Connect with us

Hausa

Yadda Abdullahi Abbas ya sa aka kona ofishin mu-Barau Jibril

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Sanatan Kano ta Arewa Barau I Jibrin ya zargi shugaban jam’iyyar APC tsagin gwamnan Kano Abdullahi Abbas da kona masa ofishi.

Haka kuma sanatan ya zargi  shugaban karamar hukumar Gwale, Khalid Ilyasu Diso da kuma mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan al’amuran na musamman Murtala Gwarmai  da hannun a ciki.

Mai magana da yawun Sanata Barau, Shitu Madaki Kunci ne ya bayyana hakan ya yin da yake zantawa da KANO FOCUS ranar Alhamis.

Madaki ya ce basa kokwanto kan zargin da suke yi a kan mutanen uku, acewarsa ba za su bar abin ya tafi hakaba, ba tare da daukar mataki ba.

“Abdullahi Abbasa da Honorable Khalid Diso, da Gwarmai  S A sun jagoranci gungun wasu matasa yan bata gari zuwa wannan ofis inda suka faffasa kuma saka sa wuta a wannan waje”

Ya ce tuni suka fara hada bayanai kuma da zarar sun kammala za su shigar da kara a kotu.

Yadda al’amarin ya faru.

Da safiyar yau ne wasu matasa dauke da muggan makamai suka farwa ofishin jam’iyyar APC na jihar Kano tsagin Malam Ibrahim shekarau, wanda mallakin Sanata Baraune.

Matasan sun cinna wuta a wurare da dama na ofishin tare da farfasa gilasansa da kuma sace wasu muhimman abubuwa da ke cikinsa.

Muhammad Shehu shaidar gani da ido ne ya ce matasa sun fito ne daga harabar Sakatariyar Audu Bako, suka kuma bi kan titin Sokoto suka bullan kan titi Maiduguri.

da ga nan ne kuma suka isa inda ofishin ya ke suka kuma sa duka tare da cinna wutar.

“Matasa ne aka turosu da makamai da galan galan na fetur zuwa ofishin nan na Barau, kawai sun sa duka sun faffasa wajen sun saci kujeru.

“Abinda zai baka haushi wai motar ‘yan sanda na binsu a baya daya gaba daya a baya, akwai ma ‘yan sandan da na sansu da idona.

“Jami’an gwamnati muke zargi da turosu, su ne nan suka sakasu yin wannan aikin.

Shi ma Ibrahim Jamilu ya ce a gabansa matasan suka isa ofishin dauke da makamai masu tarin yawa, suka kuma sa duka kan mai uwa da wabi.

“Harga Allah a gabana suka zo sun kai su kunsan dubu da adduna da wukake suka fara kona wurin.

“Nan take muka fara waya muna kiran mutanenmu, muna gaya musu su zo za a kona ofishin Barau.

“Suna ganin mun fara yawa ne kuma sai suka fara guduwa daga wurin. Acewarsa.

Yadda na sha da kyar

Isma’il Muhammad da ke gadin ofishin ya ce ba dan ya buya a bandaki ba da tuni matasan sun kashe shi.

Ya ce Allah ne kadai ya kubutar da rayuwarsa, ya sa ya kewaya bayan ofishin, basu same shi a ciki ba.

“Na gansu dauke da makamai masu tayar da hankali da suka kidimanin rayuwa.

“Sun shigo da fetur ne a galan, ai idan aka ce maka adadinsu ya kai dubu bazan musaba, sai da na gudu fah, karshe a bandaki na buya.

“Ta kan titin Maiduguri suka bullo babban tititin da ko shaidan ne ya biyo sai an ganshi, sai daga baya kuma yan sanda suka zo.

Abdullahi Abbas yaki magantuwa

A kokarin jin ta bakin Abdullahi Abbas kan zargin da ake yi masa mun ziyarci gidansa, inda aka ce bai sakko ba.

Bayan mun jira ne kuma ya fita zuwa filin jirgin sama domin zuwa Abuja.

Mun kuma bishi har filin jirgin saman sai dai hakanmu bai cimma ruwa ba domin yaki cewa komai.

An kama mutum 13

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane 13 cikin masu tada husumar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da tsakar ranar Alhamis.

Ya ce an kamasu da nau’in makamai iri-iri, da suka hadar da wukake, da gorori, gariyo da barandami.

Kiyawa ya ce tuni kwamishinan ‘yan sandan Kano Shu’aibu Sama’ila Dikko ya bayar da umarnin a fadada bincke kan al’amarin.

Sakatariyar Audu Bako ce matattarar ‘yan daban

An dai ga matasan sun fito daga sakatariyar Audu Bako dauke da makaman, inda suka bi kan titin Sokoto, zuwa Cinimar  Marhaba suka bulla kan titin Maiduguri.

Haka zalika bayan kammala aikinsu an gansu sun koma cikin sakatariyar suna sauya kaya, daga nan suka tafi gida.

Haka zalika an ga yadda suka dinga fada da junansu bayan fitowa daga Sakatariyar harma aka jikkata wani matashi da aka yasar bakin hanya.

Matashin dai ya sha suka da wuka a wuyansa da kansa, inda jini ke kwarara, amma aka ransa wanda zai kai masa dauki.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

An fake da taimako, ana yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Published

on

 

 

Misbahu Hamza

 

Zuwa Ga Gwamnatin Jihar Kano, Masarautar Kano, Hukumar Hisba, Da Ƙungiyar Mallaman Jihar Kano

Assalamu Alaikum,

Da sunan ƴancin ɗan Adam; da sunan nema wa ƴaƴanmu mata ƴanci da sana’a mai ɗorewa; da sunan taimakawa marayu, gajiyayyu da masu buƙata ta musamman, ana ta ƙoƙarin yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Ana yaɗa wannan manufa ne a bainar jama’a babu kunya ballantana ganin girmanku ko shakkarku a matsayinku na masu faɗa a ji a jihar Kano—a makarantu da unguwanni. Abin takaici ma har da ma a tsakanin ma’aikatun gwamnati (masu ɗamara)!

Ƙungiyar da ta ke ta wannan mummunan aiki a jiharmu ita ce “Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality.” Suna kiran kansu “WISE” a taƙaice kuma a bayanin da muka gani a shafukan su, har ofishi suke da shi mai zaman kanshi a Yankaba Kawaji, Bompai GRA, Kano.

A wani bayani da muka gani a shafukan wannan ƙungiya, mun ga sun taɓa haɗa bita wa jami’an Hisba, da na KAROTA, da na NDLEA, da sauransu!

Domin tabbatar da duk waɗannan abubuwa, a duba shafinsu kawai na Facebook mai suna “Wise Wage.”

In har wannan ƙungiya ta yi ƙarfin da za ta tara waɗannan jami’ai a wuri guda da sunan yi musu bita—a kan ko ma mene ne—to muna tsoron irin tasirin da suka riga suka yi a cikin jihar mu. Jihar musulunci.

Za ku iya tunawa a makon nan me ƙarewa ne ake ta dambarwar kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ta karɓo daga ƙasashen Turai wanda ake zargin cewa ɗaya daga cikin sharuɗɗan amfana da wannan maɗuɗun kuɗaɗe shi ne a sakarwa masu da’awar luwaɗi da maɗigo mara, irin su WISE, su fantama baɗalarsu yadda suke so.

Wannan ya jawo kace nace a ƙasarnan. Kuma mun ga yadda Mallaman jihar Kano ku ka tashi tsaye a mimbari, kamar yadda muka yi tunanin za ku yi, domin yin tofin Allah tsine da wannan yunƙuri matuƙar ya tabbata gaskiya.

Wannan dambarwar ta ƙara bayyanar mana cewa a ƙasarnan akwai doka da kai tsaye ta yi hani da duk wani yunƙuri ko yaɗa manufar luwaɗi da maɗigo. Kuma mun ƙara samun natsuwa ganin yadda Musulmi da Kirista suka haɗa kai domin barranta da wannan ɓarna.

Da wannan muke kiran Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, da Shugaban Hisba ta Kano, Mallam Aminu Daurawa, da Shugabancin Kungiyar Mallaman Jihar Kano, da su tabbatar wannan ƙungiya ta WISE ta tattara ƙomatsonta ta bar mana gari kuma a haramta mata aiki a jihar ta kowace hanya da za a iya.

Al’ummar jihar Kano amana ne a wajanku! Kuma Allah zai tambaye ku amanar da ya damƙa muku ranar alkiyama!

Mu mun yi namu—isar muku da saƙon. Idan da ba ku san da wannan kungiya ba ko aiyukanta, to yanzu mun sanar da ku.

Bissalam,

Misbahu Hamza

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending