KANUN LABARAI
Uwa da ‘ya’yanta biyu sun kashe matashi a Kano
Aminu Abdullahi
Iyayen wani matashi a karamar hukumar Wudil mai suna Yusuf Baba na zargin wata mata mai suna Hafsat Ahmad da ‘ya’yanta biyu da kashe musu dansu na.
Kano Focus ta ruwaito cewa matashin da aka kashe Yusuf Baba yaje gidan Hafsat Ahmad ne don ya karbi kayan sa da yake zargin dan ta mai suna Auwalu Ahmad da sace masa.
Zuwan sa ke da wuya ne kuma Hafsat Ahmad da ‘ya’yanta Auwalu Ahmad da Sabuwa Ahmad suka rufe shi da duka wanda hakan ya kai ga yi masa jina jina.
Abdullahi Baba mahaifi ga mamacin ya ce makwabtan shagon dan sa ne suka gaya masa wanda ya yi masa sata a shagosa.

Hakan ta sanya ya garzaya gidan don meman hakkinsa, inda shugarsa ke da wuya ya yi ido biyu da kayan nasa.
Ya kara da cewa bayan da ya nemi a abashi kayanne sai matar da ‘ya’yanta suka rufe dan nasa da duka wanda yayi sanadiyar mutuwar sa.
A cewarsa bayan da suka kai shi asibiti ne, likitoci suka tabbatar da cewa tuni ya mutu.
Malam Abdullahi ya ce ba wannanne karon farko da Auwalu yake satarwa dan nasa kaya a shago ba, amma ake sulhuntawa.
Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida wanda ake zargi da yin kisan Auwal Ahmad ya ce yana daki ne ne marigayin yazo ya balle masa kofa da nufin neman kayansa.
A cewarsa ya fara futo da wasu daga cikin kayan ne kuma sai rigima ta barke a tsakanin su.
“Sun babballe muna kayan dakinmu tare da dukan ya yata da hakan yasa ya na dauki katako na doke shi.” A cewarsa
Itama Sabuwa Ahmad da ge zaman ya ya ga barawon ta ce sun zage ta ne da hakan yasa ta rama tare da kai musu duka.
Sai dai mahaifiya ga wanda ake zarigin Hafsat Ahmad ta ce lokacin da ‘ya’yan nata suka fara fada da marigayin gida ta koma saboda tasan dan nata ne ya satar masa kaya.
Zanga-zanga ta barke bayan da aka zargi jami’an ‘yan sanda da kisan matashi a Kano
Barayin waya sun yiwa alaramma yankan rago a Kano
Gwamnatin Kano ta saki fursunoni 37
“Allah bai sa nayi masa komai ba ko zagin sa banyi ba balle duka. “San da suka fara fadan ina gurin amma na tafi gida daga baya,” a cewar ta.
A nata bangaren hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni suka kama wadanda ake zargi da yin kisan.
Ya kuma ce sun samu wasu daga cikin kayan da ake zargin an satarwar marigayin da har takai ga an halaka shi.
Ya kara da cewa tuni kwamishinan ‘yan sanda ya nemi da a maida tuhumar babban sashen bincike dake bomfai don fadada bincike.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
