KANUN LABARAI
Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama barayin zanga-zanga 59
Mukhtar Yahya Usman
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 59 da ake zargin suna da hannun kan tashin hankalin da ya faru a Kano yayin zanga-zangar #EndSARS.
Kano Focus ta ruwaito kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan ya yin taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba a shelkwatar rundunar da ke nan Kano.
Abdullahi Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce cikin mutane 59 da aka kama 31 ankamasu dumu-dumu da kayan jama’a da suka wawushe.
ya ce ko da ya ke an samu nasarar kwantar da tarzomar amma dai ‘yan tada kayar bayan sun kone babura 7, adai-daita sahu daya sai kuma motoci biyu.
Haka kuma sun sace babura 8 suka kuma fasa shaguna 38 ciki har da babban shagon sayar da kayayyaki na Galaxy ta ke kan titin zuwa fili jirgin sama.
Wadanda ake zargin har ila yau sun sace kayayyaki a shagon sayar da abinci na Chicken Republic.
Haka kuma ya ce ragowar 28 din da aka kama dukkaninsu na da hannu kan tashin hankula da suka faru yayin zanga-zangar ta #EndSARS.
Ganima muka samu
Sai dai wasu daga cikin wadansa aka kama sunce su fa ba sata suka je yi ba gani ma ce suka dauka.
Yakubu Muhamamd Tudun Wada ya ce shi ko kadan bai saci kayan kowa ba illa iya ka ganimar yaki ce ya gani ya kuma kwasa.
“Na dawo daga wurin aiki ne sai na tarar ana yaki tsakanin musulmi da arna kuma naga ganima sai na kwasa.
“Donhaka ni ba barawo ba ne ban kuma saci kayan kowaba kuma ai ganima halak ce”. ya ce.
Shima Auwalu Musa da ke unguwar kwana hudu ya ce ko da ya ke an kamasu amma ba a kyauta ma sa ba domin shi kayan da ya dauka nag anima ne.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.