Connect with us

Hausa

ADP: Zan kawo karshen matsalolin al’ummar Jigawa-Ibrahim Sabo

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Jam’iyyarADP mai alamar littafi ta tsayar da Alhaji Ibrahim Sulaiman Sabo, a matsayin ɗan takarar gwamna a jihar Jigawa.

Wannan na zuwa ne biyo bayan taron ƙaddamar da takarar tasa, wanda aka gudanar a Alhamis ɗinnan, a helkwatar jam’iyyar dake Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Jam’iyyar ta zabi Sabo ne ta hanyar masalaha, inda delegate 16 suka amince da zabin.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan ayyana takarar tasa, Alhaji Sabo, wanda haifaffen ƙaramar hukumar Taura ne, yace ya shirya tsaf domin ceto al’ummar Jigawa daga ƙangin da manyan jam’iyyun kasarnan na APC da PDP suka jefasu.

Yace sabuwar dokar zabe da gwamnatin APC ta kawo, ta basu cikkaken gwarin gwiwar samun nasara.

“Lokacin PDP, Jonathan ne ke kan mulki, da Allah ya ƙaddara zuwan ƙarshensa, sai ya kawo Card Reader, wanda shine yayi silar faduwarsa. To itama gwamnatin APC da ta kawo dokar zabe, matukar za’abi ƙa’ida, to ta kada kanta.”

Alhaji Sabo ya ƙara da cewa idan suka kafa gwamnati, zasu baiwa bangaren noma fifiko, zuwa fannin lafiya da ilimi da kuma tattalin arziki.

“Bangaren noma, ina tabbatar maka cewa mudai nan a Arewa, mun rike noma, kuma rabon taki da ake, nima manomi ne amma ban taba samu ba, wannan ba ƙa’ida bace. Kamata yayi a tura wakilai ko ina, a gano gonarka hekta nawa ce, kuma buhu nawa ne zai isheka.”

“Na biyu bangaren lafiya, zan tabbatar cewa in Allah ya yarda, mutum yayi haɗari ya karye ko wani abu ya faru, ba zamu bari ya zauna babu kulawar lafiya ba, har yazo ya mutu.” Inji Alhaji Sabo.

Ya kara da cewa “idan kaba mutum wadataccen abinci da lafiya da ilimi ka gama masa komai.”

Tun daga 6 ga watan Yunin da muke ciki ne jam’iyyar ta ADP ta fitar da yan takarar majalisar jiha 30 ta hanyar masalaha, sannan a 7 ga wata, ta zabi yan takarar majalisar wakilai ta tarayya 11, har ila yau ta kaddamar da masu takarar Sanata gida 3, dukkaninsu ta hanyar masalaha.

Shugaban jam’iyyar na jihar Jigawa, Comrade Bua Abdul Azeez, yace sun zabi fitar da yan takarar ta hanyar masalaha ce bisa amincewar yayan jam’iyyar.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa duk da jam’iyyar tasu ƙarama ce, zatayi nasara, kasancewar dukkanin manyan jam’iyyun sun gaza.

An gudanar da taron ƙaddamar da takarar ce gaban idanun wakilan hukumar zabe INEC, da jami’an yan sanda.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

An fake da taimako, ana yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Published

on

 

 

Misbahu Hamza

 

Zuwa Ga Gwamnatin Jihar Kano, Masarautar Kano, Hukumar Hisba, Da Ƙungiyar Mallaman Jihar Kano

Assalamu Alaikum,

Da sunan ƴancin ɗan Adam; da sunan nema wa ƴaƴanmu mata ƴanci da sana’a mai ɗorewa; da sunan taimakawa marayu, gajiyayyu da masu buƙata ta musamman, ana ta ƙoƙarin yaɗa da’awar luwaɗi da maɗigo a jihar Kano!

Ana yaɗa wannan manufa ne a bainar jama’a babu kunya ballantana ganin girmanku ko shakkarku a matsayinku na masu faɗa a ji a jihar Kano—a makarantu da unguwanni. Abin takaici ma har da ma a tsakanin ma’aikatun gwamnati (masu ɗamara)!

Ƙungiyar da ta ke ta wannan mummunan aiki a jiharmu ita ce “Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality.” Suna kiran kansu “WISE” a taƙaice kuma a bayanin da muka gani a shafukan su, har ofishi suke da shi mai zaman kanshi a Yankaba Kawaji, Bompai GRA, Kano.

A wani bayani da muka gani a shafukan wannan ƙungiya, mun ga sun taɓa haɗa bita wa jami’an Hisba, da na KAROTA, da na NDLEA, da sauransu!

Domin tabbatar da duk waɗannan abubuwa, a duba shafinsu kawai na Facebook mai suna “Wise Wage.”

In har wannan ƙungiya ta yi ƙarfin da za ta tara waɗannan jami’ai a wuri guda da sunan yi musu bita—a kan ko ma mene ne—to muna tsoron irin tasirin da suka riga suka yi a cikin jihar mu. Jihar musulunci.

Za ku iya tunawa a makon nan me ƙarewa ne ake ta dambarwar kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ta karɓo daga ƙasashen Turai wanda ake zargin cewa ɗaya daga cikin sharuɗɗan amfana da wannan maɗuɗun kuɗaɗe shi ne a sakarwa masu da’awar luwaɗi da maɗigo mara, irin su WISE, su fantama baɗalarsu yadda suke so.

Wannan ya jawo kace nace a ƙasarnan. Kuma mun ga yadda Mallaman jihar Kano ku ka tashi tsaye a mimbari, kamar yadda muka yi tunanin za ku yi, domin yin tofin Allah tsine da wannan yunƙuri matuƙar ya tabbata gaskiya.

Wannan dambarwar ta ƙara bayyanar mana cewa a ƙasarnan akwai doka da kai tsaye ta yi hani da duk wani yunƙuri ko yaɗa manufar luwaɗi da maɗigo. Kuma mun ƙara samun natsuwa ganin yadda Musulmi da Kirista suka haɗa kai domin barranta da wannan ɓarna.

Da wannan muke kiran Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, da Shugaban Hisba ta Kano, Mallam Aminu Daurawa, da Shugabancin Kungiyar Mallaman Jihar Kano, da su tabbatar wannan ƙungiya ta WISE ta tattara ƙomatsonta ta bar mana gari kuma a haramta mata aiki a jihar ta kowace hanya da za a iya.

Al’ummar jihar Kano amana ne a wajanku! Kuma Allah zai tambaye ku amanar da ya damƙa muku ranar alkiyama!

Mu mun yi namu—isar muku da saƙon. Idan da ba ku san da wannan kungiya ba ko aiyukanta, to yanzu mun sanar da ku.

Bissalam,

Misbahu Hamza

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending