Connect with us

KANUN LABARAI

An kubutar da matar da aka yankawa wuya, aka kuma soketa a wuri 15 daga mutuwa a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Al’amin Mohammed Bello mai shekaru 20 da wasu mutane uku bisa yunkurin hallaka wata mata a unugwar Guringawa dake karamar hukumar kumbtso, bayan da suka yankamata wuya suka kuma soketa a wuri 15.

Kano Focus ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Laraba.

Kiyawa ya ce a ranar 14 ga watan da ya gabatane wanda ake zargin ya shiga gidan matar mai suna Yusrah Zakari mai shekaru 20 tare da abokanansa  suka kuma yankamata wuya da sauran sassan jikinta sannan suka sace motarta suka gudu.

Acewarsa sun samun korafin ne daga mijin matar Abba Adam jami’an su je wurin, suka kuma dauketa zuwa asibitin Aminu Kano da a nanne aka ceci rayuwar ta.

Kiyawa ya ce rundunar ta samu nasarar cafke wanda ake zargin ne kwanaki talatin da biyu da faruwar alamarin tare da motar da suka sata.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, Inda ya bayyana wadanda suka yi fashin tare da Abubakar Hassan mai shekaru 28 da Yusuf Lawan 21 ma zauna unguwar Sabuwar Gandu.

Sai Yahaya Salisu mai shekaru 28 dan unguwar Sheka duk a karamar hukumar Kumbotso.

Ya kuma ce zasu gurfanar da wadanda ake zargin da zarar sun kammala bincike.

‘Yan sanda sun kama guda cikin wadanda suka hallaka dattijo a Kano

Kotu ta yankewa matasa biyu hukunci bulala 12 a Kano

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da attajirin Minjibir da aka yi garkuwa da shi

A nata bangaren Yusrah Zakari ta ce mijin ta ya fita lokacin da lamarin ya faru, a cewarta ta shiga kitchen don ta zuba abinci sai kawai gani tayi annufota da wuka daga nan ba ta sake sanin abinda ya faru ba.

“Bayan suka na a wuya sun soke nu a wuri shabiyar a jikina.

“Sai kawai ganina nayi a asibiti, naji dadi sosai da aka kamasu kuma ina fatan za a bi min hakki na,” a cewar ta.

Shima daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Al’amin Mohammed Bello ya ce sun shiga gidan matarne a Sabuwar Gandu don satar mota.

“Mutum biyu suka tare kofa ni da Yusuf sai muka shiga ciki na dauki mukullin motar zamu fita sai ta janyo Yusuf shi kuma ya buga mata wuka a wuya.

“Shi ne muka dauketa muka sakata a cikin bandaki daga nan na dauki motar zuwa Kaduna ni kadai dan na sayar motar mu raba kudi,” a cewar sa.

Ya ce sunyi karatu a gidan mahaifinta kafin rasuwarsa sai dai bayan da ya mutu ne sai suka yi farin ciki da hakan tare da hada baki don aikata laifin da ake zargin su akai.

“Na batawa iyayena da ‘yan uwana, suna basu taba tsammanin zan aikata haka ba ina matukar nadama,” inji shi.

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending