KANUN LABARAI
KAROTA ta kama inyamuri da ya yi safar tabar wiwi katan 60 zuwa Kano
Aminu Abdullahi
Hukumar KAROTA ta kama wani inyamuri Mista Ekennah Okechuku da ya yi safarar kwalaye sama da guda 60 dake dauke da tabar wiwi zuwa jihar Kano.
Kano Focus ta ruwaito cewa hukumar ta kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba bayan da ya boye tabar a cikin motar safa.
Wanda ake zargin ya fito ne daga jihar Imo ya ce yana safarar magungunan daga Lagos zuwa Kano inda yake kai wa kwastomominsa.
Haka zalika mista Okechuku sunansa na cikin jerin sunayen da hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA) take nema, bisa aikata laifin dillacin tabar wiwi zuwa Kano.
A yayin mika wanda ake zargin ga Kwamandan, NDLEA, shugaban hukumar Karota Baffa Babba Dan’agundi yace hukumar sa ta ba da umarnin sauya gurin zama na tashar motar Sabon Gari da ake kira (Luxurious Buses) saboda irin wadannan laifuka da ake aikatawa da irin wadannan motoci.
KAROTA ta baiwa ‘yan kasuwar katako awanni 44 da su bar bakin titi
Hukumar KAROTA za ta tara harajin sama da miliyan dubu a shekar 2021
Akwai lada ga wanda ya kawo tsurkun miyagun ayyuka a Kano -KAROTA
Ya kara da cewa umarnin ya fara haifar da da mai ido dan kuwa wasu kamfanonin motocin na hada kai da KAROTA don tona asirin duk wani mutum ko gungun mutane da ke safarar haramtattun kayayyaki zuwa Kano.
Ya kuma yi gargadin cewa duk kamfanin da aka samu da laifin hada baki da wasu marasa kishi wajen aikata laifi a jihar nan to za a kwace motar su tare da korar kamfanin daga jihar baki daya.
A nasa bangaren Kwamandan, NDLEA, a nan Kano Ibrahim Abdul ya yi godiya ga KAROTA bisa hadin kan da ke tsakanin hukumomin biyu wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin.
Ya ce a baya rundunar ta cafke wasu kayayyaki guda biyu na mutumin wanda ya yi amfani da dabaru wajen boye su a cikin wasu buhunna wanda hakan yasa aka gaza kamashi.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.