KANUN LABARAI
Ba za a bude bodar Najeriya ba-Nanono
Mukhtar Yahya Usman
Ministan Aikin Gona na Kasa Muhammad Sabo Nanono ya ce babu ranar da za a buɗe iyakokin kasar nan.
Kano Focus ta ruwaito Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron bikin rabon kayan aikin gona ga manoman da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihar Kebbi.
Nanono ya ƙara da cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta shirya buɗe iyakokin ƙasar nan ba, domin har yanzu tana nan akan bakarta na ganin harkar noma a ƙasar nan ta bunƙasa.
“Manoma a ƙasar nan sun yi matuƙar ƙoƙari wajen noma kayayyakin abinci da su ka haɗa da Shinkafa da Gero da Dawa da kuma Riɗi. “Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta shirya buɗe iyakokin ƙasar nan ba, hakan ne ya sanya gwamnatin ta shirya domin baiwa manoman da su ka haɗu da ibtila’in ambaliyar ruwa tallafi domin haɓaka noman rani.
“Domin hakan zai sanya su samu abin da su ka yi asara a lokacin damuna” In ji Sabo Nanono.
Da gaske ne an ce za a bude boda?
A makon jiya ne dai Ministar Kuɗi ta ƙasa Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce za a iya buɗe kan iyakokin ƙasar nan ba da jimawa ba.
Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin tarayya.
Ta ce kwamitin fadar shugaban ƙasa da aka kafa kan lamarin ya kammala aikinsa kuma ya bayar da shawarar a buɗe.
Ta ƙara da cewa nan ba da ɗaɗewa ba kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, daga nan kuma za a gabatar da sanarwa a hukumance kan lamarin.
Yaushe Aka Rufe?
Tun dai a cikin watan Agustan shekarar 2019 ne gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin ƙasar nan da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Matakin rufe iyakokin ya ja hankalin mutane da dama a kasar nan tare da jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke goyon baya wasu kuma ba sa goyon baya.
A cikin watan Maris din shekarar da mu ke ciki fadar shugaban ƙasa ta ce ‘yan kasar nan sun ga irin amfanin da rufe iyakokin ya yi a fannin tattalin arzikinta.
Malam Garba Shehu, kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya bayyana hakan, ya jaddada cewa ba za a bude iyakokin kasar ba sai gwamnati ta samu tabbaci daga wurin makwabtanta cewa ba za a su rika yin abubuwan da suka saba wa doka ba a kan iyakokin.
Labarai24
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.