KANUN LABARAI
Ranar yaki da cin zarafin mata: Yadda mata a Kano ke rayuwa cikin ukuba
Zulaiha Danjuma
A ya yin da ake bikin ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya, mata a nan Kano sun bayyana yadda suke rayuwa cikin ukuba a gidajen miji da kuma cin zarafinsu akan hanya da makarantu, da kuma yadda dangi ke nuna musu wariya.
A zantawar Kano Focus da wasu mata a nan Kano sun ce rayuwarsu a gidan miji sai godiya, domin kuwa ba ta da maraba da rayuwa akiyama.
Ya yin da wasu kuma suka ce rayuwa a gaban iyayensu da sauran danginsu ita ke zame su ukuba.
Haka zalika wasu matan sun ce suna fuskantar cinzarafi a kan titi, ta yadda maza ke hantarasu yadd suka ga dama.

Matsalolin aure
Rabi’utu Abba uwa ce da ke da yara uku ta shaidawa Kano Focus irin rayuwar ukubar da take fuskanta a gidan mijinta, musamman ma daga bagaren danginsa.
Ta ce har yanzu tana iya tuna yadda dangin mijinta suka yi mata taron dangi wajen zaneta.
“A wata ranar Asabar a watan Fabrairun shekarar 2015 mun tsara cewa a ranar litinin mai zuwa ne za mu fara kai yaranmu makaranta, sai ga yan uwan sa sunshigo da zagi da cin zarafi da barazanar sai sun koreni daka gidan.
“Kafin na ce wani abu kanin mjina ya sureni ya kuma damfarani da kasa, kafin kace kwabo sauran sun rufeni da duka
“Wani abin takaici da ke sosa raina har yanzu shi ne da mijina ya zo kawai sai ya goya musu baya, tundaga wannan rana naji sansa ya fita a raina, a na dai zaman ne kawai” A cewarta.
Hafsat Sani wata daliba ce da ke karatu a jimi’ar Bayero ta shaidawa Kano Focus irin yadda ‘yar uwarta ke karbar ukuba a gidan miji.
A cewarta ‘yar uwarta ta auri wani malamin makaranta a jami’ar Bayero da dake azabar neman mata.
“Abinda zai baka haushi shi ne yadda yake neman matan da basu cika manta ba a jama’ar, ya kuma yi musu barazana da zai kayar da su idan basu amince da shi ba.
Zaben kananan hukumomi: Matashi ya sha fiya-fiya kan dan takara a Kano
Gwanda yawo a kwararo da zaman ukubar gidan miji- matar aure
Ranar bandaki: Yadda matsalar bandaki ke tagayyar dalibai mata a makarantun Kano
“Sanna matar nan ta san dukkanin masha’ar da ya ke aikatawa, amma dai ta ci gaba da zama da shi.
“Dukan tsiya ya ke mata kullum, kuma duk sanda ya dake ta sai ta suma, sannan, yana tsaka da dukan nata zai fara nemanta, yana nemanta yana dukanta.
“Haka kuma baya basu abinci har ma yaran da ya Haifa, amma haka take zaune da shi, sai dai ta bi dangi menam me za su ci.
Ita kuwa wata mata mai suna Esther da ke unguwar Nasarawa a nan Kano ta shaida yadda take shan azaba a hannun mijinta.
Ta ce mijnta na dukanta kowacce rana ba tare da la’akari da lafiyarta ba.
Ta kara da cewa bayan da ta kai kara wajen mahaifiyarsa sai ta ce mata, sai dai ta yi hakuri haka suka yi gadon duka, shima a wurin ubansa ya gada.
Ta ce a yanzu haka gudawa ta ke cikin wata makarantar firamare a nan Kano tana kwana, alabashi da safe sai ta koma gidan.
Auren dole
Zahra Auwal, daliba ce da ke karantar aikin likita a jimi’ar Bayero ta ce mahafiyarta ta tsaneta saboda ta ki auren wani mai kudi da uwar keso ta aura.
A cewar ta hakan ta sanya baya ga tsanar da uwar ta yi mata dangi ma suka sawo ta a gaba.
Ta ce ta shiga damuwa da tashin hankali kan yadda kowa ya tsaneta saboda taki auren mai kudi, a cewarta shekaru hudu ke nan tana cikin wanna bala’i.
“Loacin da nake tasowa babana yana son na yi karatu, haka kuma ya sanyamin son karatun.
“Masu nemana da yawa sun fito amma sai yace musu a bari na kammala karatuna, sai da na gama sakandire ne kuma wani yafito nemana da aka dameni na aurenshi.
“A lokacin shekaruna 16 ina so na ci gaba da karatu, shi kuma irin mutanen nan ne da kasuwace kawai a gaban su ba karatu ba.
“Naki na aureshi ne, kan wannan dalili, amma da yake yana da abin hannu sai ya rufewa dangina ido.
“Mahaifiyata ta tsaneni saboda naki na aureshi, a yanzu da nake karatu a jami’ar Bayero har fargarbar komawa gida nake idan anyi hutu saboda kalubalen da zan fuskanta.
Cin zarafin akan hanya
Wasu matan da Kano Focus ta zanta da su sun shaida irin tasu matsalar da cewar ana cin zarafin su ne akan hanyoyi, musamman ma a cikin kasuwanni.
Zainan Nasiru wata budurwace a nan Kano ta ce ta sha gamuwa da barazana da cin zarafi daga maza.
Zainab ta ce a yanzu haka tana tsoron shiga jama’a ne saboda cin zarafin da ta fuskata.
“Lokacin ina daliba a jami’ar Bayero an kafe sakamakon jarrabawa, mun taru muna dubawa, sai kawai wani yazo ya tsaya a bayana, kamar yana duba nasa sakamkonne, kawai sai ya fara shafani a mazaunaina.
“Na yi zaton cinkonson jama’ ne ya saya ya matseni haka, sai nayi kokarin canza wuri, amma makirin sai ya biyo ni ya ci gaba da shafani har ya kai min hannu kasan.
Dole ne manyan makarantu su bi doka wajen yaki da cutar Covid-19 a Kano-Kwamish
Dalilan da ke sa iyaye yiwa ‘ya’yansu auren dole
‘Yan wasan Hausa a Kano sun yi tofin alatsine ga shugaban Faransa
“Da na fuskanci hakan ne sai na kwalla ihu domin ankarar da jama’a a binda ya ke yi , amma sai ya yi mursisi ya ce shi ko kadan bai aikataba.
“abin takaicin shi ne yadda jama’ar wurin suka goyamasa baya suka nuna ai ma sharri nake son yi masa, lallai wanna cin zarafi ne babba.” A cewar Zainab.
Ita ma wata Fatima Ahmad ta ce cin zarafin da ta fuskanta a cikin kasuwar kantin kwari ne.
Ta ce ta ziyarci kasuwar ta kwari da wasu mata uku domin yin siyayya sai kawai suka fada cikin wani cinkoso.
“Shiga ta cikin wannan cinkosonne sai na ji wani matum na gogamin gabansa a bayana.
“Ba shirin na daskare a wurin saboda tsoro, saboda ban taba fuskantar irin hakan ba.
“Bayan farfadowa daga razanar da nayi ne, sannan na ci gaba da kwarara ihu.
“Kafin a ankara ya bi cikin taron jama’a ya bace sanan na dawo gida na shiga na yi wanka.
“Tun daga wannan rana ban kara zuwa kasuwa ba sai na nemi katuwar jaka na rufe mazaunaina da shi, guduna sake fadawa cikin wannan masifar.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
