lafiya a cikin al’umma.

A cewarsa akasarin masu kwacen wayar ba amfani suke da shi ba siyarwa suke yi suyi afani da kudin.

Shaye-shaye

Dakta Maikano madaki ya ce dalili na uku shi ne ta’mmali da miyagun kwayoyi da matasan ke yi.

Ya ce yaran da suke ta’ammali da miyagun kwayoyi adadin su ya karu ainun, da hakan ya kara kawo rashin zaman lafiya.

Ya kara da cewa duk al’ummar da ta ke da matasa masu yawa da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi to tana cikin hadarin kwace da sace sace.

Sakacin Gwamnati

Malamin ya bayarda dalili na hudu da sakacin gwamnati wajen shawo kan matsalar. 

ya ce haryazu gwamnati ta kasa fitar da wani tsari da zai taimaka wajen fitar da al’umma daga kangin talauci.

A cewarsa da mahukunta za su dauki nauyin da Allah ya doramusu su yi abinda ya da ce da ba a kai ga wannan matsalaba.

Ko me jami’an tsaro ke yi

Rundurar ya  sandan jihar Kano na ci gaba da farautar irin wadannan batagari a duk inda suke a dadin jihar nan.

Ko a ranar Talatar da ta gabata sai da rundunar yan sandan ta kama matasa 63 da ke addabar jihar Kano da kwacen waya da sace-sace.

Haka zalika jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida mana cewa kwamishinan yan sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko ya fito da wasu sabbin tsare-tsare da suke taimakawa wajen kawo karshen matsalar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Continue Reading

Trending