KANUN LABARAI
Rundunar ‘yan sanda ta kama matasan da ke balle shaguna a unguwannin Kano

Aminu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu da ake zargin barayi ne dake balle shagunan al’umma tare da kwato wasu kayayyakin.
Kano Focus ta ruwaito wadanda ake zargin sun balle wani shago a unguwar Gwale tare da sace kekunan dinki guda biyar.
Haka kuma bayan bincike sun bayyana wadanda suke kaiwa kayan idan sun sata.
Wannan na kunshene cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.

Cikin wadanda ta kama akwai Naziru Haruna da ake kira Kwado mai shekaru 16 da Yusif Muhammad dan shekara 18, da kuma Abdulrahman Saminu shima mai shekaru 18 sai Halifa Iliyasu dan shekaru 14.
Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce haka zalika rundunar ta kama wasu dake siyan kayan da aka sato duk da cewa sun san kayan sata ne.
Ya kara da cewa wadanda aka kama da laifin siyan kayan satar akwai Ibrahim Muhammad dan shekara 25 dake unguwar Sani Mainagge, da Isma’il Mohammed shima mai shekaru 25 mazaunin unguwar Sani Mainagge, sai Saminu Salisu dan shekara 34 dan unguwar Makwarari.
Ya kuma ce duk kan wadanda aka akama an same su dumu dumu da kekunan dinki na sata da suka siya.
Haka zalika ya ce rundunar ta kama wani mai suna Halifa Iliyasu dan unguwar Gwale mai shekaru 14 da ya balle shagon dinki a unguwar Sani Mainagge inda ya sace keken dinki da kayan sawa.
Ya ce rundunar ta kara samun nasarar kama wasu masu siyan kayan sata mazauna unguwar Sani Mainagge da suka hada da Saifullahi Ali mai shekara 24 sai Abduljabar Muhammed dan shekara 26.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda ya bayarda umarnin gudar da bincike tare da gargadin al’umma da su guji siyan duk wani abu da ake zargin na sata ne.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
