Connect with us

KANUN LABARAI

Dalilai biyar da ya sa mata suka fi son namiji mai gemu

Published

on

Zulaiha Danjuma

Mata a Kano sun bayyana dalilai biyar da ya sanya suka fi son namiji mai gemu fiye da wanda bashi da shi.

A hirar da Kano Focus ta yi da wasu ‘yan mata sunce nuna mutuntaka, kyawun fuska ra’ayi, sunna da kuma damar yin wasa da gemun na da cikin dalilan da suka sanyasu zabar maza masu gemu.

Nuna mutuntaka

Wata budurwa a nan Kano Farida Abubakar da ke sana’ar sayar da abinci ta ce duk  cikin maza ba wanda ke burgeta fiye da mai gemu.

A cewar ta namiji mai gemu komai kankatarsa yana nuna mutuntaka yana kuma kara gyara shi.

A don haka ta ce matukar ita za ta zabi mijinta to shakka babu mai gemu zata zaba.

Ita kuwa Khadija Adamu da ke Jami’ar Bayero ta ce namiji mai gemu ba wanda ya kaishi kamala da cika ido da kuma nuna mutuntaka.

A don haka ita dai zabin ta shi ne namiji mai gemu ko da kuwa mummuna ne.

Kwanciyar rai

Haka zalika matan sunce namiji mai gemu ko ba komai a kwai shiga rai.

Zainab Ka’oji daliba a kwalejin kimiyya da ke nan Kano ta ce ita dai namiji mai gemu ya fi kwanta mata a rai ba tare da l’akari da kalar sa ba.

Ta ce namiji mai gemu yana matukar burgeta musasamn mai mai saje musamman ma idan yana kula da shi.

Ita kuwa Nusaiba Magaji da ke Unguwar Tarauni a nan Kano ta ce baa bin da za a yi da namiji mara gemu ko saje.

Ta ce namiji mai gemu ya fi shiga rai ya kuma fi sanya mace farinciki da zarar ta kalleshi.

A cewar ta mazan da basu da gemu basu da ko dadin kallo.

Ta kara da cewa namijin da bashi da gemo komawa yake kamar mace baya bada sha’awa ko kadan.

Kyawun Fusaka

Haka zalika wasu ba’arin yan matan sunce abin da yasa suka fi zabar namiji mai gemu shi ne sun fi wadanda basu da shi kyau.

Fatima Ibrahim da ke unguwar farm Center a nan Kano ta ce maza masu gemu suna da tsananin kyau fiye da shagirai.

Ita kuwa Farida Abubakar da ke unguwar Hauwasa a nan Kano ta ce ana ganin namiji mai gemuma a zahirin sa kaga kyayyakwa.

A don haka ta ce ita dai ta zabi mai gemu domin ko da yana da muni to gemun na boye munin sa.

Zaka iya wasa dashi

Ba’arin wasu yan matan kuwa cewa suke sun zabi namiji mai gemu ko dan su yi wasa da gemun.

Khadija Adamu dake Unguwar Kabuga ta ce babban abin da ya sanya ta zabi namiji mai gemu shi ne ko dan ta yi wasa da gemu iya son ranta.

A cewar ta idan mace tana da miji mai gemu to ko ya bata mata rai da ta fara wasa da gemunsa sai zuciyar ta ta sakko.

Sunnah

Haka kuma wasu ‘yan matan sun ce sun zabi mai gemu ne domin shi gemu sunna ne.

A cewar Ramatu Shehu ta zabi namiji mai gemu ne saboda cewar mafiya yawan masu ajiye gemu suna dabbaka sunnan ne.

Ko me mazan ke cewa game da ra’ayi matan?

Wasu daga cikin samari a nan Kano da Kano Focus ta zanta da su sun bayyana yadda suka tsinci kan su a hannun yan matan.

Mustapha Fagam dalibi ne a jami’ar Bayero da ke nan Kano ya ce ya ga mata ba adadi da zuciyar su ke kaunar namji mai gemu.

Ya ce mata sun sha gaya masa ra’yin su na son namiji mai gemu ko da kuwa mummuna ne.

Ya ce mata da dama ne suka guje shi sabo da bashi da gemu.

Shi kuwa Mustapha Rabi’u da ke sana’ar sayar da katin waya a unguwar Tudun Yola ya ce ya rabu da mata kusan biyar sabo da shi shagiri ne.

Mata nason gemu

A cewar Bashir Tahir Sulaiman mata da yawa na manne musu saboda gemun da suke dashi.

A cewar sa yadda mata ke masa saboda gemunsa na sa shi ya dan ji girman kai.

Ya ce hakan ta sanya ya tanaji mai da sauran kayan gyara domin ya ci gaba da burge matan

Shima Abdussalam Danjuma da ke zaune a unguwar zoo road ya ce mata na rububin sa saboda kyawun gemunsa.

Ya ce mata basa dauke ido da ga gemusa musamman ma idan ya sanya dogayen kaya da kuma hula.

Ya ce hakan ta sanya shi ya ke sanya mai domin gyaran gemun nasa yadda matan za su so shi sosai.

Said dai duk da wannan batu akwai matan da su kuma gemun bai damesu ba.

Maza masu gemu kazamai ne

Wata budurwa mai suna Khadija Nuhu Umar da ke unguwar hotoro

ta ce ko kadan namiji mai gemu baya burgeta domin maza masu tara gemu kazamai ne.

Ta ce mafiya yawan mata masu gemu haka suke barin sa butsa-tsa  ba kyan gani  da hakan ke sanya ta shirin yin amai idan taga mai shi.

Wata malamar jinya Asibitin koyar na Aminu Kano Hafsa Inuwa ta ce maza masu gome basa burgenta ko kadan.

A cewar ta masu tara gemu kazamai ne basa iya tsafta ce gemun nasu.

Ko da ya ke ana samun wasu suna wankewa amma duk da haka baya burgeta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending