Connect with us

KANUN LABARAI

Satar yaran Kano 118: Iyayen yaran sun zargi gwamnati da nuna halin ko inkula

Published

on

Aminu Abdullahi

Yayin da aka cika shekara goma da fara satar yara a Kano ana kaisu kudancin kasarnan, iyayen yaran sun zarigi gwamnatin Kano da nuna halin ko inkula wajen kubutar da yaran nasu.

Kano Focus ta ruwaito wannan zargi na fitowa ta bakin wasu daga cikin iyayen yaran mata lokacin da suke gudanar da zanga-zangar lumana kan sace yaran nasu ranar Alhamis a nan Kano.

A cewar jagorar masu zanga-zangar Aisha Haruna Kabuga  haryanzu suna cikin wani hali na rashin dawo musu da yarannasu.

Ta ce  kwamitin da gwamnati ta kafa kusan shekara guda da watanni ya gaza tabuka wani abun kirki.

“Ko yaushe muka tuntubi kwamitin sai suce mu saurare su suma suna sauraren gwamnatine.

“Gwamna ya gayyace mu, kuma batun yana gaban kotu amma har yanzu shiru ba abinda akayi,” a cewar ta.

Aisha ta kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Gabduje da suyi duk mai yiwuwa don kubutar musu da yaransu kamar yadda aka kubutar da yaran jihar Katsina.

Ta ce a cikin yara 118 da suke nema har yanzu ba suga yaro ko guda dayaba.

“Mun kasa yadda cewa gwamnati na yin wani abu don a kwato mana yaranmu kuma ansan inda suke.

“Mun zama kamar bamuda shugabanni, kamar bamuda manya a arewa, saboda ba ‘ya’yansu aka sace ba,” a cewar ta.

Ita ma wata uwa Zainab Abdullahi Giginyu cewa tayi watanni uku da suka gabata sanatan Kano ta Kudu Kabiru Gaya ya ce an gano wasu daga cikin yaran sai dai har yanzu basu ga ko daya ba.

Itama Aisha Bashir ‘Yankaba ta ce akwai ‘danta mai suna Musa Abdurrauf da aka ganoshi a jihar Anambra, sai dai har yanzu an gaza dauko shi.

Ta ce ko a cikin yaran da aka debo Aisha da Farouk sun tabbatar mata da cewa makaranta daya aka sakasu tare da dan nata a can Anambra.

“Abokinsune kuma sun tabbatar min dacewa yana can amma gashi gwamnati ta watsar da al’amarin ba tama kulawa da halin da muke ciki.

“Shekaru shida kenan da sace min yaro, ya kamata gwamnati ta san cewa danmu take yin mulkin nan,” a cewar ta.

Da take mayar da jawabi, kwamishiniyar mata da walwalar kananan yara ta jihar Kano  Zahra’u Muhammad Umar ta ce gwamnatin Kano ta shirya tawaga da za ta nemo yaran da aka rasa.

Ta ce rikicin zanga-zangar Endsars da bullar annobar Korona ne ya dakatar da tafiyar.

Ta kara da cewa dole ne aji shiru daga kwamitin da gwamnati ta kafa don dawo da yaran, domin abu ne da ya shafi tsaro da ba za a dinga bayyana duk shirye shiryen da ake yi ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending