KANUN LABARAI
Yansanda a Kano sun kama wanda ya sassari matarsa a kotu
Aminu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutumin da ya sassari matar sa mai dauke da juna biyu tare da wanta a harabar kotu bayan da mai shari’a ya raba auren su a ranar Litinin data gabata.
Kano focus ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a anan Kano.
Kiyawa ya ce an kama Bilyaminu Abdullahi mai shekara 48 bisa zargin yunkurin kisan kai ta hanyar sarar matar sa Shafa’atu Sale wanta Ado Sale a harabar kotun shari’ar musulunci dake karamar hukumar Rano.
Da yake jawabi wanda ake zargi Bilyaminu Abdullahi ya ce ya aikata laifin da ake zargin sa akai ne sakamakon hukuncin da alkali ya yanke bai yi masa dadi ba.
“Alkali yace ya raba aure na da ita akan fansar naira dubu ashirin, duk da na fada masa cewa ni matata nake so ba wai kudinne yayimin kadan ba amma ya ce a tura a kwashe kayan ta.
“Abinda ya bata min rai kenan ana fitowa daga kotu na kama yankar su da wuka.
“Wuka tace ina sana’ar saida zuma ne kuma na yanke ta akanta da hannunta shi kuma na yanke shi a kafadarsa da hannun sa,” a cewar Bilyaminu.
Kotu a Kano ta yankewa gawa daurin shekara guda a gidan yari
Miji ya sassari matarsa a gaban kotu a Kano
An kafa kotunan sauraron korafin zaben kananan hukumomi a Kano
Ya kara da cewa wantane ya maida ita gida, da ya bibiya don jin ba’asi sai iyayen da ‘yan uwanta suka nemi da ya sakar musu ‘yar su.
Ya kuma ce bayan da yaki amincewa ya sake ta ne, suka maka shi kara a gaban kotu da har takai ga alkali ya raba auren su.
A nata bangaren Shafa’atu Sale ta ce duka da cin zarafi ne yasa ta nemi da a raba auren nasu.
Ta kara da cewa bayan da suka fito daga kotune sai ya dinga kiran sunanta, kin amsawar da tayi sai ya zaro wuka ya fara caka mata akan ta da wuya da kuma hannu sannan ya koma kan wanta inda shima ya sassara shi.
Shafa’atu ta kuma ce ita ta nemi da a raba auren nasu inda kuma ta bukaci da abi mata hakkinta bisa raunukan da ya yi mata ita da dan uwan nata.
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”