Connect with us

Hausa

Kwanaki goman farkon watan Zul-Hajji, ranar Arfah, layyah da bukukuwan Idi

Published

on

Kwanaki Goman Farkon Watan Zul-Hajji, Ranar Arfah, Layyah Da Bukukuwan Idi

Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Yaku bayin Allah masu girma! Ku sani, daga cikin muhimman lokutan yin ibada, lokuta masu tsada, masu falala, wadanda Allah Madaukaki ya hore wa bayinsa, akwai kwanaki goman farkon watan Zul-Hajji – wato wata na goma sha biyu a jerin kalandar Musulunci kenan, wadanda Allah Ya fifita su a kan sauran kwanakin shekara. Hakika, Imamul Bazzar ya fitar da Hadisi a cikin Musnad din sa, daga riwayar Jabir (RA), yace: lallai Manzon Allah (SAW) yace:

“Mafifitan kwanakin duniya, sune kwanaki goman farkon watan Zul-Hajji.” [Albani ya inganta Hadisin a cikin Sahihut-Targib Wat-Tarhib]

Kuma sannan Abdullahi Dan Abbas ya ruwaito cewa, Annabi (SAW) yace:

“Babu wani aiki da yafi alheri fiye da wanda aka yi a kwanaki goma na farkon Zul-Hajji.” Sai wadansu Sahabbai suka ce: “Koda jihadi ne a wurin daukaka kalmar Allah?” Sai Annabi (SAW) yace: “Eh koda jihadi ne a wurin daukaka kalmar Allah, sai dai idan mutum ya tafi da kansa da dukiyarsa bai dawo da komai ba.” [Buhari ne ya ruwaito shi]

Wadannan kwanaki goma masu daraja ne, masu girma da falala ne, kuma mafiya soyuwa ne a wurin Allah (SWT). Abdullahi Dan Umar (RA) ya ruwaito cewa, Annabi (SAW) yace:

“Babu wasu ranaku da suke da girma kuma mafi soyuwa a wurin Allah fiye da wadannan kwanaki goma na farko Zul-Hajji, don haka ku yawaita tahlili da takbiri da tahmidi a cikinsu.” [Musnad Imam Ahmad, kuma Sheikh Ahmad Shakir ya inganta shi]

Daga cikin darajojin da wadannan kwanaki goma suke da su akwai cewa:

1. Mun sani, Allah Yana yin rantsuwa da wani abu domin Ya nuna muhimmancinsa da girmansa da matsayinsa a wurin sa, kuma Allah Yayi rantsuwa da wadannan kwanaki goma a cikin Alkur’ani Mai girma, a inda yace:

“Ina rantsuwa da alfijir. Da darare goma.” [Al-kur’ani, 89:1-2]

Malamai magabata da suka hada da Abdullahi Dan Abbas (RA) sun ce wadannan darare goma da aka ambata a cikin wadannan ayoyi na Alkur’ani, su ne kwanaki goma na farkon Zul-Hajji.

2. Annabi (SAW) yace wadannan kwanaki goma sune ranaku mafiya alheri a shekara, kamar yadda muka ambata a Hadisi na sama.

3. Su ne ranaku mafiya alheri na yawaita ambaton Allah (wato Zikiri), kamar yadda Hadisin da ya gabata ya nuna.

4. Wadannan kwanaki goma a cikin su ne ake da rana mai kima da daraja, wato ranar Arfah, ranar 9 ga Zul-Hajji, wanda a cikinta ne (ranar Arfah) Allah Ya kammala wannan addini, kuma ya cika wa bayinsa ni’imarsa. A ranar Arfah ne shaidan, iblis la’ananne yake bakin ciki, yake jin haushi, yake kuka da shiga damuwa, saboda rana ce da Allah yake ‘yanta bayinsa daga azaba, kuma rana ce da Allah yake gafartawa dukkanin bayinsa. Kuma yin azumi a ranar Arfah ga wanda baya wurin aikin Hajji, yana kankare kananan zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ake ciki, (manyan zunubai kuma suna bukatar tuba da mayar da hakki ga mai shi).

5. Wadannan kwanaki goma na farkon Zul-Hajji, a cikin su ne ake da ranar “Hajji Mafi girma” wato ranar Idin Layyah (wato 10 ga Zul-Hajji kenan). Kuma kamar yadda muka sani, wannan rana ita ce rana mafi girma a daukacin shekara.

Don haka yaku ‘yan uwana masu daraja, kuyi kokari ku yawaita karatun Alkur’ani a cikinsu, kuyi sallolin nafilah da kiyamul Laili da sadaka da kyauta da alkhairi da yada ilimi da tuba da neman gafarar Allah. Ku yawaita neman gafarar Allah, ta fadin Astagfirullah, kuyi azumi da jikinku, ma’ana ku kaurace wa haram ko fadin haram ko sauraren haram ko cin haram da sauransu. Kuma ku yawaita yin addu’o’in alheri, da addu’o’in zaman lafiya, musamman ga kasar mu Najeriya, da al’ummar Musulmin Najeriya, da al’ummar Musulmin duniya baki daya.

Yaku ‘yan uwana maza da mata! Lallai ya zama tilas dukkanin mu muyi gaggawa wurin ribatar wadannan kwanaki kafin lokaci ya kure muna.

Bayan wannan, yaku bayin Allah! Ku sani, a yau, babu wani aikin da yafi hada dukan Musulmi, matasa da dattawa, maza da mata, bakake da farare, kuma yake kawo farin ciki a fuskar kowa da kowa, kamar bukin ranar Idi da ibadar Layyah. Layyah ibada ce ta sadaukarwa, ta hanyar yanka dabbobi domin neman yardar Allah. Ana yin ta ne domin tunawa da wani muhimmin abin tarihi da ya auku a lokacin da Allah Ya umarci Annabi Ibrahim (AS) da yayi layyah da dan sa Annabi Isma’il (AS). A lokacin da yake shirin aiwatar da umarnin Allah, sai Allah Ya musanya masa da rago mai girma, ya fanshi Annabi Isma’il da shi, wanda Annabi Ibrahim (AS) ya yanka. Lallai Annabi Ibrahim (AS) da dan sa Annabi Isma’il, sunci jarrabawa, domin ya shirya don ya yanka dan sa saboda bin umarnin Allah, shi kuma dan ya amince a yanka shi saboda mika wuya ga umurnin Mahalicci!

Yaku Abokaina masu girma, yanzu gashi ayau, muna jin wahala kwarai ko, wurin yin layyah da dabba (ta hanyar amfani da kudinmu) domin bin umarnin Allah? To ina ace ‘ya ‘yan mu ne Allah yace mu yanka? A gaskiya bai kamata ni da ku mu kasa cin wannan jarrabawa ba. Don haka duk wanda yake da hali don Allah yayi layyah, a madadinsa da iyalinsa.

’Yaku ‘yan uwana maza da mata! Ku sani, za’a iya yanka Layyah a kowane lokaci bayan Sallar Idi har zuwa faduwar rana ta uku a bayan ranar Idin. Wannan na nufin wuni hudu (wunin Idi da karin wuni uku na ayyamut-tashriq). Kamar yadda Imamu Shafi’i ya nuna. Amma a fahimtar sauran manyan malamai: Abu Hanifah da Malik da Ahmad, sun ce ana yin layyah ce a cikin wuni uku. A fara da ranar Idi a kare a wuni na biyu bayan wunin Idi, lokacin faduwar rana.

Ana iya yanka Layyah da rana ko da dare, matukar dai a cikin wadannan ranaku ne, amma yin ta da wuri (jim kadan bayan Sallar Idi) shi yafi.

Sannan Sunnar Layyah ita ce a raba naman kashi uku, kuma ba tilas ba ne a raba daidai-wa-daida. daya a raba wa talakawa da mabukata, dayan a bar wa iyali da makwabta da dangi da abokai, dayan kuma ka yi yadda ka so da shi.

Layyah Sunnah ce mai karfi a kan kowane Musulmi mai hali. Wannan shine ra’ayin akasarin malamai. Amma a wurin wadansu malaman sun ce wajiba ce a kan Musulmin da yake da halin yin ta. Kuma tana daya daga cikin kyawawan ayyuka a Musulunci kamar yadda A’isha (RA) ta ruwaito daga Annabi (SAW) cewa:

“Dan Adam bai taba yin wani aiki a ranar Layyah ba wanda yafi soyuwa a wurin Allah, kamar zubar da jinin dabba (wato yanka dabbar Layyah).”

Kuma galibin malamai sun tafi a kan cewa, yanka Layyah shi yafi alheri a kan yin sadaka da kwatankwacin kudin abin yankar.

Yaku ’yan uwana! Ku sani, ana yin Layyah ne da dabbobin gida, dabbobin ni’ima, wato: shanu da rakuma da tumaki da awaki. Kuma yanka rago/tunkiya da bunsuru/akuya shi yafi a kan sauran dabbobin, saboda Annabi (SAW) bai taba yin Layyah ba face da wadannan dabbobi. Amma ana iya yanka rakuma da shanu lokacin Layyah. Kuma wajibi ne abin yankan ya kasance lafiyayye, kosasshe wanda za’a iya cin naman sa a matsayin ibada ga Allah kamar yadda Allah Yace:

“Kuma wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai ne ita (girmamawar) tana daga ayyukan zukata na takawa (wato tsoron Allah).” [Al-kur’ani,22:32]

Don haka kenan dabbobi marasa lafiya, ko masu aibu basu yin layyah.

Kuma wajibi ne idan rago ne ko tunkiya su haura wata shida kamar yadda Ibn Majah ya ruwaito cewa, sai Jaza’ah za’a yi Layyah da ita. Ga jinsin akuya kuwa wajibi ne ya kai shekara daya. Sannan sa ko saniya shekara biyu, shi kuma rakumi shekara biyar.

Kuma kada ayi Layyah da nakasasshiyar dabba, kamar mai ido daya ko marar lafiya ko gurguwa wadda hakan ya bayyana, ko ramammiya marar mai da nama, kamar yadda Buhari ya ruwaito daga Barra’u Dan Azib (RA), daga Annabi (SAW).

Kuma mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa siffofi hudu da aka ambata a Hadisin za’a iya amfani dasu wajen hukunci a kan duk wata nakasa. Don haka duk wata nakasa da ta kai ta, ko tafi ta, to ba za’a yi Layyah da dabbar ba, kamar makauniya ko marar kafa daya.

Kuma ana iya yin Layyah da dabbar da aka dandake, saboda Annabi (SAW) yayi haka. Haka dabbar da aka haifa ba ta da jela/bindi ko wanda take da rabin jelar, amma wadda aka yanke jelarta/bindinta duka ba za’a yi Layyah da ita ba.

Sannan tunkiya ko akuya daya ta wadatar mai gida yayi Layyah da ita ga kansa da iyalansa. Kuma ya halatta mutum bakwai su yanka saniya ko rakumi daya a matsayin layyarsu. Kamar yadda Jabir Dan Abdullahi (RA) ya ruwaito cewa Annabi (SAW) yayi haka a shekarar Sulhun Hudaibiyyah. [Muslim ne ya ruwaito shi]

Kuma mai yin haka zai iya hadawa da iyalinsa a cikin ladan domin a nan daidai yake da mai yanka tunkiya ko akuya.

Kuma bai halatta a yanka Layyah kafin yin Sallar Idi ba, duk wanda ya yanka layyah kafin Idi, to ya sani, ya yanka wa iyalinsa nama sun ci ne kawai, amma bai yi Layyah ba, kamar yadda Annabi (SAW) ya nuna. Kuma idan mutum zai yanka layyar ana so ya ambaci sunan Allah, yace:

“Bismillah, Ya Allah, wannan daga rahamarKa ce kuma dominKa ne.”

Sannan an fi so mutum ya yanka dabbar Layyarsa da hannunsa, idan ba zai iya yin haka ba, to ya halatta ya wakilta wani, kuma ya halarci wurin yankan, sannan ya raba naman kashi uku kamar yadda na ambata a baya. Yaci rubu’i daya shi da iyalinsa, ya bayar da daya rubu’in sadaka, dayan kuma yayi kyauta da shi, kamar yadda Annabi (SAW) ya shaida wa ’yar sa Fatima (RA) cewa:

“Ki kasance a wurin, lokacin da ake yanka dabbar Layyarki. Allah Yana gafarta miki a lokacin digar farko na jininta.” [Baihaki da Abdul Razzak]

• Hikimar shar’anta yin Layyah:

1. Neman kusanci ga Allah ta hanyarta.

2. Raya Sunnar Shugaban Masu Tauhidi, Annabi Ibrahim (AS), wanda Allah Ya umarce shi yayi Layyah da dan sa Annabi Isma’il (AS) sannan daga baya ya musanya shi da rago, Annabi Ibrahim (AS) ya yanka shi a madadin Annabi Isma’il (AS) din.

3. Yalwatawa da kyautata wa iyali a ranar Idi.

4. Sanya jin dadi a tsakanin matalauta da mabukata, ta hanyar ba su sadakar naman Layyah.

5. Yin godiya ga Allah akan yadda ya hore muna dukkan dabbobin ni’ima (wato Bahimatil An’am).

• Abubuwan da wanda yayi niyyar Layyah zai guje musu:

Idan mutum yayi niyyar zai yi Layyah to da zarar watan Zul-Hajji ya kama, ba zai yi aski ko ya yanke farce/kumba/akaifa ba har sai ya yanka abin Layyarsa. Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa cewa Ummu Salmah (RA) cewa, Annabi (SAW) yace:

“Idan kuka ga jinjirin watan Zul-Hajji, kuma dayanku yana da niyyar yin Layyah, to kada ya aske gashinsa ko ya yanke farcensa.” [Muslim]

Haka kada a biya ladan mai gyaran naman Layyah daga abin Layyar. Domin Aliyu Bin Abi Talib (RA) yace:

“Manzon Allah (SAW) ya umarce ni da in lura da Layyar wani rakumi, in bayar da namansa da fatarsa a matsayin sadaka, kuma kada in bayar da komai daga cikinta ga mahauci a matsayin ladan aikinsa. Yace, “Zan iya ba shi wani abu daga abin da na mallaka.” [Muslim]

Ya ku bayin Allah masu girma! Lallai babu shakka, idan watan Zul-Hajji ya kama, kuma shigowarsa ko ganinsa ya tabbata, shugabannin da Allah ya dora wa alhakin yin sanarwa suka yi sanarwa, kuma dayan ku yana da niyyar yin Layyah, to an hana shi ya rage gashi ko ya aske gashi a jikin sa. Haka kuma an hana shi ya rage farce/kumba/akaifa, ko ya rage wani abu daga cikin fatar jikinsa. Amma ba’a hana mata masu niyyar yin ibadar layyah suyi Kitso ko suyi lalle/kunshi ko sanya turare ba, kamar yadda naji wasu suna fada.

Kuma ya kamata mu sani, wannan hukuncin ya shafi mai niyyar yin layyar ne kawai, ban da matansa da sauran iyalin gidansa. Haka nan hukuncin bai shafi wanda aka sanya shi matsayin mai wakiltar layyar wani ba, koda shine zai yanka. Wannan hukuncin ya shafi mai niyyar layyah ne kawai, ya hada namiji da mace duk daya ne, in ban da maganar kitso da lalle. Wannan kuwa saboda ingantaccen Hadisin uwar Muminai Ummu Salmah (RA) tace:

“Lallai Manzon Allah (SAW) yace: Idan aka ga watan Zul-Hajji, kuma dayan ku yayi niyyar yin Layyah, to ya kame daga aske gashinsa da farcensa.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

A wata ruwayar yana cewa: “Kada ya rage wani abu daga gashinsa ko fatarsa.”

Hakika malamai sun tattauna, kuma sun karawa juna sani game da wannan Hadisin. Dan Musayyib yana cewa: Da Rabi’atu Dan Abdurrahman da Imam Ahmad da Imam Is-haq da Dawud da wani bangare na Mabiya Shafi’iyyah sun tafi akan cewa:

“Baya halatta, wato haramun ne ga mai niyyar yin layyah idan watan Zul-Hajji ya kama, ya rage gashi ko farce ko wani abu a fatarsa, har sai ya yanka dabbar layyar sa, saboda Hadisin da yazo a zahiri yana hukunta haka…” [Duba Sahihu Fiqhus-Sunnah wa Adillatuhu, mujalladi na 2, shafi na 375]

Sannan Imamu Malik da Imamu Shafi’i, mabiya shafi’iyyah, sun tafi akan cewa:

“Yin hakan makaruhine, wato ka yanke farce ko ka aske gashi. Hani ne na karhanci wanda aka kyamata, ba haramun bane, saboda Hadisin Nana Aisha (RA)…” [Bukhari da Muslim]

Sannan Majalisar Koli ta kwamitin Malaman Kasar Saudiyyah wato Al-Lajnatid Da’imah…, sun bayar da fatawa cewa:

“An shar’anta wa mai niyyar yin layyah cewa, idan an ga watan Zul-Hajji, kada ya rage wani abu daga jikin fatarsa ko gashinsa ko farcensa, har sai ya yanka abin yankan sa. Saboda Hadisin da Malaman Hadisi guda shida suka ruwaito in ban da Imamul Bukhari, daga Ummu Salmah (RA), tana cewa lallai Manzon Allah (SAW) yace: “Idan anga jinjirin watan Zul-Hajji, kuma dayan ku yana da niyyar yin Layyah, to kada ya rage wani abu daga gashinsa ko farcensa.”

A cikin lafazin da Imam Abi Dawud da Muslim da Nasa’i suka ruwaito yana cewa:

“Wanda yake da abin layyar sa idan watan Zul-Hajji ya kama, kada ya rage wani abu daga gashin jikinsa ko farcensa, har sai ya yanka abin yankan sa.” [Duba Fatawa Al-Lajnatid Da’imah, mujalladi na 11, shafi na 397-398]

Sannan Imam Ibn Hazm (rahimahullah) yana cewa:

“Wanda yake son yayi Layyah, idan aka ga sabon watan Zul-Hajji, to wajibi ne a kan sa kada ya rage wani abu na gashin jikinsa ko farcensa, har sai ya yanka abin yankansa. Amma wanda baya da niyyar yin layyah, wannan hukunci bai hau kansa ba.” [Duba Al-Muhallah na Ibn Hazm]

Sannan Imam Ibn Qudamah (rahimahullah) yana cewa:

“Idan tsayuwar watan Zul-Hajji ya tabbata, to mai niyyar yin Layyah zai kame daga yanke farce da aske gemu idan kuma yayi hakan to sai ya nemi gafarar Allah, babu fansa a kan sa a bisa haduwar Malamai, kuma ya aikata hakan da mantuwa ne ko da gangan.” [Duba littafin Al-Mugni, mujalladi na 9, shafi na 346]

Sannan Imamu Shawkani (rahimahullah) yana cewa:

“Hikimar da ke cikin hani akan rage gashi ko farce ga mai niyyar yin layyah shine, domin ya sami cikakkiyar ladar sa ta layyah, na samun ‘yantawa gaba daya daga wuta zuwa Aljannah, domin kuma yayi koyi da mai yin aikin Hajji cikin Ihrami, an hana shi wadannan abubuwa a lokacin aikin Hajji har sai ya gama jifan farko. To kai ma a nan gida sai aka sa ka kayi hakan don samun ladar ibadah irin ta shi…” [Duba littafin Nailul Autar na Imamu Shawkani, Mujalladi na 5, shafi na 133]

Sannan game da Malaman da suke karyata ko musun wannan Sunnah ta hana yanke farce da aske gashi ga mai niyyar yin Layyah, ina kira da suji tsoron Allah, su daina yin izgilanci da Hadisan Annabi (SAW), su daina batar da al’ummah da sunan bin Mazhaba ko kuma bin wani Malami. Su daina yada irin wannan sabani, domin kaucewa rudani da haifar da rarrabuwa a cikin al’ummah. Suji tsoron Allah, su tabbatar da abinda ya tabbata da ingantattun hujjoji, su daina kore duk wani abu da nassi ya tabbatar da shi, kawai domin son zuciyar su da kuma neman a sansu, ko don girman kai, da kin karbar gaskiya.

Wannan mas’alah ba wata sabuwar mas’alah bace. Malamai magabata nagartattu, masu ikhlasi da tsoron Allah sun yi bayanin ta. Don haka, a yau wani yazo da rana tsaka ya nemi rusa abinda ya tabbata kuma ya inganta a Hadisin Annabi (SAW), kawai don son zuciyar sa, ko don dakusasshen ra’ayin sa, sam wannan ba zai karbu ba a wurin duk wani mai imani, kuma al’ummah ba zasu taba yarda da shi ba. Ina addu’a da rokon Allah ya nuna muna gaskiya ya bamu ikon bin ta, kuma ya nuna muna karya ya bamu ikon guje mata, amin.

A takaice dai jama’ah, layyah ita ce abun da ake yankawa na daga dabbobin ni’ima (wato Bahimatul An’am), kamar yadda bayani ya gabata a baya. Wato rakuma, shanu, awaki da tumaki, a ranar yanka (wato ranar babbar Sallah) da kuma ranakun shanyar nama ko busar da shi (wato ayyamut-tashriq), da niyyar yin ibadar layyah. Sannan a bisa zance mafi inganci daga cikin zantukan Malamai shine, layyah Sunna ce mai karfi ga mai ikon yi (amma wasu malamai suna ganin idan mutum yana da halin yin layyah, to wajibi ce a gare shi).

Kuma lokacin yanka dabbar layyah shine, daga bayan Sallar idi na ranar babbar Sallah har zuwa karshen ranakun busar da nama (wato ranakun 10, 11, 12 da 13 kenan).

Sannan an sunnanta raba naman layyah kashi uku, wato mutum yaci kashi daya da iyalansa, yayi sadaka da kashi daya, kuma yayi kyauta da kashi daya.

Ya ku jama’ah, ku sani, layyah tana da falala mai girman gaske, domin abunda ke cikin ta na lada mai tarin yawa da kuma amfanar da talakawa, da kuma toshe musu hanyar roko domin bukatun su.

Sannan mu sani, ba’a yin layyah ko hadaya da komai sai abinda ya kasance na rakumi matashi mai akalla shekara biyar. Sannan da shanu ko maraki akalla mai shekara biyu. Sannan rago akalla mai watanni shida. Sai taure akalla mai shekara daya.

Sannan game da akuya da rago da taure da tunkiya, ko wannen su yana halatta ne ga mutum daya. Rakumi kuma ga mutane bakwai, sa ko saniya kuma su ma ga mutane bakwai. Kuma ya halatta mutum yayi layyah da akuya ko rakuma ko sa, ga kansa da kuma iyalansa. Kuma ya zama wajibi abunda za’a yi layyah da shi ya kasance mai lafiya, mara aibu ko wata matsala.

Kuma kamar yadda kuka sani, kuma kamar yadda fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi suka sanar, yau muna ranar Asabar, 03 ga watan Zul-Hajji, 1443 AH, wanda yazo daidai da 02/07/2022, kenan daga yau bai wuce saura kwanaki 7 mu shiga babbar Sallah ba (sati daya), idan Allah yasa muna cikin masu yawancin rai.

Ina rokon Allah ya bamu ikon ganin babbar Sallah lafiya, ya bamu hali da ikon sayen dabbar layyah, kuma ya bamu lafiya da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, a kasar mu Najeriya da kuma yankin mu na arewa baki daya.

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawarka a koda yaushe.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah, Muhammad (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi a cikin dukkanin al’amurran mu, amin.

Yaku ‘yan uwana maza da mata! Ina rokon Allah Madaukaki ya amsa min da kuma ku da sauran Musulmin duniya baki daya, kuma Yasa dominSa kadai muke yi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da Sahabbansa. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Ya Allah! Ka taimake mu wurin rayuwa bisa koyarwar Alkur’ani da Sunnah. Ya Allah Ka nuna mana gaskiya kuma Ka bamu ikon bin ta, kuma Ka nuna mana karya Ka bamu ikon guje mata.

Ya Allah! Ka shiryar da mu, Ka kare mu daga ayyukan jahilci da barna. Ka kare mu daga gazawarmu. Ka sanya karshen ayyukanmu su kasance mafi alherinsu da dacewarsu. Kuma Ka gafarta mana Ya Ubangiji.

Yaku ’yan uwana! Ku sani, duk abin da na fada mai kyau a wannan jawabi na yau, ni’ima ce da falala daga Allah Madaukaki, kuma duk wani kuskure daga gare ni ne, kuma ina neman tsarin Allah daga bayar da muguwar shawara, da kuma daga dukkan barna da fitina. Kuma ina rokon Allah gafara idan na ketare iyaka a cikin duk abin da na ce ko na aikata.

Godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Allah da alayensa da Sahabbansa.

Ina mai kammala wannan jawabi nawa, ina mai rokon Allah Madaukaki Ya gafarta mana zunubanmu. Ku nemi gafararSa, Lallai Shi (Allah) Mai gafara ne Mai jin kai.

Daga karshe, yaku bayin Allah! Muna neman taimakon ku matuka, domin ci gaba da gudanar da ayukkan mu na da’awa da yada ilimi da karantarwa da kula da marayun da suke karkashin kulawar mu. Ku sani, wadannan marayu suna bukatar cin naman layyah kamar yadda ‘ya ‘yan mu suke bukata. Ku tallafa masu, kuma sai Allah ya tallafawa ‘ya ‘yan ku a bayan ku. Ku taimaka, kuma sai Allah ya taimake ku a cikin dukkanin abun da kuka sa a gaba. Kun san cewa gaskiyar magana, duk abubuwan da muke yi wallahi makudan kudade muke kashewa wurin aiwatar da shi, domin ayau, babu abunda ake yi kyauta, ba da kudi ba. Don Allah ku taimaka Fisabilillah!

Muna godiya, Allah ya biya ku da mafificin alkhairi duniya da lahira, amin.

Ga lambar Account kamar haka:

Account no. – 0048647196

Account name – Murtala Muhammed

GTBank

Wassalamu alaikum,

Dan uwanku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’ah na Nagazi-Uvete, da Masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene, da suke garin Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za a iya tuntubar Imam ta lambar tarho kamar haka: +2348038289761 ko email: gusaumurtada@gmail.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Gaskiya Kwankwaso ya nunawa Ganduje halasci – Bello Sharada

Published

on

Na saurari jawaban da Sanata Rabi’u Musa  Kwankwaso ya yi a gaban ‘yan jaridar Aso Rock jiya. Magana ta gaskiya a duniyance, Kwankwaso ya nuna wa Dr Abdullah Ganduje halasci na rayuwa da zamantakewa. Amma siyasa ta lalata al’amura a tsakaninsu. Daga abin da na rairaiyo a shekara 24 tun daga 1999 zuwa 2023  na rayuwa a tsakanin Kwankwaso da Ganduje, Kwankwaso da zuciya guda yake tafiya da Ganduje, shi kuma Ganduje likimo ya yi wa Kwankwaso.

Sabanin da ke tsakaninsu kuma, tsarin Kwankwasiyya ne haka. Kwankwasiyya da Kwankwaso Danjuma ne da Danjummai.  Da gangan Ganduje ya ki ragawa Kwankwaso, haka zalika ta hannun Abba K Yusuf, Kwankwaso ba zai ragawa Ganduje ba. Dole sai ya biya farashi mai tsada. Maganar gaskiya a mulkin shekara takwas 2015-2023 na Ganduje zai yi wahala ya kubuta a hannun mutanen Kano da hannun ‘yan Kwankwasiyya. Kuma ba shakka Ganduje zai samu karancin tausayawa. Mutane da yawa za su sha wahala a sakamakon yadda Ganduje ya yi mulki, Abba K Yusuf yake son ya yi nasa mulkin.

Cikin shekaru 24 na mulkin farar hula da muke ciki, an ga mulkin Kwankwaso da Shekarau da Ganduje, zamu ga mulkin Abba K Yusuf in Allah ya nufa da rai da lafiya. Lallai gwamna Kwankwaso na Abba ya bi sannu-sannu. Kwankwaso ya sani nasarar cin zabe ba shi ne  lasisi na Kwankwasiyya tayi duk abin da ta ga dama a Kano ba. Cikin mutanen da suka yi rajistar zabe su, miliyan biyar da dubu dari tara  (5, 921,370) da kuma mutanen Kano gaba daya su kusan miliyan 15 zuwa 20, wanda suka zabi Kwankwasiyya mutum  miliyan daya NE kacal da dubu 19 (1,019,602 ). Akwai mutane dubu dari tara da hamsin da bakwai da basu zabi Kwankwasiyya ba (957,408)  A tsakanin Kwankwasiyya da sauran mutanen da suka je zabe bambancin kuri’a dubu 68 ce.

Duk aikin da za a yi kada a kalli Ganduje da Goggo da ‘ya’yanta da Dan Sarki masu APC, a kalli mutanen Kanon da wajen Kanon da Najeriya.

Bello Muhammad Sharada,
Mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum

Continue Reading

Hausa

Shugabannin Fulani sun goyi bayan takarar Tinubu

Published

on

Aminu Abdullahi

 

 

Shugabannin Fulani wato (Ardo) daga sassa daban-daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu a wani taro da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar lahadi.

A taron da suka yi tare da hadin gwiwar Kungiyar Sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shugabannin sun yi alkawarin yin amfani da ‘yan kungiyar 33,661 wajen tattaro sauran ‘yan uwansu Fulani domin su zabi Sanata Bola Tinubu.

A lokacin da yake nasa jawabin bayan an kammala al’adar Fulani ta rabon goro ga mahalarta taron, shugaban Kungiyar Aliyu Liman Bobboi ya ce raba goron da aka yi yana nufin shugabannin za su koma gida su isar da sakon shawarar da aka yanke a wajen taron zuwa ga mabiyansu.

Ya kara da cewa taron an gudanar da shi ne domin su nuna wa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda, sun kuma yi amanna da cancantarsa, suna kuma masu adduar samun nasara a zabe mai zuwa.

Ya kara da cewa Ardo a matsayinsu na shugabanni suna da ta cewa sosai akan wanda mutanensu zasu zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu za su yi ma su biyayya.

Liman ya yi nuni da makusanta shakikai dake tareda Tinubu kamar Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Badaru na jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani yace wannan na nuni ga yadda Tinubu ya dauki kabilar ta Fulani da muhimmanci.

Kungiyar ta shuwagabannin Fulani ta kuma bawa Tinubu sarautar Barkindo.

Gwamnan jahar kano Abdullahi Umar Ganduje da yake bayani ya yi tsokaci akan irin bajinta da kwarewa da kuma cancantar Tinubu da ya shugabanci Najeriya. Ya kuma kara da cewa Fulani a matsayinsu na kabila dake fuskantar barazana a sassa daban-daban, suna bukatar zabar shugaban da zai iya basu kariya.

Ganduje ya kara da cewa suna nan kan kokarin samarwa Fulani da wani tsari wanda zai bunkasa hanyoyin kiwo a duk fadin kasar nan.

A nasa bayani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Tinubu ya yi tsokaci akan irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa a bangare daya da kuma Fulani a dayan bangaren. Ya nuna cewa alakarsa da Fulani amana ce ta dindindin.

Ya kara jaddada niyyarsa ta samarwa Fulani hanyoyin kiwo na zamani da za su kawo cigaba da kuma yalwa ba tare da tsangwama ba.

Tinubu ya kara da cewa bai taba tsammanin zai hadu da bafulatanin da ya fi shi jin yaren yarbanci ba sai gashi yau ba zato ba tsammani ya hadu dasu. Ya ce wannan abun a yaba ne.

“Wannan itace irin Najeriyarda muke bukata, kasa daya al,umma daya.  Ina mai tabbatar maku idan da zamu kasance anan tsawon sa,o,I biyar iyakacindai zancenda zakucigaba da ji daga gareni kenan.  Ina mai matukar mika godiya da gareku.

“Tabbas makiyayan Najeriya na fama da matsaloli dabban dabban amma ina mai tabbatar maku da cewa munada tsari na musamman da zai magance wudannan matsalolin,’ a cewar Tinubu.

A nasa jawabin Malam Nuhu Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ya cancanta, ya dace wanda kuma zai iya kawo ci gaba mai dorewa ga kabilar ta Fulani.

Ya kuma yi godiya ga goyon bayan da suka bashi tareda alkawarin ba zai ba su kunya ba.

Continue Reading

Hausa

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Baƙon Shehu Maghili

Published

on

Magaji Galadima

 

 

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa  wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar. 

Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.

Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har ya zo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare ma su muhimmanci a fadar Kano, kana kuma ya yi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano da ma nahiyar yammacin Sudan.

Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes.  A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.

Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.

Daganan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano  yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu.

Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune a wannan unguwa tun lokacin har zuwa yanzu, kuma shugabansu Sidi Fari shine Sarkin Sharifan Kano kuma yana da gurbin zama a majalisar Sarkin Kano.

A ƙarshen jawabin Sarki yayi godiya ga Allah wanda Ya ƙudura cewa a zamaninsa ne akayi wannan babbar hobbasa ta sake dawo da wannan tsohuwar alaƙa tsakanin Kano da Nijeriya da kuma ƙasar Aljeriya kamar yadda su Shehu Maghili suka shimfiɗa.

Daga nan kuma sai aka buɗe fage inda malamai da masana suka yita ƙwami akan tarihin rayuwa da rubuce-rubucen Shehu Maghili.

Bayan an tashi daga taron wannan rana ta farko, sai mutane suka yanyame Sarkin Kano, malamai da jami’an gwamnati da baƙi daga sauran ƙasashe kowa burinsa shine ya samu ya ɗauki hoto da Sarkin Kano.

Bayan an fito waje ma haka har zuwa inda ya shiga mota. Mu ma ‘yan kwarakar Sarki da kyar muka yakice ‘yan jarida masu son jin kwakwaf domin yawansu babu lokaci da zamu warware musu zare da abawa. Koda muka isa masauki sai muka tarar ashe tuni wasu jama’ar sun yi kwamba suna jiran isowar Sarki domin su samu su gaisa kuma su ɗauki hoto da shi.

 

Bayan ya shiga ɗaki kuma sai manyan malaman ƙasar su kuma suka yi layin shiga suna yiwa sarki addu’a har saida rana tayi gora sannan jami’an tsaro suka tare mutane suka hana su shiga don a kyale Sarki ya huta.

A rana ta biyu mai martaba Sarki da tawagarsa ya sake komawa wajen taron inda malamai suka ci gaba da gabatar da takardu.

Bayan anyi hutun zango na farko sai mai martaba Sarki ya fita domin kai ziyara ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar ta Aljeriya.

Jakadiyar Nijeriya Hajiya Aisha Muhammad Garba ta taryi Sarki da tawagarsa kuma anyi jawabai masu muhimmanci.

Da maraice kuma har ila yau sai Jakadiyar ta shiryawa mai martaba sarki wata liyafar alfarma a gidanta inda aka gaiyaci ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Aljeriya da kuma wasu malamai daga Nijeriya.

A rana ta uku kuwa mai martaba Sarki ya halarci bikin rufe taron kuma abin ya ƙayatar ƙwarai musamman yadda Sarkin Kanon ya zama tauraro a wajen taron domin dai hankalin kowa na kansa tun daga farko har i zuwa lokacin da aka ja labulen rufe taron.

Da yammaci kuma sai shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya gaiyaci Sarki Aminu zuwa fadarsa inda suka zauna suka yi zantuka na girma. Shugaban ƙasar yace yayi murna matuƙa da karɓar baƙuncin Sarkin, ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar tasu tana sane da tarihin masarautar Kano da rawar da Shehu Maghili ya taka wajen bunƙasa al’adu da addinin Musulunci a birnin Kano.

Shugaba Tebboune yace Sarkin Kano a wannan ziyara shi baƙon Shehu Maghili ne, duk da yayi wafati fiye da shekaru 600, wannan ziyara ta Sarki lallai Shehu Maghili shine sila.

Shi kuma a lokacin da yake maishe da jawabi Sarki Aminu yayi godiya ga Allah da Ya bashi ikon amsa gaiyatar shugaban ƙasar da kawo wannan ziyara, ya yabawa gwamnatin ƙasar Aljeriya saboda ɗawainiyar ɗaukar nauyin wannan taro mai muhimmanci.

Daga nan kuma sai yayi kira ga shugaban na Aljeriya da su haɗu su farfaɗo da hulɗar cinikayya da kasuwanci tsakanin Kano da Aljeriya wanda yace zai taimaka wajen ƙara yauƙaƙa danƙon zumunci tsakanin nahiyoyin biyu. Baya ga wannan kuma da yake ance lokacin iska ake cin ɗan jinjimi sarkin ya bukaci gwamnatin ƙasar ta Aljeriya da ta bawa ɗaliban jihar Kano tallafi na guraben ƙara ilmi a fannoni dabam-daban a jami’oin ƙasar inda shugaban ƙasar nan take yayi wuf yace ya amince da wannan shawara kuma yana jira in Sarki ya koma gida,  ya tsaro jadawalin yadda duk yake so ayi , su kuma in Allah Yaso zasu aiwatar. a nan dai akayi muwafuƙa duk shawarar tasu tazo daidai.

Daga nan suka yi bankwana cikin farin ciki da girmama juna.

A rana ta hudu mai martaba Sarkin Kano tare da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa sun ziyarci garin Ain-Madhi wato ainihin garin da aka haifi Maulana Shehi Ahmadu Tijjani (RA) wanda ya kafa ɗarikar Tijjaniyya.

Sarkin ya ziyarci muhimman wuraren tarihi a garin sannan ya gana da manyan malamai da sharifai zuriyar Shehin inda suka yiwa Sarkin da Kano da Nijeriya  addu’oi na musamman.

A rana ta biyar Sarki ya kammala ziyarar kamar yadda aka tsara, don haka sai ya karyo linzami zuwa gida. Manyan jami’an gwamnati da malamai da kusoshin diflomasiyya da kuma jakadiyar Nijeriya sune suka raka mai martaba Sarki zuwa filin jirgin sama, akayi ban kwana kowa na cike da farin ciki.

Ko shakka babu wannan ziyara da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya kai jamhuriyyar dimokuraɗiyyar ƙasar Aljeriya ta buɗe wani sabon babi na dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasar da kuma Nijeriya. Wannan tagomashi da Sarkin Kano yake samu a duk inda yaje lallai abin godiya ga Allah ne ga duk mai ƙaunar ci gaban jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ɗadin daɗawa gashi har mai martaba Sarki yayi hobbasa har shugaban ƙasar na Aljeriya yayi alkawarin baiwa ɗaliban jihar Kano guraben ƙaro ilmin jami’a kyauta da shiryawa malamai da limamai kwasa-kwasai na ƙara sanin makamar aiki, sannan a waje ɗaya kuma shugaban na Aljeriya ya bada umarni cewa ayi duk abinda za ayi don ganin kwance duk wani daurin Gwarmai don sassauta hulɗar kasuwanci ga ‘yan kasuwar Nijeriya masu sha’awar zuwa Aljeriya.

Mai martaba Sarki ya samo nasarar da ba a taɓa samowa ba a bigiren dangantakar  siyasa ko diflomasiyya, don haka babu abin yi da ya wuce mu yiwa Allah godiya da muka samu Sarki wanda addu’ar magabata da kyakkawar mu’amala  da nagartaccen lamiri suke haskaka masa turbar tafiyarsa, ba kuskunda ba jalla-kujalle.

Fatanmu shine Allah Mabuwayi Ya kara wa Sarki lafiya da jimiri da jinkiri, yadda yake fafutukar samawa al’ummar Kano tudun dafawa, shima Allah Ka dafa masa.

Yadda Sarki ya ɗauko saitin gwadabe tun ba a je ko’ina ba a tafiyar yayi nuni da cewa nan da ɗan lokaci zai ginawa Kanawa rijiya gaba dubu wacce ko da an shekara saran  ruwa toh sai tamfatse.

A laaaafiya baƙon Shehu Maghili !!!

Magaji Galadima
Kachallan Kano
Disamba 25, 2022.

 

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending