KANUN LABARAI
Kisan kiyashin Ibadan: Buhari ya kasa jajantawa wadanda al’amarin ya shafa
Mukhtar Yahya Usman
Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya gaza jajantawa Hausawa Fulani da aka yiwa kisan kiyashu a kasuwar Shasha da ke Birnin Badin din jihar Oyo.
Kano Focus ta ruwaito cikin sakon da hadimin shugaban kasar kan yada labarai Garaba Shehu ya fitar kan rikicin, ko kadan bai ambaci inda al’amarin ya faru ba da kuma wadanda aka yiwa lafin.
Idan za a iya tunawa dai tun a ranar Alhamis ne rikici ya balle tsakin wani Bahaushe mai talla a kasuwar ta shasha, bayan da ya bangaji wata bayarabiya a rashin sani.
Hakance ya sanya ita kuma ta debo zaratan ‘yan daba domin su ramamata bangazar da ya yi mata, lamarin da ya sauya zuwa kazamin fada.

Haka zalika rikicin ya ci gaba har zuwa ranar Juma’a, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa, aka kuma kona shaguna da dama, da kuma gidajen mutane.
Rikicin ya janyo an yiwa Hausawa Fulani kisan kiyashi, tare da lalata dukiyarsu da kuma kone gidajensu.
Sai dai a sakon da shugaban kasar ya fitar ko kadan bai anbaci wadanda aka yiwa laifin ba ballantama wurin da aka aikata laifin.
Sakon na shugaban kasa ya ce.
“Gwamnatinsa zata kare dukkannin addinai da kuma kabilun kasar nan, masu rauninsu da masu karfinsu, dai-dai da yadda kundin tarin mulki ya bashi dama.
“Gwamnati ba za ta aminci ko wacce irin kabila ko wasu mabiya addini su cusa kiyayya da tashin hankali akan wasu kabilunba.
“Shugaban kasa yayi allah wadai da irin wannan rikici, ya kuma bada tabbacin gwamnatinsa za ta dauki matakin dakatar da irin wadannan fitintinun baki daya.
Wadannan dai sune kalaman da shugaban kasar ya yi kan wancan rikici da ya kaucewa jajantawa wadanda al’amrin ya shafa kamar yadda Garba Shehu ya ruwaito.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
