Connect with us

Hausa

Matashi na neman wanda zai saye shi a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wani matashi mai suna Aliyu Na Idris ya sanya  kansa a kasuwa  yana neman wanda zai saye shi a Kano.

KANO FOCUS ta ruwaito matashin mai shekara 26, dan asalin Jihar Kaduna ne,  yana yawo ne a kan tituna a Kano, dauke da kwali da aka rubuta  “wannan mutumin na sayarwa ne a kan Naira miliyan 20.”

Shi dai Aliyu, wanda ya shafe kimanin kwana biyar yana yawon neman wanda zai saye shi a garin Kano, ya ce shi tela ne, matsin rayuwa ce ta sa yake son sayar da kansa N20m, kuma da sanin iyayensa.

Ya ce da farko sai da ya fara tallata kansa a Kaduna ko za a samu mai sayen shi, amma da ya ga ba a taya shi da kyau ba, sai ya wuce zuwa Kano ko zai dace a saye shi a kan farashin.

“Duk da cewa na samu wadanda suka taya ni a kan Naira miliyan 10, miliyan biyar da N300,000 a Kano, amma ban sallama musu ba, saboda abin da suke son su biya bai kai abin da nake sa rai ba,” inji shi.

Matashin ya ce shi tela ne amma daga baya komai ya tabarbare mishi saboda matsalar kudade, ya rasa kwastominsa, ga shi kuma jarinsa ya karye.

A cewarsa, a halin yanzu ba shi da wani abin da zai iya dogara da shi, ballantana ya samu jarin da zai fara wata sana’a, shi ya sa ya yanke shawarar ya dora wa kansa ganye ko zai samu a saye shi a Naira miliyan 20.

“Idan aka siyeni zan baiwa iyayena Naira miliyan 10, in ba da miliyan biyar a matsayin haraji a jihar da aka saye ni.

“Mutumin da ya tallata ni har aka saye ni zan ba shi Naira miliyan biyu, ragowar miliya uku kuma zan ba wa duk wanda ya saye ni ya ajiye a matsayin kudin kula da dawainiyata.”

A cewarsa, ya san zai rasa ’yancinsa idan aka saye shi, amma ya gwammace hakan kuma a shirye yake ya yi abin da iyayen gidansa za su sa shi.

Ya kara da cewa idan ba a samu mai sayen shi a Kano ba zai tafi wata jihar ya ci gaba da neman wanda zai saye shi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yanzu-yanzu-Kotu ta rushe shugabancin Abdullahi Abbas

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Wata kotun tarayya dake Abuja ta rushe zaben shugabancin jam’iyya APC da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar.

KANO FOCUS ta ruwaito mai shari’a Hamza Mua’zu ne ne ya rushe zaben a zaman kotu na yau  Talata.

Haka kuma mai shari’ar ya tabbatar da zaben da tsagin tshohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar.

A cewar mai shari’ar zaben na bangaren Shekarau ya samu sanya hannun mutum 7 daga cikin wadanda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano domin gudanar da zaben.

Cikin abinda tsagin Shekarau ya gabatar, gaban kotun shi ne tsagin na gwamna Ganduje bai gudanar da zaben matakin kanan nan hukumomi da mazabu ba.

Idan za a iya tunawa a watan da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugabancin jam’iyya APC a jihohin kasar nan ciki har da nan Kano.

Sai dai a nan Kano an samu rashin hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar.

Hakan ta sanya gwamna Ganduje ya gudanar da zaben tare da wadanda ke goya masa baya a wani wuri daban.

Yayin da Malam Ibrahim shekarau ya gudanar da nasa zaben da a wani wurin daban

Haka zalika tsagin na gwaman Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas  a matsayin shugaba, ya yin da tsagin Ibrahim Shekarau ya zabi Ahmad Haruna Zago a matsayin shugaba.

Continue Reading

Hausa

Yanzu-yanzu: Sarkin tsaftar Kano ya rasu

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Allah ya yiwa Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Ahmed Gwarzo rasuwa.

KANO FOCUS ta ruwaito Sarkin Tsaftar ya rasu ne ranar Laraba a kasar Saudiyya.

Daya daga cikin ‘yan uwan marigayin Alhaji Nasiru Sani Gwarzo ne ya tabbatar da rasuwar tasa ga manema labarai.

Sarkin tsatar ya rasu ne bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya a kasa mai tsarki da ya tafi domin aikin umara.

Kafin rasuwarsa, Sarkin shi ne mataimaki na musamman ga gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kan rigakafin cutar shan Inna.

Continue Reading

Hausa

ASUU ta gargadi Ganduje kan sayar da kadarorin jami’ar Yusuf Maitama Sule

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Kunigyar malaman jami’oi ta kasa ASUU ta gargadi gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya daina kwacewa da sayar da kadarorin Jami’ar Yusf Maitama Sule (YUMSUK).

KANO FOCUS ta ruwaito wannan na kunshe cikin sanarwar da shugaban kungiyar reshen jami’ar ta (YUMSUK Dakta Abdurrazaq Ibrahim ya sanyawa hannun ranar Asabar.

Ta cikin sanarwar kungiyar ta bukaci gwamnan ya gaggauta dawo da wuraren da ya karbe, da kuma filayen da ya siyarwa jama’a.

Haka kuma ta bukaci gwamnan da ‘kada ya sake’ karbe wabi abu ko sayar da filin jami’ar a nan gaba.

“Sayar da kadarorin gwamnati da gwamnanti Kano ke yi ba sabon al’amari ba ne. Babban abin takaicin shi ne yadda ake sayarwa da kuma kwace wasu muhimman wuraren mallakin jami’ar da ke tasowa”

Wuraren da aka kwace

Kugiyar ta bayyana wasu muhimman wuraren jami’ar da aka kwace da suka hadar da cibiyar koyar da sana’o’in dogaro da kai da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.

Haka kuma gwamnan ya kwace tsangayar nazarin al’amuran lafiya da ke Asbitin kwanar Dawaki.

“Wannance ma ta sanya dole aka dawo da daliban da ke karatu a kwanar Dawaki zuwa cikin jami’ar da ke kan titin zuwa Kabuga”.

Haka kuma kungiyar ta ce gwamnan ya yanka filaye a wuraren da suke mallakin jami’ar ne ya kuma sayarwa da jama’a.

Za mu duki matakin shari’a

Kungiyar ta ASUU ta ce za ta ci gaba da sa ido da kuma matsawa gwmnanati wajen ganin ta dawowa da jami’ar wuraren da ta kwace.

A cewarta ya zama dole gwamnati ta dakatar da sayarda filayen makarantar, ko kuma ta dauki matakin shari’a.

Ta kuma yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da ke da alaka da al’amarin su sanya baki domin ceto makarantar da ga fadawa halaka.

Continue Reading

Trending