KANUN LABARAI
Mata a Kano su yi tanadin tabarya da muciya kafin zaben 2023-Kwankwaso
Mukhtar Yahya Usman
Tsahon Gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga mata a jihar Kano musamman ma ‘yan Kwankwasiyya da su tanadi muciya da tabarya, da kuma majanyi domin tunkarar zaben 2023.
Kano Focus ta ruwaito tsohon Gwamnan na wadannan kalamai ne ya yin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a makon da ya gabata a nan Kano.
Cikin wani faifan bidiyo mai minti 1:28 da ke yawo a kafafene sadarwa na zamani, an gano tsohon gwamnan na cewa ba za su sake yarda da irin zaben shekarar 2019 da ta gabata ba.
Kwankwaso ya kuma gargadi jam’iyyar APC da ke mulki a Kano, cewar ba za su sake aminta da zaben ‘inconclusive’ ba kamar yadda suka yi a shekarar 2019.

“Yanzu sun sha giyar mulki, shi gani ya ke ma kamar ba zai bar mulki ba, sai a tuna yanzu 2023 saura shekara ba iyaka.
“Su fa a tinanisu duk da wannan laifin da suke yi, za su je su hada kai da INEC, su hada kai da masu damara, su hada kai da sauran shugabanni, a zo a sake yi mana ‘inconclusive’ sai kuma mu kyalesu.
“2023 kalarta dabance, idan da wani abu da siyasa da ‘yan siyasa ke cewa ko a mutu ko ayi rai ita ce 2023.
“2023 ina sa rai mata idan Allah ya kaimu lafiya su yi tanadin majanyi, su yi tanadin tabarya, su yi tanadin muciya, wadannan mutanen yan kalilan, ko dai su bari a yi demokradiyya a jihar Kano ko kuma suyi da na sani”

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
