KANUN LABARAI
Zanga-zanga: yadda aka kashe yarana hudu a Kano.
Mukhtar Yahya Usman
Hajiya Hadiza Shareef da ke unguwar rijiyar lemo a nan Kano ta ce yaranta hudu da ke yi mata aikatau aka kashe ya yin zanga-zangar @EndSARS a Kano.
A wata hira ta musamman da jaridar Kano Focus a ranar juma’a ta ce yaran nata na kular mata da gidan ‘Wanka da Bahaya’ da ke Middle Road a unuwar Sabon Gari.
Ta bayyana matasan da aka kashe da Abdurrahman Sobo wanda ya fito daga garin Minjibir kuma yake aikatau a hannunta tsahon shekaru biyu.
Sai Kuma Jamilu Muhammad da ke unguwar Zoo rood a nan birinin Kano da shi ma ya shafe sama da shekara yana yi mata aikatau,
Sai kuma na uku Aliyu Shehu da ake yiwa lakabi da Gatari mutumin sheka makaranta a nan birnin Kano.
Cikon na hudun shi ne Badamasi Ibrahim da ya zo ci rani daga Katsina, yake kuma zaune a unguwar Jaba.
Hajiya Hadiza ta ce mutum uku daga cikin wadannan an samu gawar su biyu ma har an yi musu jana’iza ya yin da daya har yanzu yake mutuware a asibitin Murtala.
Sai dai ta ce cikon na hudu wato Abdurraman Sobo an koneshi kurmus ne ba su iya tantance gawar sa ba kamar na ragowar.
Yadda al’marin ya faru
A cewar Hajiya Hadiza an mamayi yaran nata ne cikin dare a ranar Talata da ta gabata inda wasu matasa dauke da makamai da galibinsu inyamuraine suka kewaye gidan da yaran nata ke yi mata aikatau da nifin Hallaka su.
“A ranar Talatar da ta gabata ‘Da’ na Arabi ya kirani a waya ya ce naje na debo yarana wato kannensa daga makaranta ana tashin hankali.
“Ba shiri na tafi na debo su, da yake suna karatu ne a makarantar Tony Chetta.
“Sai na ce mishi suma su rufe wurin nasu da suke sana’ar su taho gida, sai ya ce ba komai an kwantar da tarzomar.
Da magariba na sake kiransu na ce ku fito daga wurin nan kungani ya zama kamar fadan kabilanci da Inyamuran kunce suna ta dukan Hausawa, sai ya ce min ba komai, wuta ta lafa.” A cewar ta.
Cikin dare aka kai musu hari
Hajiya Hadiza ta kara da cewa bayan wannan tattaunawa da yaron nata ne kuma ta kara samun waya marar dadi cikin dare.
“Karfe 3:00 na dare sai Arabi ya sake kirana ya ce gabadaya Inyamuran nan sun sake yi musu kawanya.
“da yake yaran namu a ciki suke kwana kuma wannan gidan shi kadai na Hausawa a yankin, don haka suka mayar da hankali a kansa.
“Bayan da aka yi hatsaniyar da rana kura ta lafa shi ne fa suka sake komawa cikin dare suka yi musu kawanya suka kashe na kashewa suka kona na Konawa”. A cewar ta.
Da kyar muka sha da ranmu
Arabi Sahrif Hadi da ke zaman Da ga hajiya Hadiza da kuma ke kula da gidan wankan ya shaidawa Kano Focus yadda suka tsira da ransu kuma sauran abokan sana’ar sa suka salwanta.
Ya ce bayan kura ta lafa a zanga-zngar ranar Talata bayan magriba sai wasu gungun matasa da makamai suka taso musu kamar za su hallakasu.
“Sun yo kan mu da makamai muka ce musu mu ina ruwan mu ba fada muke da sub a, muka dai samu muka gudu muka shiga muka kulle.
“Sunyi ta kokarin balla gidan amma Allah bai basu sa a ba sai suka hakura suka koma.
“munan zaune cikin razani da firgici domin kowa ya kasa tafiya gida a nan muka kwana, da misalin karfe uku saura muka fara jiyo ihu da hayaniya sai wuta ke tashi ta ko ina.
“”suka zo suna dukan gidan suna mu bude idan ba haka ba za su hauro sai sun kashe kowa, suka bankara Kofar cikin ikon Allah basu samu sun karya ba.
“to bayan munji kamar sunja bayan ne wasu daga cikin mu sai suka fita suka ruga don menan ceton ransu ni kuma na tsallaka wani Hotel da ke kusa da mua na fake.
“shi Badamsi ya na fita suka bigeshi sai gawar sa muka gani da safe a cikin kwata, shi kuma Abdurrahman Sobo ga shinan kusa da Badamasi an saka masata taya an kone shi kurmus ko da dai bamu ganeshi ba amma dai ina kyautata zaton shi ne.
“Sauran yara kuma akwai sabbin gine-gine da aka yi da ba a kammala ba sai suka bude sokaway din suka shiga suka buya, wasu kuma suka buya cikin ciyayi, wannan shi ne abin da ya faru cikin dare.”
Arabi ya shaidawa Kano Focus cewar duk da wannan al’amari da ya faru cikin dare washe gari suka sake dawowa suka nemi balla gidan domin su cimmusu.
“bayan sun dawo washe gari ne suka kuma koramu muka shiga muka kulle yara suka ruga aguje neman mafita.
“Muna gani akan idon mu aka dauki Jamilu aka dannashi a cikin duron da suka kunnawa wuta ya kuma kone kurmus akan idon mu.
“Akwai wani Abuakar shima muna gani suka dannashi a cikin doron ya kone kurmus. A cewar sa.
Ya kuma ce kafatanin wadanda suka mutu an aike da gawarwakin su dakin adana gawarwaki na asibitin Murtala da ke nan Kano.
Haka zalika tuni wasu da ga cikin su ‘yan uwansu suka fara karbar gawawwakin su domin yi musu suttura.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.