KANUN LABARAI
Sha’aban Sharada ya nemi a rushe ‘yan sandan ‘Anti-daba’ a Kano
Mukhtar Yahya Usman
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai Sha’aban Ibrahim Sharada ya ne me rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ta rushe sashin da ke yaki da ‘yan daba da ake kira ’Aniti-daba’.
Kano Focus ta ruwaito dan majalisar ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi bayan da ya ziyarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Habu Sani kan kisan da aka yiwa wasu matasa biyu a unguwar Sharada.
Idan za a iya tunawa a shekaran jiya Asabar ne ‘yan sandan Anti-daba suka kashe wasu matasa biyu, ‘yan ba ruwana a unugwar Sharada bayan da sukaje kamen masu laifi.
Matasan da suka hallaka a hannun ‘yan Anti-dabar sune Abubakar Isah da kuma Ibrahim Sulaiman da aka yi ittifakin abokanaine.

Wannance ta sanya al’ummar yankin na Sharada harzuka da kuma fara kiraye-kirayen a soke sashin na Anti-daba.
A cewarsu ko kadan ‘yan sandan na Anti-daba na wuce gona da iri a cikin ayyukan su.
Haka ta sanya Saha’aban Sharada kai koken sa ga kwamishi nan ‘yan sadan na jihar Kano kan daukar matakin gaggawa kan barnar da ‘yan sanda suka yi musamman ma na kashe yan baruwa na.
Cikin bukatar da dan majalisar ya gabatarwa kwamishina shi ne a hukunta wadanda suka yi barnar sannan a gyara musu ayyukan su ko kuma a rushesu ma baki daya.
Yadda al’amarin ya faru.
A cewar mazauna yankin na Sharada, da misalign karfe 11.00 na daren ranar Asabar ne ‘yan sadan na Anti daba suka mamayi yankin dab da masallacin juma’a na Sharada domin kama masu laifi.
Shaidun gani da ido sun ce ‘yan sandan sun mamayi wurin mai sayar da shayi ne da ke kira da ‘Indomie spot’ da suke zargin akwai musu lafi a wurin.
Rikici ya barke ne a dai-dai lokacin da mai wurin Ibrahim Sulaiman ya bukaci sanin dalilin da ‘yan sadan za su kama dan uwansa mai suna Gaddafi duk da cewa ba mai laifi bane.
‘Yan sanda sun kashe matasa biyu a Kano
Budurwa ta kashe kanta a Kano ta hanyar rataya
Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da matashi da ya shafe awa 7 a cikin kwata
Sai dai wani dan sanda da ake kira Ado da ya yi yunkurin dakatar da Ibrahim ya yi amfani da wuka inda ya yankeshi har sau biyu.
Hakan ta sanya wani matashi Abubakar Isah da ke wurin ya taso domin kawowa Ibrahim dauki, nan ma wani dan sandan ya sa bindiga ya harbeshi da kuma ya mutu nan take.
A cewar wadanda suka shaida lamarin nan take aka garzaya da su asibiti basa kokarin ceto rayuwar Ibrahim sai dai da misalin karfe 2.00 na dare shi ma ya mutu.
An kama ‘yan sandan
Tuni dai kwamishinan yan sandan jihar Kano Habu A Sani ya bada Umarnin Kama ‘yan sandan da suka yi wannan aika aika.
A cewar Jami’in hulda da jama’a na runduar yan sandan Abdullahi Haruna Kiyawa, Kwamishinan ‘yan sandan ya bada umarnin kama jami’an ne jima kadan bayan da ya samu labarin faruwar al’amarin.
Abdullahi Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce ko kadan ba za a bar wannan al’amari ya wuce haka siddan ba.
A cewar sa za a gudanar da bincike za kuma a baiwa mai hakki hakkin sa da zarar an kammala binciken.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
