KANUN LABARAI
Masarautar Rano ta dakadar da dagatai biyu da suka sace tallafin Korona
Mukhtar Yahya Usman
Masarautar Rano da ke jihar Kano ta dakatar da Dagatai guda biyu sakamakon zarginsu da ɓoye kayan tallafin korona da gwamnati ta bayar a rabawa talakawa.
Kano Focus ta ruwaito Chiroman Rano kuma hakimin Rano Alhaji Manniru Tafida Abubakar ILa ne ya dakatar da dagatan biyu, bisa umarnin mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammadu Kabiru Inuwa.
Dagatan da su ka haɗa da Umar Yusuf, wanda shi ne dagacin Zurgu da kuma Kamilu Zambur da shi kuma ya ke a matsayin Dagacin Zambur, ana zarginsu da ƙin rabawa talakawansu kayayyakin abinci wanda gwamnati ta bayar domin ragewa al’umma radadin rayuwa.
Tuni dai aka aike da wakilci zuwa ƙasar dagatan da abin ya shafa.
KWARONA: Ana Zargin kwamandan Hisbah da sace kayan tallafi
Hisbah ta dakatar da kwamandan da ake zarigi da sace tallafin Korona
Ra’ayi:Yanayin sanyi ke samu sanya takunkumin fuska a Kano ba cutar Korona ba
Idan za a iya tunawa dai makwanni biyu da su ka gabata aka samu rahoton kwamandan hisbah na karamar hukumar Dala Siyudi Muhammad Hassan, da zargin sace tallafin kwarona da karamar Hukumar Dala ta baiwa jami’an hisbar.
Haka zalika a cikin watan Oktoba ma sai da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma sauraron korafe korafe ta jihar Kano, ta tsare shugaban karamar hukumar Kumbotso Alhaji Kabiru Ado Panshekara, bisa tuhumar sa da yin amfani da karfin kujerarsa wajen karkatar da tallafin kayan masarufin gwamnati na ragewa jama’a radadin dokar hana su fita saboda annobar coronavirus.
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”