Connect with us

KANUN LABARAI

Matasa a Kano na shiga hadari sakamakon siyan wayar hannu

Published

on

Aminu Abdullahi

Matasa da dama ne a kano ke fadawa hadari sakamokon siyan wayar hannu (second hand)  sakamkon rashin tartibin yadda aka samota.

Binciken da Kano Focus ta gudanar ya nuna  cewa dayawa da ga cikin matasa da basa tantance wayar da suke saya, suna sayan wadanda aka yi kwacen su ne ko kuma aka fasa shago aka dauke.

Idan ba a manta ba dai a yan kwanakin nan ana ta samun rahoton yadda kwacen waya yayi Kamari a jihar nan da ta kan kai ga raunta mutum wani sa’in ma ta kai ga ajali kafin a dauke masa wayar.

Haka zalika da yawa da ga cikin masu sayan wayar basu damu da a basu rasiti ko wata shaida da za ta iya kade su daga fitina ba.

Shiga mawuyacin hali

wananan al’amari na kai jama’a da dama cikin mawuyacin hali.

Malam Lawan Abdullahi mai shekaru 25 mazaunin unguwar Dakata na daya daga cikin wadanda suka taba fadawa hannun jami’an tsaro sakamakon siyan wayar sata.

Ya ce ya sayi wayar kirar Nokia akan naira dubu uku amma a karshe saidai aka kashe naira dubu dari uku kafin ya samu ya kubuta daga hanuna jami’an tsaro.

Malam Abdullahi ya ce sai da aka daure shi kwana hudu a ofishin  ‘yan sanda dake Gwagwarwa daga nan aka wuce dashi sashen binciken masu aikata laifi dake jihar Delta.

Saidai yace har zuwa lokacin da aka bada belin sa ba a nuna musa mutumin da ya ke shari’a dashi ba.

Itama wata mata mai suna  Jamila Umar dake zaune a unguwar Rijiyar Zaki a karamar hukumar Ungoggo, tace saurayin ta ne ya siyamata waya wacce wani ya tabayin amfani da ita da ta jefa ta cikin hadari.

“Ina zaune a gida sai naji an kirani ance daga state CID tare da bani umarni nakai kaina ofishin ‘yan sanda dake rijiyar Zaki.

“Na fadawa iyaye na abinda ya faru ance  naje ofishin ‘yan sandan amma sai naki zuwa.

“Ina zaune kawai sai gani nayi jami’an ‘yan sanda sun shigo gidan mu suka wuce dani ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki,” a cewar ta.

Ta kara da cewa daga nanne ta fahimci kuskuren da tayi na kin kai kanta ofishin ‘yan sandan.

“An kirawo saurayin nawa cikin ikon Allah kuma aka kama wanda ya siyar masa da wayar a karshe dai saida aka bada bellin mu sanan ba a dawo mana da kudin wayar ba.

“Kuma  saurayin nawa saida ya kwana biyar a hannun ‘yan sanda ana bincike,” inji malama Jamila.

Masu sayar da waya na sayan ta sata

A nasa bangaren shugaban kasuwar saida wayoyi ta Beirut Malam Ibrahim Rabi’u Tahir, ya ce masu sayar da wayaoyi da dama na fadawa hadarin sayan kayan sata.

a don hakan ne ma yaja hankalin jama’a da masu siyar da waya da su guji siyan wayoyin da basu da shaida ko kwali.

Ya kara da cewa duk kan wanda zai sai waya ya tabbatar yasan gurin wanda ya siya don gujewa samun matsala.

Malam Tahir ya kara da cewa da yawan masu siyar da waya na karewa a magarkama sakamakon siyan wayar sata.

Ya kuma ce wasu wayoyin na sata ne, ko kwace ko kuma wanda wasu sukayi fashi sanan a shigo dasu kasuwa da idan mutum bai kiyaye ba sai ya fada ruwa.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending