KANUN LABARAI
‘Yan bindiga sun sace matar dagacin Tsara a karamar hukumar Rogo
Nasiru Yusuf
Masarautar Karaye ta sanar da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga gano ko suwaye ba sun sa ce Aishatu Aliyu matar dagacin Tsara dake karamar hukumar Rogo a nan Jihar Kano.
Kano Focus ta ruwaito ‘yan bindigar sun mamayi gidan dagacinne mai suna Aliyu Muhammad da misalin karfe daya na daren ranar J’uma’ar da ta gabata suka kuma yi awon gaba da matar tasa
Jami’in hulda da jama’a na masarautar Karaye Haruna Gunduwawa ya shaidawa Kano Focus a ranar Talata cewar ‘yan bidigar sun yi ta harbi a iska kafin su dauke matar a gaban mijin nata.
A cewarsa mazauna kauyen sun kirga harsashi goma sha bakwai da yan bindigar suka harba da aka tsinci fankonsu kashegari.
Ya kara da cewa mafi yawa daga jama’ar garin dazuka suka gudu suka kwana domin neman ceton rai.
Gunduwawa ya ce har kawo yau Talata masarautar Karaye bata gano manufar ‘yan bindigar ba, sabo da har yanzu basu waigo kan neman kudin fansa ko su bada wani bayani ba.
Idan za a iya tunawa dai cikin abin da bai gaza watanni biyu ba an samu rahoton sace jama’a har sau hudu a karamar hukumar ta Rogo.
Gunduwawa ya ce mai martaba sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II ya roki jami’an tsaro da su samar da matakan tsaron da za su kawo karshen matsalar amasarsutar sa.
Sai dai da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Kano kan al’amarin ta ce bata da masaniya.
Mai Magana da yawunta mataimakin sufurtandan ‘yan sanda Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ko kadan basu samu rahoton cewar an sace wani ko wata a karamar hukumar Rogo ba.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.