Connect with us

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Ya kamata a yi dokar ‘kisa’ kan masu kwacen waya a Kano-al’umma

Published

on

Aminu Abdullahi

Al’ummar jihar Kano na ta kiraye-kiraye ga gwamnati da jami’an taro da su fara kashe wadanda aka kama da laifin kwacen waya a nan Kano.

KANO FOCUS ta ruwaito wannan na zuwa ne tun bayan da rundunar yan sandan jihar Kano tayi  holin wasu matasa 62 da ke addabar jihar nan da kwacen wayoyi al’umma.

Wannan ce ta sanya jama’a da dama suka fara tofa albarkacin bakin su, cewar matasan da ake kamawa da wannan lafi basu da amfani kamata ya yi jami’an tsaro da gwamnati su fara hallakasu.

Shamsu Mansur Isah dan asalin jihar Kano ne ya kuma ce kamata ya yi a dinga masu irin wannan al’amari a dinga kashe kawai.

A cewarsa suma basu damu ba ko mutun zai yi rai ko ba zai yi ba matukar za su samu abinda suke so to za su kashe mtum.

Ya ce sau da yawa idan an kama su ba a jin irin hukuncin da ake yanke musu da hakan ke kara sanya wasu su rungumi muguwar ta’adar.

“Ana sanar da kama su ne kawai sannan babu wani hukunci da ake yanke musu mai tsauri ina ganin harbe su shi ne zai zama mafita wajen kawo karshen wannan masifa,” a cewar sa.

Shima wani matashi Nura Abdurrahman ya ce  da a ce ana kashe su kamar yadda suke kashe mutane akan wayar da bata fi naira dubu biyar ba da an samu sauki.

“Abin takaici shi ne kotunanmu sun zama kamar kasuwa da an kai irin wadannan yara tara ake musu ko a yanke musu hukuncin da bai kai ya kawo ba”.

“Da yawan iyaye suna gaza baiwa ‘ya’yan su tarbiyar da ta da ce domin mafi akasari masu aikata wannan abu ‘ya’yan talakawa ne, babu ilimin islamiyya balle na boko.

“Idan har gaskiya ne ana so a kawo karshen su to ya kamata duk wanda aka kama a harbe shi ko a rataye shi ba tare da bata lokaci ba” A cewarsa.

Ko hakan na da muhalli a doka?

Fitaccen lauyan nan a nan Kano Abba Hikima Fagge ya ce dokokin da ake amfani dasu wajen hukunta masu kwacen waya sunyi rauni ainun.

A cewarsa ana iya bada bellin wanda aka kama da laifin ba tare da yaje gidan yariba.

Ya ce la’kari da yadda kwacen waya ya yawaita a jihar Kano yana da kyau ayi doka ko a gyara wacce ake da ita don samar da hukunci mai tsauri.

Ya kara da cewa ba laifi bane a yankewa duk wanda aka kama da laifin kwacen waya ba tare da ya yi amfani da makami ba hukuncin shekaru 20 a gidan yari.

Ya ce idan kuma har an kama mutum da yin amfani da makami wajen kwacen waya to a yanke masa hukunciun daurin rai da rai.

“Wanda kuma ya kashe to a kasheshi, bai kamata a kyale wanda zai dauki makami ya kwaci waya yana yawo a cikin al’umma ba.

“Sai dai matsala itace gwamnoni basa sanya hannu a kashe mutum saboda siyasa kuma ana yanke hukuncin kisan,” a cewar sa.

Ya ce abin takaici ne yadda ‘yan siyasa ke fito da ‘yan fashi da makami da masu kwacen waya wanda kuma suke sake addabar al’umma.

Continue Reading

Trending