Connect with us

Hausa

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Published

on

Hisbah Commander @ Minjibir Park

Aminu Abdullahi

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama gandaye 11 da suka hadar da mata 8 da maza uku a sassa daban daban na jihar Kano.

Kano Focus ta ruwaito babban daraktan hukumar Aliyu Musa Kibiya ne ya bayyana haka jim kadan bayan kama matasan ranar Laraba.

Ya ce hukumar ba za ta saurara ba wajen kama duk musulmin da yaki yin azumi a watan ramadan ba tare da wata lalura ba.

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

Neman matar aure: Hisba ta kafa kwamitin mutane 5 da zai binciki Uba Rimo

Hisbah za ta dauki ma’aikatan sa kai 5700

Ya ce dukkanin su an kamasu ne suna cin abinci a bainar jama’a ba tare da jin kunya ba.

Aliyu Musa ya ce hukumar za ta tantance su domin ware wadanda ke da uzuri tare da ladabtar da wadanda suka yi dagangan.

Ya kara da cewa ba gaskiya bane zargin da ake yi cewa hukumar na hukunta matan da ta kama suna cin abinci koda kuwa suna lokacin al’ada.

“A da sai kayi shekaru arba’in ko fiye amma ba za ka taba ganin iyaye ko kanne nacin abinci a bainar jama’a ba lokacin azumi.

“Kuma duk suna da irin wannan lalurar ta al’ada saboda haka abin takaicin shi ne aganki kina cin abinci ko kina yagan yagan a bainar jama’a,” a cewar sa.

Ya kara da cewa abin takaici ne da rashin kunya a ce mace tana nunawa duniya cewa tana cikin al’ada.

“Idan har suna cikin irin wannan hali kamata ya yi su kebe a wani guri na daban ba wai fitowa fili ba, wanda hakan bai dace ba,” inji shi.

Ya kuma ce babu wanda hukumar tabi har gida ta kamashi yana cin abinci yana mai cewa duk kan wadanda ta kama suna cin abinci ne a waje.

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending