Hausa
Gazawar shugabanni ne rikicin da ya faru a wasan Kano Pillars da Katsina United
Jamilu Uba Adamu
Hamayya da adawa tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar Kano Pillars da Katsina United tsohon lamari ne wanda ya dade a tsakaninsu.
Don haka ne ma kusan duk lokutan da Kungiyoyin biyu za su kara akan tanadi jami’an tsaro na musamman domin kare afkuwar hatsaniya a tsakanin bangarorin biyu.
A wasu lokuta ma akan ba da umarnin yin wasa a tsakaninsu ba tare da ‘yan kallo ko magoya baya ba.
Hatsaniya da rikici marasa dadi sun sha faruwa a tsakanin Kungiyoyin Kwallon kafar dake makwabtan jihohin biyu.
Sai dai hatsaniyar da aka samu a wasan da aka gudanar a ranar Asabar a filin wasa na Sani Abacha dake unguwar Kofar Mata, a jihar kano, tsakanin Kungiyoyin biyu ya yi muni kwarai da gaske.
Dalilin hakan kuwa, shi ne wannann wasa ya kasance na farko a cikin shekara biyu da kungiyar kwallon kafar ta Kano Pillars ta samu damar dawo wa gida jihar Kano don gudanar da wasanninta. Wanda a baya take gudanar da su a Garin Kaduna. Kafin daga baya ta mayar da wasanin nata filin wasa na Umaru Dikko a Jihar Katsina.
A garin na katsina, sun gudanar da wasa biyu, kwatsam ba zato ba tsammani sai ga takarda ta futo daga hannun hukumar gudanar da wasan Kwallon Kafa na ajin kwarraru ta Kasa ( LMC ) an umarci Kungiyar da ta karbi bakuncin Kungiyar Kwallon kafar ta Katsina United a filin wasa na Sani Abacha.
Magoya bayan Kano Pillars sun gaza jure fushi
Mahukuntan kungiyar kwallon kafar ta Kano Pillars tare da jungiyar magoya bayanta ba su yi amfani da wannan damar da suka samu ba, na dawo da kungiyar gida jihar Kano ba.
Kasancewar ba wani tanadi da akai dan hana faruwar barkewar rikici da hatsaniya a filin wasan. A mintuna na saba’in da tara ne alkalin wasa da ‘yan kwallo suka fita daga filin wasa don tserar da rayuwarsu, bayan afkawa cikin fili da wasu masu ikirarin goyan bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suka yi, sun shigo filin da makamai, wasu Kuma na jifa da duwatsu.
A wannnan lokacin wasan Yana kunnen doki (0-0)
A karshe gurbatattun magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta Kano Pillars sun huche haushin su a kan motar ‘yan wasan Katsina United. Inda sukayi wa motar raga-raga.
‘Yan wasan na katsina United ba su samu damar fita daga dakin da aka boye su ba a filin wasan, kasancewar wasu gurbatattun magoya baya na jiran fitowarsu don su ci musu mutunci, har sai misalin karfe takwas na dare kamar yadda na samu labari.
‘Yan wasan, sun yi asarar wayoyinsu, takalma, da wasu abubuwa masu amfani da suka ajiye a cikin motar daukar ta su.
Abun da mafi yawan masu bibiyar wasan kwallon Kafa suke tambaya shi ne; wane shiri shugabannin kungiyar kwallon kafar ta Kano Pillars suka yi don kare afkuwar wannan hatsaniyar?
Wane Dalili ne ya janyo mahukuntan LMC suka ba da izinin yin wannann wasa a Kano ( Kuma harda Yan Kallo ) duk kuwa da cewar sunfi kowa sanin rikicin da aka yi tsakanin nagoya bayan kungiyoyin biyu a Jihar Katsina, wacce ta yi muni kwarai a baya?
Bayan sanin da suka yi sarai na tarihin adawar dake tsakanin kungiyoyin biyu?
Akwai wata riba ko alfanu da wasu ko wani zai anfana bisa faruwar wannann hatsaniyar?
Wacce rawa ko mataki shugabannin kungiyar magoya baya suka dauka wajen ganin an yi wasan lafiya an kuma tashi lafiya, kasancewar sun fi kowa sanin magoya bayan kungiyar?
Wanda suka aiwatar da wannnan aika aika ‘yan kungiyar magoya baya ne ko wasu ne daban suka aiwatar? Idan wasu ne ba ‘yan kungiyar ba, me yasa aka bar su suka bata wa kungiyar suna?
Me ya sa shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ba su samar da kyakkyawan tsaro ba?
Kullum haka za a cigaba ba za ai gyara da wayarwa magoya baya kai ba musamman akan harkar goyan baya ba tare da rigima da hatsaniya ba?
A Ina Kungiyar zata cigaba da wasanni nata?
Wannan sune kadan daga cikin tambayoyin dake bukatar amsa.
Musamman daga wurin shugabannin kungiyar kwallon kafar ta Kano Pillars da kuma kungiyar magoya baya.
Gaskiyar magana dai koma su waye suka aiwatar da wannan aika-aika ba su yi wa magoya baya na gaskiya da ita kan ta kungiyar adalci ba.
Kuma wannan ba nuna kauna ga kungiyar ta Kano Pillars bane. Illa ma dai cutar da Kungiyar da magoya baya na hakika ne.
A karshe, addua ta ga Kungiyar, Allah ya dawo da martabarta da daukakarta. Allah ya kuma kare faruwar irin wannnan lamarin mara dadi a gaba. Ameen.
Jamilu Uba Adamu
Mai sharhi da bibiyar
Wasan Kwallon Kafa ne
jamiluubadamu@yahoo.com.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Kwankwaso Congratulates Gov. Yusuf on NUT Award for Education Reforms
Former Kano State Governor and National Leader of the New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, has congratulated the current governor, Abba Kabir Yusuf, on receiving the prestigious NUT Golden Award from the Nigeria Union of Teachers (NUT) in recognition of his significant contributions to the education sector.
In a message posted on his verified X (formerly Twitter) handle, Kwankwaso commended Governor Yusuf for his unwavering dedication to revitalizing Kano’s education system.
He described the governor as a “game changer” in the sector and encouraged him to remain steadfast in pursuing his educational reforms.
“Congratulations to His Excellency Abba Kabir Yusuf on the NUT Golden Award for his achievements in the education sector,” Kwankwaso wrote.
He further urged Governor Yusuf to strengthen his commitment toward achieving his broader goals in education reform.
The award was presented during the 2024 World Teachers’ Day celebration, which took place at Eagle Square, Abuja.
Organized by the NUT in collaboration with the Federal Ministry of Education, the event brought together teachers and educational leaders from across Nigeria to recognize and celebrate significant achievements in education reform.
Governor Yusuf was honored with the NUT Golden Award for his transformative efforts in rescuing Kano’s education system, which had suffered from years of neglect.
His administration has been lauded for implementing policies aimed at improving school infrastructure, increasing access to quality education, and ensuring the professional development of teachers in Kano.
This recognition comes as part of a broader acknowledgment of his leadership and commitment to enhancing educational opportunities for all in the state.
The event, which marked the 2024 edition of World Teachers’ Day, highlighted the importance of teachers and their role in national development, with the NUT acknowledging the critical support of political leaders like Governor Yusuf, who are spearheading reform efforts.
The governor’s administration has undertaken various initiatives to address the challenges in Kano’s education system, including rebuilding dilapidated schools, recruiting more teachers, and prioritizing student enrollment, especially for girls.
Governor Yusuf’s receipt of the NUT Golden Award serves as a milestone in his administration’s ongoing efforts to reposition Kano as a leading state in education, setting an example for others across the country. His reforms have drawn praise.