Connect with us

KANUN LABARAI

NIMC ta yiwa mutane sama da miliyan biyu rijistar dan kasa a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Hukumar kula da rijistar lambar dankasa (NIMC) ta ce ta yi wa sama da mutane miliyan biyu da dubu dari uku rajista a jihar Kano tun lokacin da aka fara yin rijistar a shekara 2007.

Kano Focus ta ruwaito cewa jami’in tuntuba na hukumar a jihar Kano Illo Sarkin-Yamma, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.

Ya ce bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na cewa al’umma su hada lambar shaidar dan kasa da layukan wayoyinsu, hukumar ta ware cibiyoyi 52 don yin rajista a jihar.

Ya kara da cewa manufar kara cibiyoyin ita ce a hanzarta yin rajistar ga wadanda suka cancanta a kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya kuma ce an samarwa cibiyoyin kayan aiki na zamani domin saukaka cunkoso da kuma hanzarta yin aikin rajistar ga al’umma.

Illo ya ce ana gudanar da aikinne ta hanyar  bin ka’idoji na kariya daga cutar KORONA a dukkanin cibiyoyin da ke fadin jihar.

Hukumar NIMC ta samar da hanya mafi sauki domin rijistar katin dan kasa

Masu satar bayanai ne ke samar da ‘link’ din dake bukatar a hada lambar NIN da ta layin waya-NIMC

Baka da ‘yancin da ya fi mallakar katin dan kasa-Sarkin Karaye

“Kowace cibiya a cikin 52 tana yin rajista tsakanin mutane 100 zuwa 200 a kowace rana, kuma mun inganta ayyukanmu don bawa mutane da yawa damar shiga,” a cewar sa.

Sarkin Yamma ya ce gwamnatin tarayya ta amince da sanya kamfanoni kimanin 203 masu zaman kansu domin saukaka gudanar da aikin rajistar a kasar nan.

Ya kara da cewa yin rijistar kyautane inda ya gargadin al’umma da suyi hattara da masu damfara.

Da yake jawabi daraktan hukumar shiyar Kano Lawal Yahya, ya ce hukumar ta kama wasu da suke yi mata zagon kasa ta hanyar damfarar mutane da sunan za su yi musu rijistar katin dan kasa inda suke karbe musu kudade.

Ya ce tuni suka mika irin wadan nan mutane hannun jami’an ‘yan sanda don cigaba da bincike.

Ya ce hukumar za ta dauki tsauraran matakai don bunkasa hanyoyin da al’umma zasuyi rijistar katin dan kasa a fadin kasar nan.

Yahya ya shawarci  al’umma da su bi ka’idojin da Hukumar ta gindaya kan yin rajistar don saukaka mata wajen gudanar da aiki.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending