Connect with us

KANUN LABARAI

Yanzu-yanzu: Ganduje ya umarci Salihu Tanko Yakasai ya dawo bakin aiki

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya umarci mai bashi shawara kan Kafafan yada labarai na internet Salihu Tanko Yakasai ya dawo bakin aiki.

Kano Focus ta ruwaito gwamnan ya bada umarninne a ranar Laraba bayan ya kwashe makwanni biyu a dakace.

Idan ba a manta ba dai gwamna Ganduje ya dakatar da shi ne makwanni biyu da suka gabatar bayan da yayi wani rubutu akan shugaban kasa Muhmmadu Buhari da bai yiwa gwamnan dadi ba.

Ya kasai a rubutun da yayi a shafinsa na twitter ya nuna shugaba Buhari a matsayin mara tausayin talaka.

Hakan ce ta sanya gwamnan ya fusata ya Kuma dakatar da shi daga bakin aiki.

Sai dai a yau Laraba gwamnan ya bada umarnin ya dawo bakin aiki.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending