Connect with us

Hausa

Idan Malamai ba su fadawa shugabanni gaskiya a munbari ba, a Ina za su fada?

Published

on

Daga Salisu Ismail Kabuga

Ita gaskiya, gaskiya ce in dai gaskiyar ce.

Ya yin da aka tozarta gaskiya, ko kuma sai an zabi wanda za’a gayawa gaskiya, ma’ana sai ma su rauni (Talakawa) za’a fadawa gaskiya ba bu shakka an tozartar da gaskiya.

Me ce ce gaskiya kuma a ina za’a fadi Gaskiya?

A takaice Gaskiya, Nasiha ce, wadda ake fadawa mutum/mutane cikin zance ko a wa’azance kamar yadda Malamai ke yi idan za su warware Zare-da-abawa kan wani abu ya yin da suke kan munbarin khudba da ma a kowanne zarafi da suka samu na fede gaskiya.

Irin wannnan muhimmin aiki na fadar gaskiya, ana iya yinsa a ko ina matukar akwai zarafin yin hakan. Kuma gaskiya ta kowa ce. Ma’ana ana iya gayawa kowa gaskiya tunda dai kamar yadda nace a takaice gaskiya Nasiha ce, Ana iya yiwa Shugabanni/Masu mulki masu kudi da Malam Talaka.

Me ye aibu idan an fadi gaskiya?

Matukar gaskiya gaskiyar ce babu wani aibu ga dukkannin bangarori biyu, wato ga wanda ya fadi gaskiya da kuma wanda aka fadawa gaskiyar,  Amma kuma ita gaskiya daci gare ta. Domin ina iya tunawa yadda a wake, Marigayi Sa’adu Zungur ke fadi.

Muddun mutum ko mai wa’azi akan gaskiya yake magana, to kuwa komai fadin gaskiyar ya jawo ta biya, cewar Sa’adu Zungur cikin wakensa.

Yadda malamai a dukkannin sassa suka dada zage damara wajen tunasar da Shugabanni halin da kasa ke ciki na rashin tsaro da kuncin rayuwa da ake ciki a yanzu abin a yaba ne, domin duk Dan’Adam kasasshe ne a koda yaushe yana bukatar a tunasar dashi game da yin abinda ya kamata, kuma ina kyautatawa Malaman nan zaton cewa sunayi ne domin neman gyara.

A ce a wayi gari ana yiwa malamai barazanar raba su da wurare ko munbarorin wa’azinsu domin kawai suna isar da nasiha ga shugabanni kai tsaye daga inda suke da ikon aikewa da sako/wa’azi, yin hakan tamkar komawa zamanin jahiliyya ne.

Ma su cewa, Malamai ba za su yiwa shugabanni Nasiha ko jan hankalinsu akan munbarin karatu/Khudba ba, to a ina kuke so suyi ?

Shin kuna zaton duk wanda nasiha bata yi masa dadi daga munbari ba zayi yi masa dadin ji idan gaka-ga-shi a fadarsa?

Shin ko kuma kuna ganin cewa su wadanda ke kewaye da shugabanni da kuma Yan sa kai wato yan jagaliyar dake kewaye da shugabannin zasu bar Malami ya samu ganin shi (shugaban) cikin karamci, domin ni dai a iya sani na a halin da ake ciki ganin shugabanni musamman na siyasa ba sauki bare shi ba a irin wannan yanayi da ‘yan bani na iya ke kewaye da fadar masu mulki domin kwadayin wani abu.

Haka kuma ina kuka kai tunanin da mafi yawan mutane suke yi cewa, akasarin wadan da shugabanni ke rufe kofa dasu, sunje karbar nasu kason ne musamman idan aka ga Malami ne ?

A tambayi duk wani shugaba cewa ya yake ji idan akace ga shi can Malam wane akan munbarin karatu/khudbar sa ya na fahimtar da jama’a game da wani abin alkhairi da shugaban yayi ko kuma ma ace gashi can yanayi masa addu’a tare da dalibansa ?

Idan har yin hakan ba ketare hakkin iyakar malunta bane, To ta yaya yin wa’azi gare shi akan ya gyara wani abu da yake damun Jama’a akan munbarin da ada aka yabeshi zai zama kuskure? Kuma idan har yabon da Malamai kewa shugabanni akan munbari yayin da sukayi abin yabo bai zama siyasa ba ta yaya gaya musu cewa su gyara ya zama siyasa ?

Dogaro da wannan nazari nake ganin, a ka’idance dama kamata yayi ace Malamai su dinga fadin gaskiya ko wacce iri yayin da suke kan munbarin karatu/khudba domin gaskiya ta kowa ce, ala basshi idan hali ya basu dama wataran sun rabauta da ganin shugaban da suka aikawa da sakon a baya ta kan munbari to sai ku ji tsoron Allah su karasa aikin su na fadin gaskiya gaba-da-gaba kamar yadda ake yiwa dalibai.

A gayawa Duk wani Shugaba dake ci ko Yan kanzagin sa, Shin basu san cewa su MALAMAI sune magada Annabawa ba?

Shin dama akwai abinda addini baiyi magana akan sa ba? Ko kuma ya ware cewa ba za’ayi magana akansa ba ?

Babban aikin Malamai shine shiryadda Al’umma wajen yin dik wani abu dai-dai (politics inclusive), yadda Allah ya ke so da kuma yadda rayuwar Al’umma zata inganta a duniya, kuma idan akace Al’umma ba ana nufin Talaka ba kawai, harda Shugabanni a kowanne mataki.

Idan har Malamai ba za su gayawa Gwamnati da shugabanni inda suka gaza ba ko kuma abinda ya zama matsalar Jama’a, to waye ya fisu wanda zai gayawa shugabannin indai har abinda ake tunasar dasu gaskiya ne?

Muyi hattara Jama’a !

Kudurce jin haushin Malamai a zuci kawai kan iya hana mutum cikawa da imani domin alamune na munafunci, ballantana yinkurin hana Malamai isar da sakon ayi dai-dai wanda aiki ne da Allah ya daura musu saboda sune masu shiryarwa tun da dai a yanzu babu Annabawa.

Gujewa Malamai ko korarsu daga Munbarin wa’azantarwa ko shakka babu aikine irin na Ashararai wadan da suka sanya duniya a gaba, kuma irin wadan nan mutane da yan kanzaginsu da ace a lokacin Annabawa suka zo wallahi irin sune zaka ga suna futo na futo da Annabawan ko ma su kore su daga gari.

Yana daga cikin alamun rashin rabo da tabewa, ka ga mutum ya futo karara yana fada da gaskiya ko kuma yana kare karya da kuma jin haushin duk abinda Malamai ke fada na gaskiya.

Ko wanne musulmi wakilin Allah ne a bayan kasa, kuma rayuwa bata wanzuwa sai kowannen mu ya amsa tare da isar da wakilcin dake kansa da hanyar fadin gaskiya da aiki da ita, domin Allah ne da kansa ya umarci masu Imani dasu kawarda mummunan abu da hannayen su, ko da bakunan su (wa’azi) ko kuma su kyamaci abin a zuciyoyinsu wanda shine mafi raunin Imani.

Babu shakka, halin da Al’ummar Nigeria ke ciki a yanzu na kuncin rayuwa da rashin tsaro wanda ya haifar mana da zullumi da furgici a birane da kauyuka, A yanzu ne ya kamata kowannen mu ya tashi wajen yin abinda zai iya. Ma’ana Shugabanni nayi, Malamai nayi talakawa ma nayi.

Hakika abin takaici ne matuka ace a irin wannan lokaci da kusan kowanne Dannajeriya, masu karfi da raunana, wadanda ke cikin rigar mulki da wadan da ake shugabanta ke cikin rashin tabbaci saboda ba wanda ya tsira, Amma ace wai a samu wasu daga cikin jama’a suna fushi da yadda Malamai ke gayawa gwamnati gaskiya a munbarin su harma ta kai ga dakatar da wasu ko korarsu da sauya su da wanda zaiyi akasin abinda wanda aka kora yayi.

Shin waima tsakanin fushin Allah dana shugaba idan har ba akan dai-dai yake ba, wanne ne abin tsoro? Kowanne Mai imani ya amsawa kansa.

Wannan na a matsayin irin gudummawar da zan iya bayarwa a matsayina na Dan-kasa da kundun mulkin Nigeria ya sahalewa tofa albarkacin bakinsa kuma banyi wannan rubutu da nufin gusgunawa kowa da kowanne bangare ba sai domin fatan ganin Kasa ta (Nigeria) ta samu zaman lafiya da bunkasar arziki ga kowanne Dan-kasa.

Allah ya fudda Kasa ta daga halin da take ciki a yanzu na rashin tsaro da furgici a dukkanin garuruwan Arewacin Nigeria dama sauran sassa na kasar nan dama duniya baki daya. Barka da Azumi !

Cmrd, Salisu Ismail Kabuga

Dan-jarida daga Kano

mallamkabuga@gmail.com

08052529040

4th, April, 2022/3rd, Ramadan, 1443 AH

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

An fake da taimako, ana yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Published

on

 

 

Misbahu Hamza

 

Zuwa Ga Gwamnatin Jihar Kano, Masarautar Kano, Hukumar Hisba, Da Ƙungiyar Mallaman Jihar Kano

Assalamu Alaikum,

Da sunan ƴancin ɗan Adam; da sunan nema wa ƴaƴanmu mata ƴanci da sana’a mai ɗorewa; da sunan taimakawa marayu, gajiyayyu da masu buƙata ta musamman, ana ta ƙoƙarin yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Ana yaɗa wannan manufa ne a bainar jama’a babu kunya ballantana ganin girmanku ko shakkarku a matsayinku na masu faɗa a ji a jihar Kano—a makarantu da unguwanni. Abin takaici ma har da ma a tsakanin ma’aikatun gwamnati (masu ɗamara)!

Ƙungiyar da ta ke ta wannan mummunan aiki a jiharmu ita ce “Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality.” Suna kiran kansu “WISE” a taƙaice kuma a bayanin da muka gani a shafukan su, har ofishi suke da shi mai zaman kanshi a Yankaba Kawaji, Bompai GRA, Kano.

A wani bayani da muka gani a shafukan wannan ƙungiya, mun ga sun taɓa haɗa bita wa jami’an Hisba, da na KAROTA, da na NDLEA, da sauransu!

Domin tabbatar da duk waɗannan abubuwa, a duba shafinsu kawai na Facebook mai suna “Wise Wage.”

In har wannan ƙungiya ta yi ƙarfin da za ta tara waɗannan jami’ai a wuri guda da sunan yi musu bita—a kan ko ma mene ne—to muna tsoron irin tasirin da suka riga suka yi a cikin jihar mu. Jihar musulunci.

Za ku iya tunawa a makon nan me ƙarewa ne ake ta dambarwar kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ta karɓo daga ƙasashen Turai wanda ake zargin cewa ɗaya daga cikin sharuɗɗan amfana da wannan maɗuɗun kuɗaɗe shi ne a sakarwa masu da’awar luwaɗi da maɗigo mara, irin su WISE, su fantama baɗalarsu yadda suke so.

Wannan ya jawo kace nace a ƙasarnan. Kuma mun ga yadda Mallaman jihar Kano ku ka tashi tsaye a mimbari, kamar yadda muka yi tunanin za ku yi, domin yin tofin Allah tsine da wannan yunƙuri matuƙar ya tabbata gaskiya.

Wannan dambarwar ta ƙara bayyanar mana cewa a ƙasarnan akwai doka da kai tsaye ta yi hani da duk wani yunƙuri ko yaɗa manufar luwaɗi da maɗigo. Kuma mun ƙara samun natsuwa ganin yadda Musulmi da Kirista suka haɗa kai domin barranta da wannan ɓarna.

Da wannan muke kiran Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, da Shugaban Hisba ta Kano, Mallam Aminu Daurawa, da Shugabancin Kungiyar Mallaman Jihar Kano, da su tabbatar wannan ƙungiya ta WISE ta tattara ƙomatsonta ta bar mana gari kuma a haramta mata aiki a jihar ta kowace hanya da za a iya.

Al’ummar jihar Kano amana ne a wajanku! Kuma Allah zai tambaye ku amanar da ya damƙa muku ranar alkiyama!

Mu mun yi namu—isar muku da saƙon. Idan da ba ku san da wannan kungiya ba ko aiyukanta, to yanzu mun sanar da ku.

Bissalam,

Misbahu Hamza

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending