KANUN LABARAI
Amare a Kano sun fara sheka kukan rufe gidajen biki
Rafi’atu Ilyasu
Tun bayan da Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe gidajen biki a fadin jihar nan sakamakon dawowar cutar Korona, amare da masu gidajen biki aka fara was an ɓuya.
A zantawar da Kano Focus ta yi da wasu amare da suka riga suka biya kudadde domin shagalin biki sun nuna rashin jin dadin su da matakin da gwamnati ta dauka na rufe gidajen bikin.
Hauwa’u Kaber wata amarya ce da ta shirya gwangwaje bikin ta a irin wadannan gidajen biki ta ce ko kadan wannan al’amari bai yi mata dadi ba.
Ta ce bayan da ta samu labarin an rife gidajen biki kadan ya rage ta fashe da kuka, domin takaici

“Sanda na samu labarin saura kaɗan na fashe da kuka saboda ɓacin rai, duk da ba a rufe ba sai da bikina ya zo?
“Mun kama Wujdan event center, daura da Jami’ar Yusuf Maitama Sule, domin yin kamu, gaskiya ba a kyautamin ba, ba a yimin adalci ba,
Halima Sa’id itama wata amarya ce, ta ce ita dai sai da ta zubar da hawaye da taji labarin na kulle gidajen biki.
A cewarta duk an yi anko anbiya kudaden abinci da na wurin da za a yi bikin sai kawai ji ta yi an ce gwamnati ta hana.
Sai dai a zantawar Kano Focus da ɗaya daga cikin masu gidajen bikin na (Darul tauheed) kuma Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar masu gidajen biki na jihar Kano Kamal Mas’ud El’jibril ya ce ba yadda za suyi dole subi umarnin gwamnati.
Ya ce matsala dai anriga an shigeta, kuma asara an tafkata, domin idan wasu da suka biya kudin abinci ba na hall ba, an riga an sayi kayan.
A cewarsa babu yadda za a yi su fitar da kudi bayan sun sayi kaya su mayarwa masu shi.
“A wancan lokacin munyi ta rigima da mutane, wasu ma kara suka kaimu akan kudadensu.
“Haka a ƙungiyance muka dinga bi muna masalaha mataki-mataki.”
“Idan mutum ya baka dubu ɗari uku, ko dubu ɗari biyu, sai dai kayi ƙoƙari ka dawo masa da su da kaɗan_kaɗan, ko kabashi shawara ya

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
