KANUN LABARAI
A dawo da mu bakin aiki-Dakatattun ma’ikatan hukumar tara kudaden haraji
Aminu Abdullahi
Ma’aikatan wucin gadi na hukumar tattara haraji ta jihar Kano da aka dakatar watanni bakwai da suka gabata sun roki gwamnati ta mayar da su bakin aiki.
A wata hira da jaridar Kano Focus a ranar Juma’a ma’aikatan sunce sun shafe a kalla watanni bakwai ba tare da an biyasu albashi ba.
Idan za a iya tunawa dai tun a watan Maris din da ya gabata hukumar tara kudaden haraji ta jihar Kano ta dakatar da ma’aikatan ta na wucin gadi sakamakon bullar cutar KORONA.
Hukumar ta ce ta dakatar da ma’aikatan saboda matsalar tattalin arziki da ta shiga sakamakon bullar cutar.
Haka kuma ta yi alkawarin mayar da su dazarar al’amura sun dai-daita.
Sai dai a cewar dakatattun ma’akatan sun shiga wani hali na damuwa sakamakon dakatar da su din, a cewar su da aikin suka dogara.
Kabiru Muhammad ya ce wadanda aka dakatar din za su kai dari uku.
Ya ce rayuwa ta yi musu tsanani, bayan da aka dakatar da su kan ayyukan nasu da zumammar nan gaba za a dawo da su.
Ya ce sun aika takarda dmin yin tuni ga shugaban hukumar sai dai har yanzu ba a ce musu komai ba.
Mukhtar Umar cewa ya yi a takardar da aka basu an rubuta musu dakatarwa ne na wani lokaci ba sallama ba.
Ya ce jawabin da akayi musu shi ne za su zauna a gida na dan wani lokaci har al’amuran Korona su lafa.
To ko me gwamnati ke yi kan koken ma’akatan.
shugaban sashen kudi da mulki na hukumar tara haraji ta jihar Kano Nasiru Abba Aliyu, ya ce babu tabbas ko za su iya komawa bakin aiki.
Ya ce tuni aka kafa kwamitin dake duba yadda ma’aikatan za su dawo bakin aiki.
Ya kara da cewa matsalar tattalin arziki da aka shiga a duniya sakamakon cutar korona ta sanya aka dakatar da ma’aikatan.
Ya kuma yi kira gare su da su kara hakuri tare da ‘yin addu’a don ganin komai ya daidai ta.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.