Hausa
Muhimancin dawo da Kungiyar Kano Pillars gida
Jamilu Uba Adamu
Wasan Kwallon kafa kamar yadda ma su bibiyarsa suka sani, yana da shiga rai, kuma yana motsa zuciya. Musamman akan goyan baya na kungiyar da mutum yake so.
Ban yi tsammanin akwai wani magoyin bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da yake farinciki da halin da kungiyar take ciki a yanzu ba.
Ita dai wannnan kungiyar wasan ta Kano Pillars ita ce daya tilo da take wakiltar jihar Kano a gasar firimiya ta kasa,
Don haka ba wani dan asalin jihar Kano da zai murna ko farinciki da wasan da kungiyar take yi a jihar Kaduna.
Lokuta da yawa magoya baya na da rawa mai muhimancin da suke takawa wajen kawo canji akan tabarbarewar lamari na kungiya, kasancewar shugaba ko masu madafun iko na kungiya na iya zuwa su tafi amma magoya baya kuwa suna nan.
A ranar asabar din da ta gabata, na samu damar halartar filin wasannin dake Kofar mata, kuma idona ya shaida mun ganin filin wasan.
A zahiri ban ga wani dalili da ya sa hukumar gudanar da gasar ta firimiya ta ki amincewa kungiyar ta Kano Pillars ta rika yin wasannin nata a filin ba.
Kasancewar da akwai filayen kungiyoyin da basu Kai irinsa ba, amma ana buga gasar acikin su.
A harkar wasan kwallon kafa jihar Kano akwai mutanen da ake yi wa kallon cewar sune yakamata su jajirce wajen ganin sun taimaka don ganin Kungiyar ta dawo tana yin wasan ta a gida.
Amma sai dai ana ganin kamar siyasa a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar wasan na Kwallon Kafa anan jihar ta Kano na da alaka da wannan abun alhinin da yake faruwa a harkar wasan na Kwallon Kafa.
A duk matsalolin na Kungiyar ta Kano Pillars ina ganin ba wacce takai girman wannan matsala ta rashin yin wasan kungiyar a gida. Wannan abun alhini ne, kuma abun kunya ne.
Yana da muhimancin gaske kungiyar ta dawo gida ta cigaba da buga wasanninta. Hakan zai taimaketa wajen samun nasara a wasannin nata.
A karshe dai abun fatan shine, Allah ya hada kan jagororin dake tafi da shugabancin harkar wasanni da kwallon kafa a jihar Kano, kuma Allah ya ba su ikon dagewa wajen ganin sun dawo da wannan kungiyar buga wasanninta gida, jihar Kano. Amin.
Jamilu Uba Adamu
Mai sharhi kan al’amuran wasan Kwallon Kafa ne.
Hausa
EFCC arraigns one for N108 million fertiliser fraud in Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
The Kano Zonal Directorate of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, has arraigned one Sanusi Hashim for allegedly misappropriating and converting to his personal use, the sum of 108 million Naira.
KANO FOCUS reports that Hashim was arraigned before Justice Kabiru Dabo of the Kaduna State High Court sitting in Zaria on a one -count charge of misappropriation contrary to Section 293 and punishable under section 294 of the Penal Code.
He was alleged to have collected a total sum of 108 million Naira from one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer but instead misappropriated and diverted the money for his personal use.
The lone-count charge reads ‘’That you Sanusi Hashim sometime in April 2020 under the jurisdiction of the Kaduna State High Court dishonestly misappropriated and converted to your own use, the sum One Hundred and Eight Million Naira (N108,000,000) property of one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer from Indorama Eleme Fertilizer and Chemicals and you thereby committed an offence under Section 293 and punishable under Section 294 of the Penal Code’’.
The defendant pleaded not guilty when the charge was read to him.
Counsel to the prosecution, Bright C. Ogbonna prayed the court for a trial date in view of the defendant’s plea.
Consequently, Justice Dabo remanded the defendant in a Correctional Centre and adjourned the matter to February 10, 2025 for hearing of bail application.
Hausa
Gov. Yusuf Directs Reassigned Commissioners to Handover and Assume Duties by Tuesday, 17th December
Mukhtar Yahya Usman
The Governor of Kano State, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has directed all reassigned commissioners to ensure a smooth handover and assumption of duties by Tuesday, 17th December 2024.
Speaking through his spokesperson, Mr. Sanusi Bature Dawakin Tofa, the Governor stated that the cabinet changes will take full effect during the next council meeting on Wednesday, 18th December 2024.
He emphasized the need for the completion of all transition processes before then.
“All commissioners affected by the changes are directed to hand over their responsibilities between Monday, 16th and Tuesday, 17th December 2024,” the statement reads.
The Governor further urged members of the state executive council to redouble their efforts and uphold a strong spirit of teamwork, dedication, and commitment to supporting his administration in serving the good people of Kano State.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”