KANUN LABARAI
‘Yan sanda a Kano sun kama dan sahun da ya gudu da kayan fasinja
Mukhtar Yahya Usman
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani dan Adai-daita sahu mai suna Sadik Hussaini da ya gudu da kayyan da fasinja ya dora masa.
Kano Focus ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar yan saan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan ga manema Labarai a ranar Litinin.
Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan yan sanda ya ce an basu labarin ana shiga da kaya wani gida a unuguwar Zawaciki da mazauna yankin basu yarda da sub a.
Kayan da ake zargin dan Sahun ya gudu da su sun hadar da fulawa buhu takwas, da sauran kayan cefanen shagon sayar da kayan yau da kullun da suka hadarda omo madara da sauransu.

kiyawa ya ce suna samun labarinne rundunar yan sanda ta aike da jami’anta domin bincika zargin.
A cewarsa bayan dogon bincikene kuma aka gano kayan a cikin gidan da kuma aka tabbatar na satane.
Kiyawa ya ce tuni suka damke dan adai-daita sahun da ake zargi da kuma dukkanin wadan da ke da hannun a aikata barnar.
Da yake bayani kan yadda kayan nasa suka salwanta, mamallakin kayan Abubakar Abdullahi Alasan, mai shekaru 24 ya ce ya doro masa kayan ne daga kasuwar singa zuwa Unguwar Kakankare da ke karamar hukumar Ungogo.
Sai dai ya ce da suka taho hanya yana tsaya, ya kuma tabayeshi dalilinsa na tsayawa, sai kawai yayi masa dariya.
Abubakar ya ce bayan da suka zo Kofar Kabuga ne kuma sai ya nemeshi sama da kasa ya rasa.
“ Na doro masa kayanne tun daga kasuwar Singa zai kaimin Kankare nan kusa da Jami’ar Bayero.
“Sai dai muna tafiya ne sai naga yana tsayawa, idan nai masa Magana, sai kawai yayi dariya.
“Muna zuwa Kabuga na nemeshi na rasa, har na koma shagona na tambaya ko ankawo kaya, aka ce ba a kawoba, na koma har Singer ko ya dawo nan ma aka ce bai dawi ba.
“ Hakan ta sanya na barwa Allah na yi ta addu’a, da safe kawai sai ‘yan sanda suka kirani suka ce an kama wanda ya gudu da kayana.
Shi ma wanda ake zargi da karkatar da kayan Sadiq Hussani ya ce ya gudu da kayan ne bayan da ya lura mai shi bayan ganin sa.
Ya ce ya kai gidan yayarsa ne a Zawaciki ya boye kayan, da a nan ne kuma yan sanda suka yi bincike suka kamoshi.
Tuni dai rundunar yan sandan ta ce ta kammala bincike za kuma ta gurfanar da shi a gaban kotun domin ya girbi abin daya shuka.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
