KANUN LABARAI
Yadda sanyi ke hana matasa sallar asubah a Kano
Zulaiha Danjuma
Shigowar yanayin sanyi a jihar Kano da ma wasu jihohin ya sanya matasa da dama kauracewa fita sallar asubahi.
A zantawar jaridar Kano Focus da wasu matasa a nan Kano, sunce yanayin sanyi kan sanyasu kauracewa masallatai musamman ma idan babu abinda za su dafa ruwa domi yin alwala.
A yanzu dai lokacin sallar asubahi a Kano shi ne 5:30 zuwa 5:32 a wasu masallatan.
Sai dai da yawa daga cikin matasan sunce yin sallah a irin wannan lokaci indai ba ruwan zafi suka tanada ba, yana basu wahala sosai

Sadiq Ibrahim mazaunin unguwar tukuntawane, yace kafin shigowar sanyi baya makara wajen sallar asubahi, a cewarsa yana tashi kafin ma ladan ya kira sallah.
“Gaskiya kafin shigowar sanyi ina ga bana makara sallar asuba, dan lokuta da dama kan ma a kira sallan asuba na tashi”
“Da akwai wata rana da aka yi wani mukumukun sanyi idan nayi lilliba ma sanyi nake ji.
“Ina jin kiran sallar na dan leka waje nace kai bazan iya fita ba.
“Da yake mutun gwauro ba matace da shi ba, balle ace a dafa maka ruwan zafi”
“Yanzu gaskiya na kan jira rana ta dan fito sai inyi sallata gabaki daya, abin da nake yi kenan” A cewarsa.
Itama wata budurwa da ke zaun a unguwar Hotoro, Aishatu Ibrahim ta ce sanyin da akeyi yana hanata tashi daga gadonta da Asubahi.
“Sanyin nan yana neman takurani wajen hanani salla a kan lokaci”
“Ina tashi karfe 5:30, amma yanzu bana ma iya tashi daga gado sai karfe 6:00. Kuma idan na tashi karfe shidan sai na tabbatar da cewa inada ruwan zafi nayin alwalla”
“Yawanci nakan tanadi ruwan zafi kafin na kwanta bacci, saboda ba zan iya yin anfani da ruwan sanyi wajen alwalaba.” A cewarta.
Shi ma wani dalibi a jami’ar bayero Nura Yusuf yace yanayin sanyi yana hana shi alwalar sallar asuba.
“A halin da muke ciki muna kokarin mu tanadi ruwan zafi dai-dai misali idan ba a samuba kuma, nakan yi anfani da ruwan rijiya”
“Yau dai nayi alwala a kan lokaci amma nayi anfani da ruwan rijiyane, da yake shi yana da dan dumi, ba zai takuramin ba.
“Gaskiya na dan yi fashin salla tunda aka fara sanyin nan amma bana wuce karfe 6:00” a cewarsa.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
