Connect with us

LABARAI

EFCC ta gurfanar da Jami’in Hukumar Gyaran Hali gaban kuliya

Published

on

Nasiru Yusuf

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta gurfanar da mataimakin shugaban gidan Yari na kasa dake jihar Katsina, Abubakar Sani a gaban Mai shari Hadiza Sabi’u Shagari dake babbar Kotun Tarayya ta Katsina.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewa ana tuhumarsa ne da laifuka guda shida da suka hada da hadin baki da zamba cikin aminci.

A sanarwar da mai magana da yawun hukumar reshen jihar Kano Idris Isyaku ya turawa jaridar Kano Focus ta ce wanda ake zargin yayi amfani da ofishin sa wajen karbar naira miliyan biyu a hannun wasu mutane da sunan zai sama musu da aiki a Hukumar Gidan Yari ta kasa.

Haka zalika ana zargin sa da karbar kudi Naira dubu dari uku da Naira dubu biyar a hannun  Umar Himma da Surajo Ibrahim da kuma Abubakar Gambo duk da sunan zai sama musu aiki.

Bayan karbar korafin ne sai Hukumar ta gayyaci wanda ake zargi amma yaki amsa gayyatar ta har zuwa ranar ashirin da shida ga watan Agustan shekarar da muke ciki inda ya bayyana a gabanta.

” Bayan anyi masa tambayoyi sai hukumar ta ba da belinsa, amma sai ya karya dokokin belin kuma yaki bayyana a gaban kotu har sau biyu.

” A ranar labara sha daya ga watan Nuwambar da yagabata ne Hukumar ta kama shi a garin Abuja tare da dawo dashi ofishin Hukumar dake nan jihar Kano,” a cewar jawabin.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotu, wanda ake zargin ya musanta dukkan tuhumar da akeyi masa inda lauyan sa G.U Jafaru ya nemi kotun data bada belin wanda yake karewa.

Saidai kuma lauyan masu kara ya soki bukatar ba da belin inda kotu ta ba da umarnin a cigaba da tsare wanda ake karar Abubakar Sani a hannun Hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa har zuwa ranar 1 ga watan Disambar shekarar da muke ciki domin sauraron bukatar bada beli.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Headlines

Kano State Reforms: Sa’adatu Rimi University Reverts to College of Education Status

Published

on

The Kano State Executive Council has approved the conversion of Sa’adatu Rimi University of Education back to Sa’adatu Rimi College of Education, Kumbotso, while maintaining its status as a degree-awarding institution.

In a statement issued by the Commissioner for Information and Internal Affairs, Baba Halilu Dantiye, the decision was made to enhance educational quality and streamline management in the state’s higher education sector.

The move follows the 18th meeting of the Executive Council, held on September 18, 2024, after extensive consultations with stakeholders and recommendations from a high-powered committee tasked with reviewing the institution’s status.

The committee raised concerns over the transition to university status, citing risks such as the potential loss of experienced lecturers, salary disputes, and administrative challenges.

Dantiye noted that similar institutions nationwide have operated successfully as colleges of education while offering degree programs through the “Dual Mode” system, as introduced by the National Commission for Colleges of Education (NCE).

This system allows institutions to maintain their core structure while expanding their academic offerings.

Governor Abba Kabir Yusuf has approved the immediate dissolution of the university’s management, with the Vice Chancellor directed to hand over to his most senior deputy.

The government assured that current students would not be affected, as they will continue their studies without disruption.

Additionally, the university’s certificate will be preserved for future use, and the institution will continue to offer both its traditional courses and new degree programs.

This strategic decision underscores the Kano State Government’s commitment to ensuring the growth, stability, and academic excellence of its educational institutions.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Trending