Connect with us

KANUN LABARAI

Hisbah za ta fara bude kananan ofisoshi a cikin unguwannin Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Hukumar Hisbah ta ce gwamnatin Kano ta sahale mata bude kanan ofishinta a dukkanin unguwannin da ke jihar Kano domin kula da kaikawon al’umma domin dakile barna.

Kano Focus ta ruwaito ce babban kwamandan Hisbah Harun Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan ya yin ziyarar da ya kai ofishin hukumar dake rukunin gidajen Sheikh Nasiru Kabara (Amana City) da na Sheikh Jafar Mahmud Adam ranar Lahadi.

Ya ce hukumar za ta gina masallatan juma’a a rukunin gidanjen duba da korafin da alummar yankin ke yi na rashin masallatan juma’a.

“Gwamanati ta samar da filin da za a gina masallatan kuma nan bada jimawa ba za a fara ginawa,” a cewar sa.

Ya kara da cewa za su cigaba da gudanar da ayyukan kakkabe bata gari a yankunan kasancewar su sabbin unguwanni.

“A bubuwa na tafiya yadda ya kamata domin ko a yau da nazo naga ana yin wani sulhu da ya bani sha’awa don saida na tsaya ma naji yadda aka gudanar da shi,” inji shi.

Ibn Sina ya ce akwai sabbin tsare tsare da hukumar ta fitar da za ta yi amfani dasu a shekarar wannan sabuwar shekaradomin tabbatar da tsaro da kuma yaki da badala a jihar Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending