KANUN LABARAI
Lafiya jari:Ko mene ne alaƙar cin goro da hawan jini
Mukhtar Yahya Usman
Goro ɗan itaciya ne da ake amfani da shi domin ci, haka nan alama ce ta karrama baƙo yayin bukukuwa da sauran taruka, musamman a al’adun Najeriya da sauran ƙasashen Afrika ta yamma.
Bugu da ƙari ana amfani da shi a abubuwan sha domin ƙarin ɗanɗano.
Goro na ɗauke da sinadarai da dama da ake alaƙanta su da amfani kamar haka
Wartsakarwa: masu cin goro na amfani da shi domin wartsakewa, ƙara kuzari ko karsashi.

Maganin bacci ko kasala: saboda sinadarin kafin (caffeine) goro na iya rage jin bacci ko kasala.
Maganin tashin zuciya: ana amfani da goro domin magance matsalar tashin zuciya, musamman mata.
Dankwafe sha’awar abinci: Cin goro yayin jin yunwa na da tasirin rage sha’awar cin abincin ko jin matsananciyar yunwa.
Sauran amfanin goro da ke da alaƙa da lafiya
Rage raɗaɗin ciwon ɓarin kai (migraine).
Kashe ƙwayayyakin cuta a jiki.
Taimakawa masu ciwon asma(asthma) wajen buɗe hanyoyin numfashi.
Sai dai duk da waɗannan alfanu da bincike ke alaƙanta goro da shi, bincike ya nuna cewa; baya ga sauran sinadaran da ke cikin goro, goro na ɗauke da sinadarin kafin(caffeine) kaso 2 – 3 cikin ɗari.
Kuma bincike ya yi nuni da hauhawar jini bayan cin sinadarin kafin da ke cikin goro.
Sai dai hauhawar jinin ya fi ƙarfi ga masu cin goron a karon farko ko kuma masu ci jifa-jifa.
Haka nan hauhawar jinin zuwa na wani ɗan lokaci ne da sinadarin kafin zai ƙare a jiki.
Amma waɗanda suka shafe shekara da shekaru suna cin goron, jiki kan jure tasirin sinadarin kafin yau da gobe.
Saboda haka tasirin sinadarin kafin a kan hauhawar jini na raguwa ne da tsawon lokacin da aka daɗe ana amfani da shi.
Sai dai kuma wani bincike ya sake yin nuni da cewa ga masu hawan jini; amfani da goro yayin da ake shan magungunan hawan jini na da tasirin rage aikin maganin, musamman jinsin maganin hawan jini da ke rufe hanyar kalsiyam(Calcium channel blockers) wanda ke taimakawa wajen buɗa hanyoyin jini.
Bayan goro, sinadarin kafin na nan a cikin kofi(coffee), lemukan roba/gwangwani da baƙin shayi, har da ma wasu magungunan ciwo kai, mura, da kasala da ake saye a kasuwa.
Mafi kyawun al’amari tsakatsakinsa, saboda haka zai fi kyau a yi amfani da goro yayin buƙata kaɗai, amma ba ya zama ɗabi’ar kullum ba.
Sannan ga masu hawan jini, saboda hauhawar jini da sinadarin kafin ke kawowa, da kuma dankwafe tasirin jinsin wancan maganin hawan jini, zai fi kyau su ƙaurace wa cin goro, da sauran abubuwan da ke ɗauke da sindarin kafin.
Wannan bayani ba zai zamo a madadin tuntuɓar likitan ka/ki ba dangane da cin goro ko kafin.
Wannan bayani Kano Focus ta kwafo ne daga shafin Physiotherapy Hausa, mallakar asibitin koyarwa na Abdullahi Wase da ke nan Kano.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
