KANUN LABARAI
NDLEA a Kano ta zargi gwamnati kan nuna mata wariya
Aminu Abdullahi
Hukumar (NDLEA) ta ce gwamnati ta mayardasu saniyar ware, sakamakon kin samar musu da wadatattun kayan aiki kamar sauran hukumomi irinsu.
Kano Focus ta ruwaito shugaban hukumar shiyyar Kano Ibrahim Abdul ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin taron manema labarai a wani bangare na bayanin aikace-aikacen da hukumar tayi a shekarar da ta gabata.
Ibrahim Abdul ya ce hukumar na fama da karancin motocin gudanarda ayyuka, a cewarsa mota biyu ce da su duk fadin hukumar da ke Kano.
Ya ce cikin motocin biyu daya shugaba ne ke yin mafani da ita yayin da ragowar dayar kuma a ke ayyukan hukumar da ita.
Abdul ya ce idan aka yi la’akari da sauran hukumomin gwamnati da suke a mataki iri daya, hukumar NDLEA ce kawai kwamandanta bashi da motar hawa ta ofishinsa.
Ya kara da cewa koda yaushe gwamnati tana baiwa ‘yan sanda da sojoji da DSS fifiko inda take mancewa da su.
“I dan aka tashi haka akeyi amma mu kullum ana mantawa damu kuma aikin su bai fi namu muhimmanci ba saboda akwai alaka tsakanin shaye-shayen kwayoyi da duk laifuka.
“Duk yawancin mutanen da aka kama masu Kidnapping, masu fashi da makami, duk in kaduba aljihunsu sai kasamu kwaya.
Kaga kenan kwayar suke sha take fidda musu imani idan baka dakile kwaya ba ya zaka dakile wancan daga sama,” a cewar sa.
Ya kara da cewa koda kasafin kudi da akeyi ana warewa hukumar NDLEA abinda bai wuce naira miliyan dari da goma sha hudu ba, a cewarsu duk basu wuce a sayi Hilux biyu ba.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.