Connect with us

KANUN LABARAI

Bude iyakokin kasa : Minstar kudi, Minstan noma wa ke da gaskiya

Published

on

Al’umma a jihar Kano na ci gaba da bayyana ra’ayinsu kan baki biyu da aka samu na batun bude iyakokin kasar nan tsakanin ministan noma da ministar kudi.

Kano Focus ta rawaito cewa a ranar Talatar da ta gabatane dai ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmed  ta ce akwai yiwuwar a sake bude iyakokin kasar nan da aka rufe tun a watan Agustan bara.

Ministar ta bayyana hakanne a taron tattalin arzikin Najeriya da akayi a jihar Legas a ranar talatar makon jiya.

Ta ce kwamitin da shugaba Buhari ya kafa don duba ribar rufe iyakokin sun bashi shawarar budewa.

Sai dai kuma a ranar Asabar ne ministan aikin gona na kasa Muhammad Sabo Nanono ya bayyana cewa babu ranar da za a buɗe iyakokin kasar domin mukullin da aka garƙame iyakokin an cilla shi cikin teku.

Minista Sabo Nanono ya bayyana hakan ne a gurin bikin rabon kayan aikin gona ga manoman da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihar Kebbi.

Ya ƙara da cewa har yanzu gwamnatin tarayya bata shirya buɗe iyakokin ƙasar nan ba, domin har yanzu tana nan akan bakarta na ganin harkar noma a ƙasar nan ta bunƙasa.

To ko me jama’ar gari ke cewa kan wadannan kalamai na minsitocin biyu?

Hajara Abdullahi Na’ibawa ta ce cin karo da juna da kalaman ministocin sukayi ya nuna karara yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza ta fuskar jagoranci.

Ta ce wasa ne da hankalin al’ummar arewacin kasar nan kawai, shi yasa suke mi’ara koma baya a kalaman nasu.

“Arewa ba ta da masu tsaya mata kowa abinda ya shafe shi kawai yake yi manyan mu basu da wani amfani,” a cewar ta.

Abdullahi Yusuf Tukuntawa cewa ya yi babu magana daya a yadda gwamnati take tafiyar da al’amuranta.

Ya ce masalaha shi ne kawai a bude boda duba da halin da ‘yan kasa ke ciki na matsi da wahala, domin rufe ta da akayi bai canza komai ba sai ma kara ta azzara abubuwa da ya yi.

“Idan an rufe boda ne don ayi maganin matsalar tsaro to har yanzu matsalar kara ta’azzara ta ke yi, kalli abin takaici yadda aka kashe manoma da basu jiba basu gani ba a jihar Borno.

Shi kuwa Adamu Abdullahi cewa ya yi Allah ya jarabci kasarne da azzaluman shugabannin masu son zuciya.

Ya kara da cewa ba karamin abin kunya bane a ce ministoci a gwamnati guda daya amma suna magana dake karyata junan su.

“Tunda har boda tana rufe ba a samu tsaro ba to tabbas bude ta ma ba zai ta’azzara matsalar ba, sai dai ma ya magance ta domin komai zai sakko kuma ayyukan yi za su karu a kasar nan.

Ya kuma ce lokaci ya wuce da za a rinka yaudarar al’ummar arewacin kasar nan da batun bude boda don ba shi suke bukata ba face a magance musu matsalar tsaro.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending