LABARAI
Zanga-zanga ta barke bayan da aka zargi jami’an ‘yan sanda da kisan matashi a Kano
Aminu Abdullah
Al umma da dama ne suka fito zanga zanga a unguwar kofar mata dake cikin birnin Kano dan nuna fushin su kan zargin da suke yiwa jami’an ‘yan sanda na kashe wani matashi Saifullahi Sani Musa mai shekaru 23.
Kano Focus ta ruwaito cewa matasa da dama ne suka mamaye titin Kofar mata da ke waye a da safiyar yau litinin, suna kona tayoyi tare da hana jama’a wucewa domin nuna adawar su da kisan matashin.
mahaifin matashin Sani Musa Kofar Mata ya shaidawa Kano Focus cewa da misalin karfe daya na dare jami’an yan sanda suka kai sumame unguwar suka kuma kama dan nasa lokacin da yake bacci a kafar gida.
“Yaro na kowa ya sanshi baya shan komai hasalima akwance yake a kofar gida saboda zafi.

“Bayan sun kamashi a daren naje ofishin ‘yan sanda sai akacemin ai tunda yan sanda ne na bari da safe naje,” a cewar mahaifin yaron.
Mista Musa ya kara da cewa bayan da gari ya waye yana kokarin tafiya ofishin yan sandan ne guda daga cikin yan kwamitin unguwar ya shaida masa cewar yan sanda sun kashe dan nasa.
Ya kara da cewa dan kwamitin ne ya shaida masa gawar dan nasa tana sashen bada agajin gaggawa na asibitin murtala amma zasu kaita dakin ajiyar gawawwaki
Malam Musa yace akwai raunukan duka da dama a jikin yaron da yake zargin jami’an ‘yan sanda sunyi masa.
Shima wanda ke tare da mamacin a lokacin da jami’an ‘yan sandan suka zo samamen Hamisu Muhammad yace suna bacci yayin da ‘yan sandan suka zo.
ya kara da cewa daga nan ne suka yi yinkurin tafiya dasu wanda shi kuma yasamu nasarar tsarewa.
“Baya shaye-shaye ko hayakin taba ma baya son shaka kuma basu kamashi da komai ba amma suka kasheshi wannan zalinci dayawa yake,” in ji Malam Hamisu.
Daya daga cikin yan uwan mamacin Musa Dahiru Kofar Mata cewa ya yi ‘yan sandan sun shigo cikin unguwar ne da daddare Inda suka rinka harba bindiga wanda daga bisani sukayi awan gaba da yaron da yake bacci da sauran yara.
Ya kuma ce bayan duka da suka lakadawa mamacin haka zalika sun sare shi a jiki.
Mista Dahiru yace suna bukatar hukuma ta dauki mataki akan kisan da akayiwa yaron tare da hukunta duk wanda keda hannu a cikin al’amarin.
A nasa bangaren mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun samu labarin afkuwar lamarin kuma suna cigaba da gudanar da bincike.

Hausa
Shugabannin Fulani sun goyi bayan takarar Tinubu

Aminu Abdullahi
Shugabannin Fulani wato (Ardo) daga sassa daban-daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu a wani taro da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar lahadi.
A taron da suka yi tare da hadin gwiwar Kungiyar Sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shugabannin sun yi alkawarin yin amfani da ‘yan kungiyar 33,661 wajen tattaro sauran ‘yan uwansu Fulani domin su zabi Sanata Bola Tinubu.

A lokacin da yake nasa jawabin bayan an kammala al’adar Fulani ta rabon goro ga mahalarta taron, shugaban Kungiyar Aliyu Liman Bobboi ya ce raba goron da aka yi yana nufin shugabannin za su koma gida su isar da sakon shawarar da aka yanke a wajen taron zuwa ga mabiyansu.
Ya kara da cewa taron an gudanar da shi ne domin su nuna wa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda, sun kuma yi amanna da cancantarsa, suna kuma masu adduar samun nasara a zabe mai zuwa.
Ya kara da cewa Ardo a matsayinsu na shugabanni suna da ta cewa sosai akan wanda mutanensu zasu zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu za su yi ma su biyayya.
Liman ya yi nuni da makusanta shakikai dake tareda Tinubu kamar Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Badaru na jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani yace wannan na nuni ga yadda Tinubu ya dauki kabilar ta Fulani da muhimmanci.
Kungiyar ta shuwagabannin Fulani ta kuma bawa Tinubu sarautar Barkindo.
Gwamnan jahar kano Abdullahi Umar Ganduje da yake bayani ya yi tsokaci akan irin bajinta da kwarewa da kuma cancantar Tinubu da ya shugabanci Najeriya. Ya kuma kara da cewa Fulani a matsayinsu na kabila dake fuskantar barazana a sassa daban-daban, suna bukatar zabar shugaban da zai iya basu kariya.
Ganduje ya kara da cewa suna nan kan kokarin samarwa Fulani da wani tsari wanda zai bunkasa hanyoyin kiwo a duk fadin kasar nan.
A nasa bayani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Tinubu ya yi tsokaci akan irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa a bangare daya da kuma Fulani a dayan bangaren. Ya nuna cewa alakarsa da Fulani amana ce ta dindindin.
Ya kara jaddada niyyarsa ta samarwa Fulani hanyoyin kiwo na zamani da za su kawo cigaba da kuma yalwa ba tare da tsangwama ba.
Tinubu ya kara da cewa bai taba tsammanin zai hadu da bafulatanin da ya fi shi jin yaren yarbanci ba sai gashi yau ba zato ba tsammani ya hadu dasu. Ya ce wannan abun a yaba ne.
“Wannan itace irin Najeriyarda muke bukata, kasa daya al,umma daya. Ina mai tabbatar maku idan da zamu kasance anan tsawon sa,o,I biyar iyakacindai zancenda zakucigaba da ji daga gareni kenan. Ina mai matukar mika godiya da gareku.
“Tabbas makiyayan Najeriya na fama da matsaloli dabban dabban amma ina mai tabbatar maku da cewa munada tsari na musamman da zai magance wudannan matsalolin,’ a cewar Tinubu.
A nasa jawabin Malam Nuhu Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ya cancanta, ya dace wanda kuma zai iya kawo ci gaba mai dorewa ga kabilar ta Fulani.
Ya kuma yi godiya ga goyon bayan da suka bashi tareda alkawarin ba zai ba su kunya ba.

Hausa
Samba Kurna da Good Boys Dorayi za su fafata a wasan karshe na ‘Ahlan cup’

Jamilu Uba Adamu
An kammala Shirye-Shiryen gudanar da wasan karshe na gasar cin kofin Kwallon kafa na “Ahlan Cup’ tsakanin Samba Kurna da Good Boys Dorayi.
Wanda yake jagorantar gasar Alh. Abubakar Tsoho Musa Rijiyar Zaki ne ya bayyana wa manema labarai cewar;
“Kungiyoyin Kwallon Kafa talatin da biyu ne (32) suka fafata a gasar, wacce aka gudanar a wasannin sili daya kwale (knock-out ). An Kuma buga wasa talatin ne. Inda Kungiyar Kwallon Kafa ta Samba Kurna da Good Boys Dorayi sukai nasarar zuwa wasan karshe.”
Za dai a fafata wannan wasa a ranar lahadi 7 ga watan Augusta da misalin karfe hudu na Yamma a filin Wasa na Makarantar sakandiren Unguwar Rijiyar Zaki

Kuma ana sa ran wasan zai samu hallatar manya- manyan baki, daga ciki da wajan jihar Kano a karkashin jagorancin Shugaban Hukumar wasan Kwallon Kafa ta Jahar Kano Dr. Sharu Rabiu Inuwa Ahlan.

Hausa
Kano Pillars ta doke Katsina United 1-0

Jamilu Uba Adamu
Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta samu nasarar doke Katsina United daci daya da nema (1-0 ) a fafatawar da suka yi yau Alhamis a filin wasa na Moshood Kashamu Abiola dake Babban birnin tarayya Abuja.
KANO FOCUS ta ruwaito cewa dan wasan Kano Pillars Auwalu Ali Mallam ne ya zura Kwallon a ragar Katsina United a ragowar mintunan da aka ware don karasa wasan.

Auwalu Ali Mallam
Idan za a iya tunatawa an daga wasan ne bayan da hatsaniya da ta barke ana tsakiyar wasa tsakanin kungiyoyin biyu a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a kwanakin baya.
Sai dai, a yau aka kammala wasan a filin wasa na Moshood Kashamu Abiola dake Babban birnin tarayya Abuja.

Hakan ya ba wa Kungiyar Kano Pillars damar darewa matsayi na goma sha shida acikin jerin kungiyoyi ashirin dake fafatawa a gasar ajin Kwarraru na Kasa.
