Connect with us

KANUN LABARAI

Kalaman Kwankwaso da Abdullahi Abbasa jagaliyancine- Ibrahim Shekarau

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce kalaman da tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa mata su dauki tabarya da muciya tsantsar shirme ne.

Kano Focus ta ruwaito Ibrahim Shekarau na wadannan kalamaine ya yin da ya ke ganawa da yan jaridu ranar Lahadi a nan Kano.

Haka zalika ya kuma soki kalaman da Abdullahi Abbasa ya yi na mayarda martani ga Kwankwaso a matsayin shashanci.

Idan za a iya tunawa dai a watan da yagabatane wani faifan bidiyo ke yawo a kafafan sadarwa na zamani da aka gano Kwankwason na cewa mata su dauki tabarya da muciya a zaben shekarar 2023 domin kare kansu.

Yace ko kadan ba za su yadda a sake maimaita musu irin zalincin da aka yi musu a zaben da ya gabata, na Inconclusive.

Wannan ce ta sanya shi ma shugaban riko na jam’iyyar APC a jihar Kano Abdullahi Abbas ya yi martani kan kalaman na Kwankwaso ya kuma ce za su sake maimaita abinda suka yi kuma ba abinda za a yi.

Abbas ya cewa mabiyansa su yi duk abinda suka ga dama su zagi duk wanda suke so ko an dauresuma su za su karbo su.

Mata a Kano su yi tanadin tabarya da muciya kafin zaben 2023-Kwankwaso

Bama tsoron barazanar Abdullahi Abbas- PDP

Sai dai shekarau ya ce abin takaicin shi ne dukkanin mutanen biyu ba wanda zai sanyo iyalansa a gaba, wajen dabbaka abin da suke kira jama’a su aikata.

Ya ce abin ayi tir da shi ne  yadda ake samun mata a Kano ana basu gariyo da makamai sunan yawon siya.

Ya kara da cewa babban abin takaicin shi ne yadda shugaba zai hau munbari ya fadi kalamai irin na yan jagaliya, duk da cewa su shugabannine.

Ya ce in dai sai an kashe wani ko wata ne ko kuma an zubar da jini sannan  zai zama shugaba to ya yafe.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending