Connect with us

Hausa

Anyi jana’izar Sarkin Bai a garin Danbatta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

 

An gudanar da jana’izar Sarkin Bai Alhaji Muktar Adnan wanda ya ya rasu cikin daren juma’a.

KANO FOCUS ta ruwaito an gudanar da jana’izar ne da misalin 2:30 jim kadan bayan Kammala sallar juma’a a Kofar fada da ke garin Danbatta.

Babban limamin Danbatta Malam Nasir Abubakar ne ya sallace shi.

Cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero, sai kuma Sarkin Kazaure Ahaji Najib Hussain Adamu.

Haka kuma cikin mahalartan akwai tsohon gwamnan Kano sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Jim kadan bayan kammala sallar ne aka binne shi kusa da Mahaifinsa a daya daga gidajen ‘ya’yansa.

Wanene Sarkin Bai?

An Mukhtar Adnan a shekarar 1926 a garin Danbatta, ya fara karatun sa na Elementari a makarantar Danbatta a shekarar 1935 daga bisani kuma ya shiga makarantar Midle ta Kano 1939 zuwa 1944.

Mahaifinsa shi ne Mohammed Adnan wanda ya rike mukamin Danmaje a Babura, sannan ya dawo garin Danbatta a matsayin  Sarkin Bai tsakanin 1942.

Ya kuma halarci makarantar harkokin mulki ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ya fara aiki da  hukumar N A, daga 1948 zuwa 1950 inda ya rike manyan mukamai a wancen lokacin ya kuma samu lambobin girma da dama.

A shekarar 1954 ne kuma mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi I ya nadashi sarkin Ban Kano kuma dan majalisar sarki.

Haka kuma a shekarar 1968 gwamnan Kano Audu Bako ya nadashi a matsayin kwamishinan Ilimi na farko a jihar Kano.

Ya nada sarakuna har hudu a Kano da suka hadar da Malam Muhammadu Inuwa a watan Afrilun 1963, sai kuma Alhaji Ado Bayero a shekarar 1963, sai Muhammadu Sanusi II a shekarar 2014, sai kuma Sarkin Kano na yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero.

Ya rasu ranar Juma’a 03 ga Disambar shekarar 2021, yana da shekara 95.

Shi ne hakimi mafi dadewa a masarautar Kano da ya shafe shekara 65 yana hakimci.

Gwamnatin Kano ta nuna alhininta

Duk da cewa ba a ga fusakun jami’an gwamnatin Kano a wurin jana’izar ba, sai dai gwamnatin ta fitar da sanarwar nuna alhininta.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labara gwamnan Kano  Abba Anwar ya fitar ta ce jihar Kano ta rasa babban bango.

Sanarwar ta ce Sarkin Bai ya rasu a lokacin da jihar Kano ke tsananin bukatar irinsu.

Haka kuma gwamnan ya ce jihar Kano ba za ta taba mantawa da irin rawar da ya taka wajen inganta ilimi ba.

A don hakan ne ma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga yan uwan mamacin da ma al’ummar jihar Kano baki daya.

Buhari na alhinin rasuwarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masarautar Kano bisa rasuwar ta Sarkin bai.

Cikin wata sanrwa da jami’in yada labaransa Garba Shehu ya fitar ta ce rasuwarsa ba wai asarace ga jihar Kano ba har  ma da kasa baki daya.

A cewarsa tsahon shekara 63 da ya kwashe yana sarauta a Kano da kuma kasancewarsa bulalaliyar Majalisa a baya ya tabbatar da matsayinsa na wanda ya taka rawa wajen gina kasa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

An fake da taimako, ana yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Published

on

 

 

Misbahu Hamza

 

Zuwa Ga Gwamnatin Jihar Kano, Masarautar Kano, Hukumar Hisba, Da Ƙungiyar Mallaman Jihar Kano

Assalamu Alaikum,

Da sunan ƴancin ɗan Adam; da sunan nema wa ƴaƴanmu mata ƴanci da sana’a mai ɗorewa; da sunan taimakawa marayu, gajiyayyu da masu buƙata ta musamman, ana ta ƙoƙarin yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Ana yaɗa wannan manufa ne a bainar jama’a babu kunya ballantana ganin girmanku ko shakkarku a matsayinku na masu faɗa a ji a jihar Kano—a makarantu da unguwanni. Abin takaici ma har da ma a tsakanin ma’aikatun gwamnati (masu ɗamara)!

Ƙungiyar da ta ke ta wannan mummunan aiki a jiharmu ita ce “Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality.” Suna kiran kansu “WISE” a taƙaice kuma a bayanin da muka gani a shafukan su, har ofishi suke da shi mai zaman kanshi a Yankaba Kawaji, Bompai GRA, Kano.

A wani bayani da muka gani a shafukan wannan ƙungiya, mun ga sun taɓa haɗa bita wa jami’an Hisba, da na KAROTA, da na NDLEA, da sauransu!

Domin tabbatar da duk waɗannan abubuwa, a duba shafinsu kawai na Facebook mai suna “Wise Wage.”

In har wannan ƙungiya ta yi ƙarfin da za ta tara waɗannan jami’ai a wuri guda da sunan yi musu bita—a kan ko ma mene ne—to muna tsoron irin tasirin da suka riga suka yi a cikin jihar mu. Jihar musulunci.

Za ku iya tunawa a makon nan me ƙarewa ne ake ta dambarwar kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ta karɓo daga ƙasashen Turai wanda ake zargin cewa ɗaya daga cikin sharuɗɗan amfana da wannan maɗuɗun kuɗaɗe shi ne a sakarwa masu da’awar luwaɗi da maɗigo mara, irin su WISE, su fantama baɗalarsu yadda suke so.

Wannan ya jawo kace nace a ƙasarnan. Kuma mun ga yadda Mallaman jihar Kano ku ka tashi tsaye a mimbari, kamar yadda muka yi tunanin za ku yi, domin yin tofin Allah tsine da wannan yunƙuri matuƙar ya tabbata gaskiya.

Wannan dambarwar ta ƙara bayyanar mana cewa a ƙasarnan akwai doka da kai tsaye ta yi hani da duk wani yunƙuri ko yaɗa manufar luwaɗi da maɗigo. Kuma mun ƙara samun natsuwa ganin yadda Musulmi da Kirista suka haɗa kai domin barranta da wannan ɓarna.

Da wannan muke kiran Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, da Shugaban Hisba ta Kano, Mallam Aminu Daurawa, da Shugabancin Kungiyar Mallaman Jihar Kano, da su tabbatar wannan ƙungiya ta WISE ta tattara ƙomatsonta ta bar mana gari kuma a haramta mata aiki a jihar ta kowace hanya da za a iya.

Al’ummar jihar Kano amana ne a wajanku! Kuma Allah zai tambaye ku amanar da ya damƙa muku ranar alkiyama!

Mu mun yi namu—isar muku da saƙon. Idan da ba ku san da wannan kungiya ba ko aiyukanta, to yanzu mun sanar da ku.

Bissalam,

Misbahu Hamza

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending