Connect with us

KANUN LABARAI

Budurwa ta yi fashin yaro dan shekara biyu a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wata budurwa mai shekaru 18 Khadija Muhammad ta sace wani yaro dan shekara biyu  mai suna  Sayyadi Nasiru a unguwar Rijiyar Lemo.

Yayin tattaunawar jaridar Kano Focus da mahaifiyar yaron mai suna Zainab Nura Ahmad ta ce budurwar ta yaudareta ne har gida ta kuma yi awon gaba da dan nata.

A cewar ta matar takan shigo gidanta a koda yaushe, inda ta ce mata ita ‘yar makotace da hakan yasa har suka kulla abota.

Zainab ta ce barauniyar ta ziyarce ta a ranar Juma’ar da ta gabata ta kuma nema ta aramata al’kur’ani, saboda an korota daga makaranta.

Sai dai bayan ta bata aron al’kur’anin ne kuma ta nemi da ta bada aron yaron ya rakata makaranta.

A cewarta da farko ta hana ta saboda yaron yayayyene, amma sai barauniyar da ake zargi tace mata kada ta damu akwai ‘ya’yan malamansu a makarantar wanda idan yagansu suna wasa ba zai fita ba.

“Ta ce min ana sayar da awara a gidansu, kuma a bayan layinmu akwai inda ake sayarda a wara.

“Yan gidanma suna shigowa su dauke shi, hakan tasa na yarda da ita.

“Bayan da na bata yaronne sai naga har lokacin tashi daga islamiyyu yayi basu dawo ba.

“Haka tasa na tura gidan su don a fada mata cewa magariba tayi ta dawo da shi sai suka ce ai kwata kwata ma ba a gidan take ba basu ma santa ba,” a cewar Zainab.

A nasa bangaren mahaifin yaron mai suna Nasir Usman ya ce ya yi tafiya ne zuwa Zamfara lokacin da al’amarin ya faru.

Ya ce bayan ya idar da sallar magriba ne sai aka Kira shi ake fada masa wata yarinya ta dauke Saiyid ba a ganshi ba.

Malam Nasir ya ce hakan tasa dole ya baro jihar yadawo Kano.

Ya kara da cewa tun daga ranar Juma’a da ta gudu da yaron, har ya zuwa yanzu ba a ji duriyar inda suke ba.

Ya kuma bukaci al’umma da su taya su da addu’a don ganin an gano inda yaron yake.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending