Connect with us

KANUN LABARAI

Ganduje ya zaluncemu miliyan 80 a albashin Nuwamba da Disamba-ma’aikatan kotu

Published

on

Aminu Abdullahi

Babbbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Usman Malam Na’abba ta dakatar da gwamnatin Kano  daga cigaba da zabtare albashin ma’aikatan shari’a har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci akan karar da aka shigar gabanta.

Hakan ya biyo bayan korafin cewar gwamnatin Kano ta zaftare musu sama. da naira miliyan 80 cikin albashinsu ba gaira ba dalili da suke ganin hakan zalincine

Kano Focus ta ruwaito kungiyar ma’aikatan shari’a ta jihar Kano ce ta gurfanar da gwamnatin bisa yanke musu albashin watan Nuwamba da Disambar shekarar da ta gabata.

Cikin wadanda ake kara sun hadarda gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinan shari’a da shugabar ma’aikata da kuma ma’ajin gwamnatin jihar.

Haka zalika mai shari’a Malam Na’abba ya umarci wadanda ake kara da suyi amfani da yarjejeniyar da aka cimma a ranar goma sha tara ga watan disambar bara dan biyan ma’aikatan shari’a cikakken albashin su.

Ya kuma dage cigaba da sauraron shari’a zuwa ranar ashirin da takwas ga watan da muke ciki na Janairu.

Shugaban kungiyar ma’aikatan shari’a Mukhtar Rabi’u Lawal ya ce gwamnatin jihar Kano ta yankewa ma’aikatan shari’a albashin su kimanin naira miliyan tamanin na watan Nuwamba da Disambar shekarar data gabata.

“Kamar yadda gwamnati ta bugi kirji ta yanke albashin ma’aikata ba tare da saninmuba, kuma ba tare da wani cikakken daliliba shiyasa mukaga yakamata muma muje munemi hakkin mu.

Ya kara dacewa koda bashi ake binsu bai kamata a yanke musu albashi hakaba, yana mai cewa ba iya miliyan tamanin kawai gwamnatin ta yankarmusu ba.

Ya ce idan aka hada da kudaden watan Janairu da Fabrairu da watan Maris kudin za su kai kimanin naira miliyan dari uku sai dai sun bar wancan ne sakamakon zama da gwamnati tayi da kungiyar kwadago inda tace anyi haka ne saboda cutar korona.

“Yanzu dai muna neman abiyamu kudin mu da aka yanka na watan Nuwamba da Disamba wato naira miliyan tamanin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending