Connect with us

KANUN LABARAI

Gwamnatin Kano za ta mayar da ma’aikatan wasu hukumomin ta  zuwa makarantu

Published

on

 

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Kano ta ce za ta zakulo masu shaidar karatu na koyarwa da ke aiki a ma’aikatu daban-daban a jihar nan domin mayar da su aikin koyarwa.

Kano Focus ta ruwaito sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da hakan a ranar Talata ya yin da ya ke kaddamar da kwamitin da zai lalalubu matsalolin da ke hana shirin Ilimi kyauta kuma dole na gwamnantin Kano ya ci gaba.

Usman Alhaji ya ce bai dace mutum na da shaidar karatu na koyarwa ba kuma ya tafi yana aiki a wasu bangarorin da basu shafi Ilimi ba.

A cewarsa a don hakan ne ma aka dorawa kwamitin alhakin zakulu irin wadannan mutane a kuma mayar da su makarantu domin su ciyar da harkar Ilimi gaba.

Ya ce wadannan mutane za su koyar ne a dukkanin bangarorin makarantu da ake da su da suka hadar da firamare da sakandire har ma da manyan makarantun gaba da sakandire.

Haka kuma kwamitin zai yi aikin nazartar dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin gano wadanda ayyukan su suka yi  iri daya domin hadesu wuri guda.

Ya ce bayan hadesun ragowar ma’aikatan za a mayar da su bangaren koyarwa domin su tallafawa jihar su.

Kwamitin mai mambobi 19 na da tsohon babban sakatare a ma’aikatar ilim ta Jiha Alhaji Danlami Garba a matsayin shugaban.

Sai kuma Abdullahi Balarabe daraktan gudanarwa a ofishin sakataren gwamnati, da kuma Abba A Dungurawa da ga ofishin shugaban ma’aikata na jihar Kano a matsayin sakatare na biyu.

Haka zalika Usman Alhaji ya kaddamar da wani kwamitin da zai duba yadda za a farfado da tattalin arzikin Kano bayan wucewar COVID-19

Ya ce gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi hangen irin halin da za a shiga  na rayuwa bayan Corona musamman ma matsin tattalin arziki da hakan ya sa ya farga tun da wuri.

Kwamitin da Sakataren gwamnati Usman Alhaji ke shugabanta ya hadar da mambobi da ga dukkanin bagarorin da suka shafi tattalin arziki a jihar nan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending