KANUN LABARAI
Rashin filayen wasanni na kara sanya yara da matasa zama dakikai a Kano
Aminu Abdullahi
Wani masanin halayyar dan adam dake jami’ar Bayero a nan Kano Aminu Sabo Dambazau ya ce rashin filayen wasanni ga matasa na kara musu kuncin rayuwa da hakan ke haddasa musu rauni fahinta a karatunsu.
Malam Dambaza ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da jiaridar Kano Focus a ranar Larabar da ta gabata.
Danbzau ya ce wata illar ta rashin samun damar yin wasanni na sanya matasa aikata mugayen dabi’u a cikin al’umma.
Ya kara da cewa wasanni na karawa dan adam karsashi da walwala da hakan ke dabe musa damuwa.
Dambazau ya yi kira ga gwamnati da ta daina gine filayen wasanni da ake dasu a cikin unguwanni duba da irin muhimmancin da suke dashi.
A nasa bangaren wani malami a sashen motsa jiki na kwalejin ilimi ta tarayya dake Kano F.C.E dakta Isyaku Labaran Fagge yace motsa jiki kantemaka wajen bungakasa lafiyar kwakwal.
Yace abin takaici ne yadda gwamnatoci ke gine filayen wasanni dake cikin unguwanni wanda kuma hakan ke baraza ga cigaban bangaren.
Ya ce yawan aikata laifuka da karuwar matsalar shaye shaye da ake samu a jihar Kano nada alaka da matsalar karancin filayen wasanni a unguwanni.
Fagge ya kuma shawarci gwamnati data bunkasa ragowar filayen da ake dasu ta hanyar gyarawa tare da samar da yanayin da ya dace don ciyar da harkokin kwallon kafa gaba a fadin jihar Kano.
Saidai kuma a wani bincike da jaridar Kano Focus ta gudanar ta gano yadda matasa a wasu unguwannin kan maida gefen titinan unguwannin su guraren buga kwallon kafa .
Yayin da wasu kuma kan zabi yin wasan kwallon kafar a tsakiyar layunka unguwannin su.
Wasu kuma matasan kan bar ma unguwannin nasu zuwa wasu unguwannin don samun gurin da za su yi wasanni musamman ma na kwallon kafa.
Najibu Ibrahim mai shekaru ashirin da biyu mazaunin unguwar Tukuntawa yace a shekarun baya basa shan wahala duk lokacin da zasu buga kwallon kafa.
Saidai yace sakamakon gine filayen wasannin unguwar da akayi hakan ta sa dole sai sunyi tafiya mai nisa kafin su samu filin da za su yi wasan kwallon kafa.
Shima wani matashi mai suna Tukur Muhammad yace sakamakon rashin filin wasa a unguwar su hakan tasa yasakale takalman sa.
Yace dole ce tashi ya dena buga kwallo saboda sai ya yi tafiya mai nisa kafin samun filin da zai buga kwallon kafa.
“Daga Gauron Dutse zuwa Kofar Na’isa sai na kashe kudi sosai sabo da nisa hakan tasa gaskiya bazan iya zuwa ba.
“Yakamata gwamnati ta rinka samar da filayen wasanni a unguwanni ta kuma daina gine wadanda ake dasu gaba daya,” inji shi.
Mubarak Muhammad wanda akafi sani da Messi mai shekaru 26 yace kafin gine filin wasan unguwar su dake Sheka yana samu ya motsa jikin sa a kowace rana.
Ya kara da cewa ada koda ba zai buga kwallo ba to yakanje filin kwallo dake kusa dasu don samun nishadi.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.