Connect with us

KANUN LABARAI

Kotu a Kano ta yankewa gawa daurin shekara guda a gidan yari

Published

on

Emir Muhammadu Sanusi II

Rafi’atu Ilyasu

Kotun majistary mai lamba hudu da ke zamanta a gidan Murtala, ta yankewa wani mutum mai suna Abubakar Bello da tuni da aka ce ya mutu daurin shekara guda a gidan yari.

Kano Foucus ta ruwaito Mai shari’a Rakiya Lami Sani ce ta yanke hukunci ranar Laraba a nan Kano.

Tun da fari dai an gurfanar da Abubakar Bello a gaban kotun bisa laifin satar mota.

Sai dai ana tsaka da shari’ar ne aka gabatarwa da kotu takardu cewar wanda ake tuhuma ya mutu.

Wannan ce ta sanya mai shari’a ta rufe shari’ar tun da dai ba a shari’a ada gawa.

To sai dai bayan rufe shari’ar ne kuma aka hango wanda akace ya mutun yana yawo a gari abinsa.

Hakan ce ta sanya aka yi masa tarko da wata budurwa, aka kuma sake kamashi.

Hisbah ta bukaci masu laifi suyi sallah raka’a 50 kafin a kaisu kotu

Kotu ta daure matashi a Kano kan furucin kashe mahaifinsa

Kotu ta yankewa matasa biyu hukunci bulala 12 a Kano

Dan sandan kotu mai gabatar da kara ASP Ahmad Mukhtar ne ya sake gurfanar da shi gaban kotun bisa zarginsa da laifin satar mota da ake yi masa tun a baya.

Haka kuma mai shari’ar bayan nazari da bincike ta tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi.

Mai shari’a Rakiya Lami Sani ta yankewa Abubakar Bello daurin shekara guda a gidan yari, ko kuma zabin tarar N50,000.

Sai dai kotu ta ce dole ne ya biya N750,000 kudin motar da ya sata tun a baya.

Barrister Tijjani Ibrahim shi ne lauyan gwamnati, ya shaidawa manema labarai cewa a baya an gurfanar da wanda ake zargi gaban kotu, sannan aka bashi dama ya kawo shaidu domin kare kansa amma sai ya bace bat.

Ya ce ana tsaka da haka ne wadanda suka karbi belinsa suka zo da takardun asibiti cewa Allah ya yi masa rasuwa.

Hakan ta sanya kotun ta rufe shari’ar, sai kuma yanzu aka sake ganinsa a gari.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending