Connect with us

KANUN LABARAI

Za a bude iyakokin kasar nan ba da jimawa- Muhammadu Buhari

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce nan ba da jimawa ba za a bude iyakokin kasar nan da aka gargame sama da shekara guda.

Kano Focus ta ruwaito shugaban kasar na wadannan kalamai ne yayin ganawar sa da gwamnonin da aka zaba na jam’iyyar APC ranar Talata a fadarsa.

Ya ce manufar kulle iyakokin kasarnan shi ne a dakile fasakaurin makamai, da kwayoyi da ga makwabtan kasar nan.

Ya ce tunda dai sakon ya isa makotan sun kuma fahinci dalilin rufe iyakar, nan ba da jimawa ba za a bude iyakokin.

Idan za a iya tunawa dai tun a watan da ya gabata ne minstar Kudi Zainab Shamsuna Ahmad ta ce gwamnati na kokarin ganin yadda za ta bude iyakokin kasar nan.

Ba za a bude bodar Najeriya ba-Nanono

Angwaye a Kano na daga aure saboda hauhawar farashin siminiti

Bude iyakokin kasa : Minstar kudi, Minstan noma wa ke da gaskiya

Ta ce kwamitin da aka kafa domin ya nazarci al’amarin zai mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon da suka cimma, su kuma bukaci da a bude iyakokin kasar.

Sai dai minsitan Noma ya ce waccan magana ta Minstan kudi ba haka ta ke ba domin kuwa mukullin da aka rufe bodar ma an jefa cikin teku.

Nanono ya bayyana hakan ne a makon jiya, yayin taron baiwa manoma tallafi da ibtilain ruwa ya rutsa da su a jihar Kebbi.

Ya ce ko kadan babu batun bude iyakokin kasar nan, inda ya bukaci manoman da su kwantar da hankalinsu.

Sai dai ajiya Talata ne kuma shugaban kasar da kansa ya fito ya ce za a bude iyakokin kasar nan, ko da dai bai anbaci ran aba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending